Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Lahadi 19/10/2025

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Isiyaku Muhammed da Umar Mikail

  1. Mu kwana lafiya

    Mun kawo ƙarshen rahotonni a wannan shafi na ranar Lahadi.

    Mu haɗu da ku gobe da safe domin samun wasu sababbi daga sassan duniya.

  2. Isra'ila ta ce za ta ci gaba aiki da yarjejeniyar tsagaita wuta bayan hare-hare a Gaza

    Rundunar sojin Isra'ila ta ce za ta ci gaba da aiki da yarjejeniyar tsagaita wuta awanni bayan hare-haren da ta kai Gaza.

    Sanarwar da rundunar ta IDF ta fitar ta ce: "IDF za ta ci gaba da aiki da yarjejeniyar kuma za ta mayar da zazzafan martani duk lokacin da aka sake saɓa yarjejeniyar."

    Ta sake zargin Hamas da karya yarjejeniyar da ta fara aiki ranar 10 ga watan Oktoba.

    Hare-haren na yau sun yi sanadiyyar kashe mutum 44 a faɗin Gaza, a cewar majiyoyin asibiti da na yaɗa labarai.

  3. Labarai da dumi-dumi, Adadin Falasɗinawan da Isra'ila ta kashe a yau sun kai 44

    Adadin Falasɗinawan da Isra'ila ta kashe a yau Lahadi sun kai 44, kamar yadda majiyoyin asibiti suka shaida wa BBC.

    Fiye da rabin mamatan an kai su asibitin Al-Awda ne da ke arewacin Gaza.

  4. Kalli hare-haren Isra'ila a Gaza duk da yarjejeniyar tsagaita wuta

    Wani bidiyo da kamfanin labarai na Reuters ya wallafa ya nuna yadda baƙin hayaƙi ke tashi a unguwar Khan Younis da ke kudancin Gaza sakamakon hare-haren Isra'ila ta sama.

    Kamar yadda muka kawo rahotonni, Isra'lla ta kai jerin hare-hare kusan 120 a Gaza bayan ta zargi mayaƙan Hamas da kashe sojojinta biyu.

    Hare-haren na yau ne mafiya muni da Isra'ila ta kai a Gaza tun bayan fara aiki da yarjejeniyar tsagaita wuta ranar 10 ga watan nan.

    Kafin yau ɗin, dakarun Isra'ila sun kashe Falasɗinawa da dama suna masu iƙirarin cewa mayaƙan Hamas ne.

    Latsa hoton ƙasa ku kalli bidiyo:

    Bayanan bidiyo, Latsa hoton sama ku kalli bidiyo:
  5. Isra'ila ta kashe Falasɗinawa 13 a tsakiyar Gaza

    Gaza

    Asalin hoton, Reuters

    Aƙalla Falasɗinawa 13 aka kashe sakamakon hare-haren da Isra'ila ta kai a faɗin Zirin Gaza.

    Majiyoyi daga Gazan sun ce cikinsu har da kwamandan Hamas mai suna Yahya al-Mabhouh, wanda aka kashe a hari ta sama kan wani wurin shan shayi.

    Wani likita a asibitin al-Aqsa ya ce an kai musu gawar mutum tara da kuma wasu da yawa da aka raunata bayan hare-hare uku a al-Zawaida da ke kusa da gaɓar ruwa.

    Akasarin waɗanda aka kashe a al-Zawaida mambobin ƙungiyar Hamas ne, inda rahotonni suka bayyana cewa suna yin wata ganawa ne a wurin.

  6. ‘Yansandan Kano sun saki ɗanjarida Dan’uwa Rano bayan zargin ɓata wa ɗansiyasa suna

    Ibrahim Dan’uwa Rano

    Asalin hoton, Amnesty Internatonal

    Rundunar ‘yansandan Najeriya reshen jihar Kano ta saki ɗanjarida Ibrahim Ishaq Rano, wanda aka fi sani da Dan'uwa Rano, bayan tsare shi saboda ƙorafin da jami’in gwamnatin jihar ya shigar a kansa.

    Ɗanjaridar ya tabbatar wa BBC cewa an sako shi ne bayan Abdullahi Rogo, babban hadimi ga gwamnan Kano, ya janye ƙorafin da ya shigar a yau Lahadi.

    Rogo ya shigar da ƙorafin cewa ɗanjaridar ya ɓata masa suna game da yaɗa labarin zargin da hukumomin yaƙi da cin hanci na Najeriya ke yi masa na ɓatan maƙudan kuɗaɗe daga lalitar gwamnatin Kano.

    Ƙungiyar kare haƙƙi ta Amnesty International ta bayyana kama ɗanjaridar a matsayin “abin da ya saɓa wa doka”. Ta ce salo ne “da ake amfani da ‘yansanda domin murƙushe kafofin yaɗa labarai masu zaman kansu”.

    An saki ɗanjaridar da misalin ƙarfe 5:30 na yammacin yau bayan tsare shi a hedikwatar ofishin yanki na Zone 1 da ke ƙwaryar birnin Kano.

  7. Labarai da dumi-dumi, Isra'ila za ta dakatar da shigar da kayan agaji Gaza, in ji rahotonni

    Isra'ila za ta dakatar da shigar da kayan agaji Gaza har sai abin da hali ya yi, a cewar rahoton kamfanin labarai na Reuters.

    Reuters ya ambato kafar yaɗa labaran Isra'ila na cewa matakin na zuwa ne bayan zargin Hamas da karya yarjejeniyar tsagaita wuta, zargin da ƙungiyar ta musanta.

    Ɗaruruwan motocin kayan agaji ne ke shiga zirin a kowace rana tun bayan fara aiki da yarjejeniyar ranar 10 ga watan Okttoba.

    A watan Agusta Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce yunwa ta ɓarke a yankin saboda matakin Isra'ilar na hana shigar da kayayyakin buƙata ziirn.

  8. Labarai da dumi-dumi, Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta fara kai hare-hare a Gaza

    Rundunar sojin Isra'ila IDF ta ce ta fara kai jerin hare-hare a kudancin Gaza.

    Wata sanarwa da ta fitar ta ce tana kai harin ne kan Hamas "bayan karya yarjejeniyar tsagaita wuta a yau".

    Hamas ta ce ba ta magana da mayaƙan da aka ce su ne suka kai harin a kusa da Rafah.

  9. Isra'ila ta buƙaci Falasɗinawa su fice daga gabashin Gaza

    Gaza

    Asalin hoton, Getty Images

    Rundunar sojin Isra'ila ta fitar da wata sanar da a ciki ta bayyana gargaɗin da ta kira na gaggawa zuwa ga mutanen Zirin Gaza kan su fice daga gabashin zirin.

    Isra'ila ta ce ba ta so Falasɗinawa su ci gaba da zama a yankunan da suka kamata daga arewa mafi nisa zuwa kudancin bakin iyakar shiga ƙasar Masar.

    Ta ce ta ɗauki wannan matakin ne domin yankuna na soji masu haɗari ga fararen hula, inda komai zai iya faruwa.

    Tun da farko, sojojin Isra'ila sun ƙaddamar da wasu hare-hare a kudancin Gaza, inda suka zargi Hamas da fara kai mata hare-hare a abin da suka kira da saɓa yarjejeniyar tsagaita wuta.

  10. Ko Colombia ta hana sarrafa miyagun ƙwayoyi ko mu ɗauki mataki - Trump

    Trump

    Asalin hoton, EPA

    Shugaban Amurka Donald Trump ya zargi shugaban Colombia Gustavo Petro da goyon bayan masu sarrafa miyagun ƙwayoyi a ƙasarsa, inda ya ce dole shugaban ya kawo ƙarshensu.

    Trump ya bayyana haka ne a shafukansa na sada zumunta, inda ya bayyana takwaransa na Colombia da 'dilan ƙwayoyi ba bisa ƙa'ida ba.'

    Ya ce daga yanzu Amurka za ta daina bayar da duk wani tallafin da take ba ƙasar ta Colombia, sannan ya yi barazanar cewa idan har Colombia ba ta hana sarrafa ƙwayoyi ba, ita Amurka za ta hana da kanta.

    Mr Petro dai ya daɗe yana samun bambancin ra'ayi da shugaban Amurka. A jawabinsa a Majalisar Ɗinkin Duniya, ya fito fili ya soki Trump, inda ya zarge shi da hannu a kisan kiyashin da ake yi a Gaza.

  11. Me Sarkin Ingila zai iya yi kan zargin lalata da ake yi wa ƙaninsa?

    Ingila

    Asalin hoton, Reuters

    Kimar Yarima Andrew wato kanin Sarkin Ingila ta sake gamuwa da wata matsalar inda jaridu ke ta bayyana wata wasikar imel da ke nuna cewa yana da alaka ta kut da kut da attajirin nan da aka kama da laifin lalata a Amurka Jeffrey Epstein, wanda ya kashe kansa a kurkuku.

    Bayanan cikin wasikar sun nuna cewa Yarima ya ci gaba da alaka da Epstein fiye da tsaewon lokacin da ya ce ya katse hulda da shi.

    Wasikar ta saba da bayanan da Yariman ya yi wa BBC a wata hira da kafar ta yi da shi, inda ya ce ya katse alaka da Epstein bayan da ya hadu da shi a New York a watan Disamba na 2010, inda aka dauki mutanen biyu a hoto.

  12. Sojojin Isra'ila sun kai hare-hare a kudancin Gaza

    iSRA

    Asalin hoton, Reuters

    Rahotanni daga Isra'ila na cewa sojojin ƙasar sun kai wasu hare-hare a wasu sassan na Zirin Gaza duk da cewa an shiga yarjejeniyar tsagaita wuta.

    Rahotannin sun nuna cewa sojojin saman Isra'ila ne suka ƙaddamar da hare-haren a birnin Rafah da ke kudancin zirin, duk da cewa har yanzu rundunar ba ta ce komai kan hare-haren ba a hukumance.

    Sai dai wani soja ya ce hare-haren na ramakon gayya ne, inda ya yi zargin Hamas ce ta fara kai hare-hare kan sojojin Isra'ila, wanda a cewarsa karya yarjejeniyar da aka shiga ne.

  13. Ɓarayi sun yi sata a babban gidan tarihi na Louvre da ke Faransa

    Faransa

    Asalin hoton, Reuters

    Ɓarayi sun kutsa cikin ɗaya daga cikin manyan gidajen adana kayan tarihi na duniya wato Louvre da ke birnin Paris na Faransa, inda kafar yaɗa labaran Fanasa ta ruwaito cewa ɓarayin sun sace wasu muhimman kayayyaki a gidan na tarihi.

    Rahotanni sun ce wasu mutum uku ne ake zargi sun shiga gidan tarihin da fuskokinsu a rufe, inda suka sace wasu kayan ado na gidan sarauta da aka adana a gidan.

    Rahotanni sun ce fasa gilashi suka yi domin samun shiga asalin gidan, sannan suka yi satar suka fita suka tafi a mota.

    Ministan al'adu na Faransa Rachida Dati ta ce babu wanda aka raunata, amma an rufe gidan tarihin na Louvre na kwana ɗaya.

  14. Afghanitan da Pakistan sun amince da yarjejeniyar tsagaita wuta

    Afghanistan

    Asalin hoton, AFP via Getty Images

    Ma'aikatar harakokin wajen Qatar ta ce Afghanistan da Pakistan sun amince su tsagaita wuta bayan cimma yarjejeniya tsakaninsu tare da shiga tsakanin Qatar da Turkiya a Doha.

    Wakilin BBC ya ce dukkaninsu Pakistan da Afghanistan sun amince su ci gaba da tattaunawa domin dorewar tsagaita wutar.

    Jiragen yakin Pakistan sun kai jerin hare-hare a kan iyakar Afghanistan a ranar Juma'a wanda ya kawo karshen fadan da ya barke a makon da ya gabata tsakanin kasashen biyu.

    Pakistan ta zargi Afgahnistan da ba mayaka mafaka, zargin da Kabul ta musanta.

  15. Hamas na yunƙurin kai hari kan fararen hula a Gaza - Amurka

    Amurka

    Asalin hoton, Getty Images

    Amurka ta ce tana da abin da ta kira kwararan hujjoji cewa Hamas na shirin saba yarjejeniyar tsagaita wuta ta hanyar kai hari kan fararen hula a Gaza.

    Ma'aikatar harakokin wajen Amurka ta ce idan har kungiyar ta ci gaba da kai harin, za a dauki mataki domin kare mutanen Gaza da kuma mutunta yarjejeniyar tsagaita wutar.

    Ana ta kai ruwa rana ne tsakanin ɓangarorin saboda gawarwakin da Hamas ta yi garkuwa da su da har zuwa yanzu ba ta gama miƙawa ba.

  16. An gudanar da zanga-zangar adawa da manufofin Trump a Amurka

    Trump

    Asalin hoton, FREDERIC J. BROWN/AFP via Getty Images

    Dubban mutane ne suka shiga zanga-zanga a sassan Amurka ta adawa da manufofin shugaban ƙasar Donald Trump.

    An gudanar da zanga-zangar da aka yi wa take da 'No Kings' a jihohin Amurka 50 har kusa da gidan Donald Trump a Florida, inda suke danganta Trump cewa yana nuna kamar shi sarki ne.

    Masu zanga-zangar kenan a birnin New York Masu zanga-zangar na adawa ne da manufofin gwamnatin Trump na korar baki da kuma girke jami'an tsaro tare da korar ma'aikata.

    karo na uku ke nan da ake hada gangami tun sake hawan Trump mulki a Fadar White House a watan Janairu.

  17. Yau za a binne Raila Odinga

    Raila

    Asalin hoton, Reuters

    A yau Lahadi za a binne tsohon Firaministan Kenya Raila Odinga. Za a binne shi ne bayan kwana uku na makokin mutuwar jagoran adawar kasar Kenya.

    A makon da ya gabata ne Mr Odinga ya rasu yana da shekara 80. Sau biyar yana tsayawa takarar shugaban kasa amma ana kada shi.

    Ya taba yin Firaminista tsawon shekara biyar a gwamnatin hadaka. A jiya Asabar dubban mutanen Kenya ne suka halarci gagarumin taron yin bankwana da shi a babban filin wasa na Kisumu.

  18. Ya kamata a ƙara ƙaimi wajen yaƙi da talauci a Najeriya - Atiku

    Atiku Abubakar

    Asalin hoton, Atiku Abubakar

    Tsohon shugaban Najeriya Atiku Abubakar ya bayyana talauci a matsayin ɗaya daga cikin manyan abubuwan da ke kawo tsaiko ga cigaban duniya.

    Atiku ya bayyana haka ne a shafukansa na sada zumunta a cikin jawabinsa na Ranar Yaƙi da Talauci ta Najeriya, inda ya ƙara a cewa abin takaici ne yadda Najeriya ta kasance gaba-gaba cikin ƙasashen da suka fi fama da talauci.

    A cewar Atiku, manyan abubuwan da suke jawo talauci sun haɗa da "jahilci da rashin tsaro da cututtuka," in ji shi, sannan ya yi kira ga gwamnati da dukkan masu ruwa da tsaki da su haɗa ƙarfi da ƙarfe wajen magance matsalar.

    "Ya kamata gwamnati da ƙungiyoyi masu zaman kansu da sauran masu ruwa da tsaki duk a taru a haɗa hannu domin yaƙi da talauci a Najeriya. Abin ban haushi ne a ce Najeriya muna cikin ƙasashen da aka fi talauci, shi ya sa nake kira da a ba al'ummar ƙasar muhimmanci domin magance matsalar nan ta talauci."

  19. Isra'ila ta zargi Hamas da saɓa alƙawarin yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza

    Netanyahu

    Asalin hoton, Reuters

    Isra'ila ta ce ta karbi ƙarin gawarwakin mutun biyu cikin waɗanda Hamas ta yi garkuwa da su, kamar yadda daftarin yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza ya ƙunsa.

    Wakilin BBC ya ce hukumomin Isra'ila sun ce Hamas ta saɓa yarjejeniyar tsagaita wuta ta hanyar jinkirin miƙa sauran gawarwakin na waɗanda suka mutu, amma ta yi garkuwa da su, inda Isra'ila ta ce da gangan Hamas ke jan ƙafa.

    Sai dai Hamas ta ce rufe mashigar Rafah ne ke kawo tsaiku ga miƙa sauran gawarwakin mutanen. Hamas ta ce rufe mashigar tsakanin Gaza da Masar na hana shigar da kayayyakin da take buƙata domin aikin gano gawarwakin da baraguzan gini suka danne.

  20. Buɗewa

    Jama'a barkanmu da safiya, barkanmu da sake haɗuwa a wannan shafin namu na labaran kai-tsaye.

    Da fata za ku kasance tare da mu.