'Ɗan tsohon jagoran Iran, Mojtaba Khamenei, na nan da ransa cikin ƙoshin lafiya'

Asalin hoton, Isna
Kafofin watsa labaran Iran sun ruwaito cewa Mojtaba Khamenei, ɗan tsohon jagoran addinin Iran, Ayatollahi Khamenei, yana nan da ransa cikin ƙoshin lafiya.
Kamfanin dillancin labarai na Mehr ya ruwaito cewa Mojtaba yana nan “yana nazari tare da duba ayyukan da suka shafi ƙasar, ciki har da nazarin waɗanda suka yi shahada da sauran al’amuran yau da kullum.“
Kwana huɗu da suka gabata ne hare-haren Isra’ila da Amurka a ofishin Ali Khamenei suka yi ajalin tsohon jagoran ƙasar.
Daga bisani kuma aka ruwaito cewa matarsa Mansoureh Khojasteh Bagherzadeh, wadda ta kwashe kusan kwana uku tana kwance a cikin wani mawuyacin hali ta rasu.
A lokacin harin, Zahra Haddad Adel, matar Mojtaba Khamenei da ƴa da surukin Ali Khamenei, da wani jikansa duk sun mutu.
Mojtaba ne na biyu a cikin ƴaƴan Ali Khamenei, kuma ana ambata shi a matsayin wanda zai iya maye gurbinsa.



















