Rufewa
Masu bin wannan shafi na kai-tsaye nan muka kawo ƙarshensa, sai kuma idan mai duka ya kai mu.
Amma kafin nan a madadin sauran abokan aiki, muke cewa mu kwana lafiya.
Wannan shafi ne da ke kawo muku muhimman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar 9 ga watan Satumba, 2025.
Usman Minjibir, Isiyaku Muhammed da Aisha Babangida
Masu bin wannan shafi na kai-tsaye nan muka kawo ƙarshensa, sai kuma idan mai duka ya kai mu.
Amma kafin nan a madadin sauran abokan aiki, muke cewa mu kwana lafiya.

Asalin hoton, Reuters
Ƙungiyar Hamas ta ce ba a kashe shugabanninta da Isra'ila ta kai wa hari a birnin Doha na ƙasar Qatar.
Sai dai ƙungiyar ta ce harin ya kashe wasu mambobinta biyar.
Rahotonni sun ce an kai harin ne a lokacin da jagororin ƙungiyar ke tattaunawa kan tsagaita wutar yaƙin Gaza.
Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce lokaci ya yi da jagororin Hamas za su daina samun kariya a duk inda suke a faɗin duniya.
Tuni dai Qatar ta yi Allah wadai da harin da ta kira na rashin mutunci.
Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres ya ce harin keta alfarma da mutuncin Qatar ne.
Qatar - wadda jagororin Hamas ke zaune a cikinta tsawon shekaru - ta kasance mai shiga tsakani a tattaunawar tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da Hamas.

Asalin hoton, Uba Sani/ X
Gwamnatin jihar Kaduna ta gargaɗi makarantu masu zaman kansu a faɗin jihar da su guji yin ƙarin kuɗin makaranta ba tare da sahalewar gwamnati ba.
Cikin wata sanarwa da babbar darakta mai kula da makarantu masu zaman kansu na ma'aikatar ilimin jihar, Mercy Bainta Kude ta fitar ta ce gwamnati ba ta amince da yin ƙarin kuɗin makaranta ba tare da saninta ba.
Matakin na zuwa ne a daidai lokacin da aka koma zangon farko na sabuwar shekarar karatu a ƙasar.
Sanarwar gwamnatin ta ce bai kamata makarantu masu zaman kansu su ƙara kuɗin makaranta ba a daidai lokacin da gwamnatin jihar ke shirin rage kuɗin makarantar.
Sanarwar ta ambato wasu ƙa'idoji bakwai da suka ce dole sai makaranta ta cika su idan tana son ƙara kuɗin makanta, ciki har da kai shekara uku bayan ƙari na ƙarshe da kuma amincewa ƙungiyar iyayen yara.
Aƙalla mutum 71 ne aka kashe a wani harin tsakar dare da mayaƙa masu alaƙa da ƙungiyar IS suka kai a gabashin DR Congo.
Majiyoyin cikin gida sun ce waɗanda suka mutun na halartar jana'iza a lardin Arewacin Kivu a lokacin da mayaƙan suka far musu.
Maharan sun yi ta saran mutanen da adduna tare da ƙona gidaje, tare da buɗe wuta kan waɗanda suka yi yunƙurin guduwa.
Tuni dai ƙungiyar ta ɗauki alhakin kisan kiyashin da ya auku a garin Lubero da ke lardin.

Asalin hoton, EPA/Shutterstock
Shugaba Emmanuel Macron na Faransa ya naɗa babban abokinsa, Sébastien Lecornu a matsayin sabon firaministan ƙasar, kwana guda bayan ƙuri'ar rashin amincewa da tsohon firaministan François Bayrou.
Lecornu mai shekara 39, na daga cikin mutanen da ake ganin za su samu matsayin.
Ya shafe shekara uku a matayin ministan dakarun tsaron ƙasar, mai kula da matsayin Faransa a yaƙin Rasha da Ukraine.
Tun da farkjo a yau ne Mista Bayrou ya ziyarci Macron domin miƙa masa takardar ajiye aikinsa a matsayin minista, lamarin da ya share masa hanyar zama firaminista na biyar a wa'adin Macron na biyu.
Lecornu zai fuskanci ƙalubale iri guda da na wanda ya gada, ciki har da rage yawan kuɗin kasafin ƙasar.
Faransa na fama da matsalar bashi, inda farkon shekarar nan bashin da ake bin ƙasar ya kai euro tiriliyan 3.3.

Asalin hoton, NNPCL
Ƙungiyar masu dakon man fetur a Najeriya, NUPENG ta dakatar da yajin aikin da ta fara bayan cimma yarjejeniyar da hukumomin matatar Dangote.
A ranar Litinin ne ƙungiyar ta fara yajin aiki domin nuna damuwarta kan matakin Dangote na ƙin barin ma'aikatan matatarsa su shiga cikin ƙungiyar.
Cikin wani saƙo da ƙungiyar ta wallafa a shafinta na X, ta bayyana cewa yarjejeniyar da suka cimma da matatar ɗangote da sauran rukunonin kamfanin ita ce za a bai wa direbobin manyan motocin dakonsu damar shiga ƙungiyar bisa raɗin kansu, matakin da matatar ɗangoten ke adawa da shi.
Yajin aikin ya haifar da fargabar samun ƙarancin man fetur a ƙasar.
An shawo kan ƙungiyar ne bayan tattaunawar sulhu ta kwana biyu da ministan ƙwadagon ƙasar ya jagoranta tare da haɗin gwiwar hukumar tsaro ta farin kaya DSS.
Hukumomin matatar sun amince cewa ma'aikatansu na da damar yin ƙungiya.

Asalin hoton, NNPCL/X
Matatar mai ta Ɗangote a Najeriya ta ce yajin aikin ƙungiyar masu dakon man fetur ta NUPENG ba zai janyo ƙarancin man fetur a ƙasar ba kamar yadda ake fargaba.
Kakakin matatar, Anthony Chiejina babu wata barazana game da yain aikin ƙungiyar direbobin tankar.
Yajin aikin da aka fara a yau Litinin na zuwa ne bayan da matatar Dangote ta ɗauki sabbin direbobi da za su yi dakon mai daga matatar zuwa gidajen man ƙasar.
Wani abu da bai yi wa ƙungiyar masu dakon man daɗi ba, waɗanda suke ganin matakin a matsayin barazana ga aikinsu.
Kafin fara aikin matatar Dangote a shekarar da ta gabata, Najeriya na shigo da kusan duka tataccen man fetur da take amfani da shi, duk kuwa da kasancewar mai ɗimbin arzikin man fetur a nahiyar Afirka.
Wani jami'in Hamas ya shaida wa BBC cewa harin da Isra'ila ta kai Qatar, ta kai shi ne kan wakilan Hamas da ke halartar taron tsagaita wuta a Qatar
Qatar na a matsayin mai shiga takanin Isra'ila da Hamas, kuma tun watan Oktoban 2023 take karar bauncin tattaunawar sulhu tsakanin angarorin biyu.
A ranar Lahadi ne Hamas ta ce ta yi maraba da ''wasu shawarwarin'' da Amurka ta bayar kan yadda za a cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a yain Gaza da ta samu ta hannun masu shiga tsakani.

Asalin hoton, AFP
Ma'aikatar harkokin wajen Qatar ta yi Allah wadai da harin da Isra'ila ta kai birnin Doha na ƙasar Qatar.
Yayin da yake jawabi ta gidan talbijin na ƙasar, kakakin ma'aikatar, Esmail Baghaei ya ce harin ya ''saɓa wa dokokin duniya'', sannan ya keta mutuncin ƙasar Qatar da masu tattaunawar sulhun''.
Ya ƙara da cewa dole matakin ya zama ''kyakkyawan gargaɗi ga ƙasashen yankin da ma duniya baki-ɗaya''.
A ƙarshen watan Yuni ne Iran da Isra'ail suka cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a yaƙin da suka yi na kwana 12.

Asalin hoton, Getty Images
Jami'ai a fadar gwamnatin Amurka sun shaida wa BBC cewa an ''sanar'' da gwamnatin Trump dangane da harin da Isra'ila ta kai Doha tun kafin ƙaddamar da shi.
Harin da Isra'ila ta kai wa Qatar - babbar ƙawar Amurka da ba ta cikin ƙungiyar Nato - ya aza ayoyin tambayoyi kan masaniyar Amurka da ma hannunta a harin.
Akwai dakarun sojin Amurka kusan 10,000 a Qatar.
Isra'ila ta ce ta kai harin ne kan manyan jagororin Hamas a Doha, babban birnin Qatar.

Asalin hoton, Reuters

Asalin hoton, Reuters

Asalin hoton, Reuters

Asalin hoton, Reuters
Isra'ila ta ce ita ce ta kai hari kan shugabannin Hamas a Doha, babban birnin Qatar.
A cikin wata sanarwa da ta fitar, rundunar sojin Isra'ila ta ce: "Dakarun IDF da na ISA sun ƙaddamar da harin kai-tsaye" kan shugabannin ƙungiyar Hamas.
Sanarwar ta ƙara da cewa: "A tsawon shekaru, waɗannan shugabanni na Hamas sun jagoranci ayyukan soji na ƙungiyar, kuma suna da hannu dumu-dumu a cikin mummunan kisan kiyashi da aka yi a ranar 7 ga watan Oktoba, kuma sun ci gaba da kitsawa da tafiyar da yaƙin da ake yi da Isra'ila.
"Kafin ƙaddamar da harin, an ɗauki matakan kauce wa cutar da fararen hula, ciki har da yin amfani da makaman da ba sa kuskure da kuma ƙarin bayanan sirri," a cewar sanarwar
"Rundunar IDF da abokiyar aikinta ISA za su ci gaba da yin aiki kan jiki kan ƙarfi domin murƙushe ƙungiyar wadda ke da alhakin kai harin ranar 7 ga watan Okotoba."

Asalin hoton, Reuters
Isra'ila ta ƙaddamar da hari kan babban birnin Qatar, Doha, da nufin kai hari kan manyan jagororin Hamas.
Rahotanni sun bayyana cewa jagororin sun je Doha ne domin tattaunawa kan kudurin yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza na baya bayan nan.
Wani babban jami'i a Isra'ila ya shaida wa manema labarai a ƙasar cewa waɗanda aka kai wa harin sun haɗa da Khalil al Hayya, shugaban Hamas a Gaza.
An ji ƙarar fashewa da dama a yankin Katara da ke birnin.
Wani bidiyo da aka wallafa a intanet ya nuna yadda hayaƙi ya turnuƙe sararin samaniyar yankin. Qatar ta yi Allah-wadai da harin.

Asalin hoton, Reuters
Firaministan Nepal, KP Sharma Oli, ya sauka daga muƙaminsa, in ji sakatariyarsa a cikin wata sanarwa.
Sanarwar ta bayyana cewa ya sauka ne domin ba wa ƙundin tsarin mulki ƙasar damar samar da mafita ga rikicin da ake ciki a halin yanzu.
Tun safe ne dai masu masu zanga-zanga kan cin hanci da rashawa suka mamaye babban birnin Kathmandu da sauran sassan Nepal.
An kai hari tare da lalata gidajen wasu manyan ‘yan siyasa, ciki har da na firaministan da tsohon firaminista Sher Bahadur Deuba.
An kuma kai hari kan ofisoshin jam’iyyu na siyasa.
Mohan Regmi, daraktan gudanarwa na Asibitin Civil Service, ya shaida wa BBC cewa mutum biyu sun rasu yayin zanga-zangar yau, Talata. Ya ce yanzu haka ana kula da mutum 90 a asibitin.

Asalin hoton, Reuters

Asalin hoton, Reuters

Asalin hoton, Reuters

Asalin hoton, Reuters

Asalin hoton, @NigeriaCAA
Hukumar kula da jiragen sama ta Najeriya (NCAA) ta kira dukkanin kamfanonin jiragen sama na cikin gida taro a Abuja kan matsalar ɗage tashin jirage da mayar wa da fasinjoji kuɗaɗensu.
Mai magana da yawun NCAA, Michael Achimugu, ya ce taron zai gudana ranar Laraba a ofishin hukumar.
Wannan na zuwa ne kusan sa’o’i 24 bayan Achimugu ya ce hukumar tana da ikon da gwamnatin Tarayya ta ba ta “na fara bayyana sunaye da tona kamfanonin jiragen sama da ke ɗage ko soke tashin jirage, musamman a lokutan da ba a saba ba, ba tare da samar da kwanciyar hankali ga fasinjojin da abin ya shafa ba kamar yadda sashe na 19 na dokokin jiragen sama na Najeriya ya tanada.
Ya bayyana cewa za a tattauna batutuwan da suka shafi ɗage tashiwar jirage, da halayen fasinjoji masu tada husuma da yadda ake mu’amala da su, da batutuwan mayar wa da fasinjoji kuɗi da biyan diyya da ajiye na'urar RFID wato wata ƙaramar na’ura da ke ajiye bayani kuma ana amfani da ita wajen sadarwa da sauran na’urori a cikin jaka da kuma hanyoyin kare ma’aikatan jirgi daga fasinjoji.
Ya kuma jaddada cewa bisa ƙa’ida, idan aka ɗage tashin jirgi tsakanin ƙarfe 10 na dare zuwa 4 na safe, dole a samar wa fasinjoji masauki.
Ya gargaɗi kamfanonin jirage da su daina barin fasinjoji cikin wahala tare da barin jami’an NCAA su fuskanci wulaƙanci.
Achimugu ya ce: “Idan kuna son a kira ku kamfanonin jirage na duniya, ku inganta ayyukanku, don mutuncinku da kuma amincin fasinjoji.

Asalin hoton, Nigerian Senate/X
Majalisar dattawa ta Najeriya ta ƙi amincewa da buƙatar Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan mai wakiltar Kogi ta Tsakiya kan komawa bakin aiki, inda ta ce har yanzu ba a kammala shari'ar dakatar da ita ba.
Natasha ta rubuta wasiƙa ne a ranar 8 ga Agustan bana, inda a ciki ta sanar da majalisar shirinta na komawa bakin aiki a ranar 4 ga watan Satumba, inda ta ce wa'adin wata shida da aka dakatar da ita ya cika.
Ta ce kotun tarayya ta yanke hukunci a watan Yuln da ya gabata cewa dakatarwar da aka mata ba daidai ba ne, sannan ta umarci majalisar ta mayar da ita bakin aiki.
Amma a wata wasiƙar martani da majalisar ta rubuta a ranar 4 ga Satumba, wadda muƙaddashin akawun majalisar, Yahaya Danzaria ya sanya wa hannu, ya ce ba za ta koma bakin aiki ba har sai an kammala shari'ar lamarin a kotu.
Ya ce, "wannan maganar tana gaban kotu, kuma majalisar ba za ta yi komai a game da batun komawarki bakin aiki ba har sai kotu a kammala shari'ar baki ɗaya. Don haka a yanzu babu abin da ofishinmu zai iya yi a game da wannan batu."
A ranar 6 ga watan Maris ne dai majalisar dattawa ta dakatar da sanatana bayan ta yi musayar yawu da shugaban majalisar, Sanata Godswill Akpabio.

Asalin hoton, Reuters
Nepal ta dage haramcin amfani da shafukan sada zumuntar da ta yi wanda matakin ya janyo zanga-zangar gama gari.
Mutum 19 aka kashe inda aka jiwa wasu fiye da 100 rauni a ranar Litinin bayan 'yan sanda sun harba hayaki mai sa hawaye da kuma amfani da harsashin roba akan masu zanga-zangar da ke adawa da irin cin hanci da rashawar da ake tafkawa a kasar.
Wakiliyar BBC ta ce har yanzu akwai yanayi na zaman dar-dar akan tituna kasar bayan an tarwatsa masu zanga-zangar kuma hakan na da nasaba da dokar takaita zirga-zirgar da aka sanya a wasu biranen kasar.
A makon daya gabata ne gwamnatin Nepal din ta bayar da umarnin a toshe dukkan wasu kafafan sada zumunta ciki har da Facebook da kuma YouTube saboda gaza cika sharudan yin rijistar da aka ware musu lokaci.

Asalin hoton, Reuters
Sojojin Isra'ila sun umarci "dukkan mazauna" birnin Gaza da su kwashe dukkan abin da za su iya kwashewa domin suna shirye-shiryen afka wa birnin da luguden wuta.
Sun ce za su far wa birnin da yaƙi ne matuƙar ƴan Hamas suka ƙi amincewa da sakin sauran Isra'ilawa da suke garkuwa da su.
A wata sanarwa da rundunar sojin Isra'ila ta wallafa a shafin X, ta ce za ta fara ƙaddamar da luguden wuta mai zafi a birnin na Gaza, wanda hakan ne a cewarta ya sa take gargaɗin mazauna birnin su fice domin tsira da rayuwar su.
"Dakarunmu a shirye suke su murƙushe Hamas baki ɗaya a birnin Gaza," in ji Avichay Adraee a madadin rundunar.
A watan jiya ne dai majalisar Isra'ila ta amince da shirin dakarun ƙasar na ƙwace birnin Gaza, inda dubban Falasɗinawa ke zaune.

Asalin hoton, Getty Images
Kotun Kolin Thailand ta daure tsohon firaiministan kasar Thaksin Shinawatra. Alkalin kotun da ke Bangkok, ya shaida masa cewa ba abi tsarin shari'a ba wajen tsare shi da aka yi a wani asibiti bayan an same shi da laifin aikata cin hanci.
Daga nan ya bayar da umarnin cewa za a tsare Mr Thaksin a gidan yari tsawon shekara guda.
Tsohon firaiministan na Thailand ya amince da hukuncin inda ya ce zai yi dukkan abin da aka umarce da yi ba tare da wata matsala ba.
A watan da ya gabata ne aka tursasa wa 'yarsa Shinawatra yin murabus daga mukamin firaiminista.

Asalin hoton, Tinubu X
Tsohon ɗantakarar gwamnn jihar Kogi, Sanata Dino Melaye ya ce ganin yadda gwamnatin Najeriya a ƙarƙashin Bola Tinubu ke cin bashi, yana ganin gwamnatin za ta iya cin bashi daga kamfanin hada-hadar kuɗi na intanet wato Opay da moniepoint.
Dino ya bayana haka ne a zantawarsa da tashar ARISE a ranar Litinin, inda ya zargi gwamnatin da jefa ƴan ƙasar cikin mawuyacin hali ta hanyar ciyo basussuka da yawa, waɗanda ya ce ba a ganin amfanin su a ƙasa,
"Ana fama da yunwa sosai a ƙasar nan. Me ya sa shugaban ƙasa zai ciyo basin dala biliyan 1.7 daga bankin duniya? me ya sa majalisar dattawa ta amince da bashin dala biliyan 21 zuwa yanzu, sannan akwai wasu da ke tafe?"
Ya ƙara da zargin cewa "wannan gwamnatin ce wadda ta fi sakaci a tarihin Najeriya. Idan ana samun kuɗin shiga, me ya za kuma ake cin bashi. Ba za mu yi mamaki ba idan nan gaba kaɗan muka ga shugaban ƙasa ya fara cin bashi daga Opay da Moniepoint."