Rufewa
Masu bin shafin namu sai gobe idan Allah ya kai mu
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya
Ibrahim Yusuf Mohammed da Abdullahi Diginza
Masu bin shafin namu sai gobe idan Allah ya kai mu
Rundunar dakarun RSF a Sudan ta ce ta kama garin Al-Tina na Arewacin Darfur, inda ta kori sojojin da ke biyayya ga gwamnatin ƙasar.
Rundunar ta fitar da wani hoton bidiyo na mayaƙanta suna murna a ƙarƙashin wata alama da ke ɗauke da sunan garin.
Garin na Al-Tina na kan iyakar ƙasar da Chadi, kuma ana yawan samun rahotannin faɗace-faɗace tsakanin dakarun RSF da dakarun Chadi da ke tsallakowa lokaci zuwa lokaci.
Yawancin waɗanda ke zaune a garin ƴan ƙabilun Zaghawa da Fur ne waɗanda ba Larabawa ba.
Yaƙin basasar da aka shafe shekaru uku ana yi a Sudan ya janyo mutuwar dubban ɗaruruwan mutane, da kuma raba miliyoyi da gidajensu.

Asalin hoton, Getty Images
Barcelona ta koma matakin farko a kan teburin La Liga, bayan doke Levente 3-0 a wasan mako na 25 da suka buga ranar Lahadi.
Ƙungiyar Camp Nou ta ci ƙwallayen ta hannun Marc Bernal da De Jong da kuma Fermín López.
Da wannan sakamakon Barcelona tana ta ɗaya a kan teburi da maki 60, sai Real Madrid ta biyu da tazarar maki ɗaya tsakani.
Real Madrid ta ci karo da komabaya, sakamakon da ta yi rashin nasara 2-1 a gidan Osasuna ranar Asabar.
Ranar Laraba, Real Madrid za ta karɓi bakuncin Benfica a wasa na biyu a neman cike gurbin zuwa zagaye na biyu a Champions League.
Wasan farko da suka buga a Portugal, Real ce ta yi nasara a wasan da Vinicius Junior ya yi zargin an yi masa kalaman wariya - Uefa tana bincike kan lamarin.
Ministan harkokin wajen Iran ya ce tawagar ƙasar da ke tattaunawa da Amurka kan shirin nukiliyarta na ci gaba da duba tayin da Amurkan ta yi matana.
Abbas Araghchi ya shaida wa gidan talbijin na Amurka cewa wataƙila a ranar Alhamis zai gana da jakadan Trump na musamman Steve Witkoff a binrin Geneva.
Mista Araghchi ya sha nanata cewa inganta sinadarin nukiliyar Iran bai kai matsayin da za a yi yarjejeniya a kansa ba.
A makon da ya gabata ne Mista Trump ya bai wa Tehran kwanaki 10 ta amince da yarjejeniya ko ta fuskanci matakin soji.
Sai ministan harkokin wajen na Iran ya ce har yanzu akwai damar cimma yarjejeniyar diplomasiyya.

Asalin hoton, Getty Images
Jami'an tsaron farin kaya a Amurka sun harbe wani mutum da ya yi yunƙurin tsallaka wani shingen tsaro a harabar gidan Donald Trump da ke Florida.
Shugaban ƙasar na birnin Washington lokacin da lamarin ya faru, jami'ai sun ce mutumin na ɗauke da bindida da jarkar mai, kuma an harbe shi lokacin da ya ɗaga makaminsa.
Hukumomi ba su bayyana sunansa ba, amma kafafen yaɗa labaran Amurka sun ce sunansa Austin Martin mai shekara 21 daga arewacin Carolina.
Shugaba Trump ya tsallake rijiya da baya yayin da aka kai masa hari a shekarar 2024 lokacin yaƙin neman zaɓe.
An kuma yanke wa wani mutum hukuncin ɗauri a gidan yari bayan kama shi ɗauke da bindiga a inda Mista Trump ke wasan kwallon gof.

Asalin hoton, Fadar shugaban Najeriya
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya taya murna da waɗanda suka yi nasara a zaɓukan Abuja da jihohin Kano da Rivers.
A ranar Asabar ne INEC ta jagoranci gudanar da zaɓukan shugabannin ƙananan hukumomin Abuja, babban birnin ƙasar da na cike gurbi a jihohin Kano da Rivers.
Shugaba Tinubu ya buƙaci waɗanda suka yi nasara a zaɓukan su nuna kishin ƙasa da sadaukarwa, sannna su auki nauyin da al'umma suka ɗora musu da muhimmanci ta hanyar riƙon amana da aiki da gaskiya..
Jam'iyyar APC ce ta lashe ƙananan hukumomi biyar cikin shida na Abuja, yayin da PDP ta samu ɗaya.
Shugaban Najeriyar ya yaba wa ministan Abuja, Nyesom Wike saboda muhimman nasarorin da ya cimma waɗanda Tinubun ya ce sun taimaka wa APC samun nasara a zaɓukan.
A zaɓukan cike gurbin yanmajalisar jihohin Kano da Rivers ma jam'iyyar APCn ce ta yi nasara a duka kujerun.
Haka Shugaba Tinubu ya yaba wa hukumar za ben kasar INEC, da jami'an tsaro da ma waɗanda suka fita domin kaɗa ƙuri'ar, wadda ya ce an yi cikin kwanciyar hankali da lumana.

Asalin hoton, Reuters
Ukraine ta ce matakan tsaron sararin samaniyarta sun kakkaɓo wasu makamai linzami na Rasha guda 50 da kuma jirage marasa matuƙa kusan 300 cikin dare, inda suka lalata mafi yawansu.
Shugaba Zelensky ya ce hare-haren sun shafi ɓangaren makamashi, gine-ginen zama, da kuma layin dogo.
An ji karar fashewar abubuwa da dama a Kyiv kafin wayewar gari.
Babban birnin ƙasar ya daɗe yana fuskantar hare-haren cikin dare a cikin ƴan makonnin nan, inda sojojin Rasha suka tsananta kai hare-hare kan ababen more rayuwa na ɓangaren makamashi, lamarin da ya sanya mazauna garin da dama suka shiga mawuyacin hali sakamakon mummunan yanayin sanyin hunturu.
Tun da farko dai wani ɗan sanda ya rasa ransa an kuma jikkata wasu 15 sakamakon fashewar wasu abubuwa guda biyu a yammacin birnin Lviv da ke kusa da kan iyakar Poland.
A ranar Talata ne za a cika shekaru huɗu da mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine.

Asalin hoton, Reuters
Gwamnatocin ƙasashen Larabawa da na Musulmi sun yi alla-wadai da kalaman jakadan Amurka a Isra'ila Mike Huckabee, wanda ke nuni da cewa Isra'ila za iya mamaye yanki mai faɗin gaske a gabas ta tsakiya bisa hujjar Littafin Injila.
A wata hira da wani mai sharhi na Amurka mai ra'ayin mazan jiya Tucker Carlson, an tambayi Huckabee ko Isra'ila na da ƴancin mallakar wani yanki da aka bayyana a matsayin "Gabas ta tsakiya baki ɗaya".
Jakadan ya ce "zai yi kyau idan ta kwashe duka".
Amma ya ƙara da cewa Isra'ila ba ta neman yin hakan, amam ta na "neman aƙalla ta ci gaba da riƙe ƙasar da ta riga ta mamaye" da kuma kare al'ummarta.
A cikin wata sanarwar haɗin gwiwa da suka fitar, fiye da gwamnatoci goma da suka haɗa da Jordan da Masar da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, sun kira kalaman "masu haɗari da tayar da hankali", da kuma barazana ga yunƙurin kawo ƙarshen yaƙin Gaza.

Asalin hoton, Anadolu via Getty Images
Sudan ta ja wa Uganda kunne bayan da ta karɓi baƙuncin jagoran ƙungiyar ƴan tawaye ta Rapid Support Forces (RSF).
Ma'aikatar harkokin wajen ƙasar ta buƙaci mahukuntan Uganda da su nesanta kansu daga kwamandan RSF Hamdan Dagalo, wanda aka fi sani da Hemedti, inda ta zargi dakarunsa da aikata munanan laifuka a yaƙin da ake gwabzawa.
Khartoum ta ce tana son kiyaye dangantakar da ke tsakanin ƙasashen biyu amma ba za ta lamunci tsoma baki daga waje a cikin harkokinta ba.
Shugaban ƙasar Uganda, Yoweri Museveni, wanda ƙungiyar Tarayyar Afirka ta naɗa a matsayin mai taimakawa shiga tsakani, ya ce ganawarsa da shugaban ƙungiyar RSF a ranar Juma'a ta mayar da hankali ne kan hanyoyin kawo ƙarshen yaƙin basasar Sudan.

Asalin hoton, Reuters
Gwamnatin ƙasar Hungary ta ce za ta dakile sabon ƙudurin takunkumin da Tarayyar Turai ke niyyar ƙakabawa ƙasar Rasha, muddin Ukraine ta ƙi buɗe bututun da ke kai wa Budapest man fetur.
Tare da Slovakia, Hungary kuma tana barazanar katse wutar lantarki zuwa Kyiv matuƙar ba a sake buɗe bututun ba.
Man fetur ya daina bin bututun ne a watan Janairu bayan abin da Ukraine ta kira ɓarnar da jiragen saman Rasha suka yi.
Ƙasashen biyu dai su ne kan gaba wajen samun man fetur daga Rasha a cikin Tarayyar Turai.

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Najeriya (INEC) ta fara fitar da sakamakon zaɓen ƙananan hukumomin Abuja, da aka gudanar a ranar Asabar.
Sakamako daga runfunan zabe na kananan hukumomi shida na babban birnin tarayya Abuja sun farasamuwa ne sa'o'i kaɗan bayan hukumar zaɓe ta INEC ta kammala gudanar da zaɓukan.
Sakamakon zaɓen ƙananan hukumomi biyar daga cikin shida da ke birnin sun nuna cewa jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ta lashe ƙananan hukumomi huɗu (Abaji, AMAC, Bwari, Kwali) yayin da jam'iyyar PDP ta lashe ƙaramar hukuma ɗaya (Gwagwalada) kuma ana dakon sakamakon zaɓen ƙaramar hukumar Kuje.

Asalin hoton, Kano state Govt
Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta samu nasara a zaɓen cike gurbi na mazaɓar Ungogo da Kano Municipal a majalisar dokokin jihar Kano.
Gidan Talbijin na Ƙasar NTA ya ruwaito cewa a karamar hukumar Kano Municipal ɗan takarar jam’iyyar APC, Aliyu Nabil Daneji, ya samu nasara da ƙuri’u 7,484.
Jami’in tattara sakmakon zaɓen Farfesa Ibrahim Tajo Siraj ne ya bayyana sakamakon zaɓen tare da ayyana shi a matsayin wanda aka zaɓa.
Hakazalika, a mazaɓar Ungogo, ɗan takarar jam’iyyar APC, Aminu Sa’ad, ya samu nasara ne bayan ya samu ƙuri’u 8,975. Jami’in tattara sakmakon zaɓe, Farfesa Ali Tijjani Abdullahi, ya bayyana sakamakon zaɓen tare da ayyana shi a matsayin wanda ya lashe kujerar.

Asalin hoton, AFP
Mayaƙan ƙungiyar Rapid Support Forces RSF) sun ce sun ƙwace garin Al-Tina da ke arewacin Darfur, tare da fatattakar mayaƙan sa kai masu biyayya ga sojojin gwamnati.
Al'ummomin da ba Larabawa ba Akasarin mazauna garin da ke kan iyakar Sudan da Chadi, ba larabawa ba ne.
Wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya da aka wallafa a wannan makon ya ce RSF na kai wa waɗannan ƙungiyoyi hari ne a wani lamari da ke da "kamanceceniya da kisan kiyashi".
Ƙungiyar bayar da agajin ta MSF ta ce jirage marasa matuƙa na kai hare-hare a kasuwanni da makarantu, da cibiyoyin kiwon lafiya a Arewacin Darfur.
A farkon watan Fabrairu kaɗai, ta yi jinyar marasa lafiya sama da ɗari da sittin da suka samu raunuka sakamakon hare-haren jirage marasa matuƙa.
Yaƙin basasar da aka shafe shekaru uku ana yi a ƙasar Sudan ya yi sanadin mutuwar dubban ɗaruruwan mutane.

Asalin hoton, EPA
Shugaban Amurka Donald Trump ya ce zai sanya harajin da ya kai kashi 15 cikin 100 a kan ƙasashen duniya, yayin da ya ci gaba da nuna adawa da hukuncin da kotun kolin ƙasar ta yanke kan harajin shigo da kaya da ya ƙaƙaba baya.
Trump ya faɗa a ranar Juma'a cewa zai maye gurbin harajin da kotu ta soke da kaso 10% kan duk kayayyakin da ke shigowa Amurka.
Amma a ranar Asabar, ya sanar a shafinsa na dandalin Truth Social cewa za a ƙara wannan zuwa iyakar da aka yarda a ƙarƙashin wata dokar kasuwanci da ba a taɓa amfani da ita ba.
Wannan doka ta ba da damar waɗannan sabbin harajin su ci gaba da aiki har na tsawon watanni biyar kafin gwamnati ta nemi amincewar Majalisar dokoki.
an shirya cewa harajin na kashi 10 cikin 100 zai fara aiki ne a ranar Talata, 24 ga Fabrairu.
Ba a tabbatar tabbas idan ƙarin kashi 15 ɗin shi ma za zai fara aiki daga lokacin ba.

Asalin hoton, EPA
Ana ci gaba da nune-nunen yatsa tsakanin Pakistan da Afghanistan bayan da Islamabad ta kai munanan hare-hare ta sama kan maboyar ƴan ta'adda a ƙasar ta Afghanistan.
Pakistan ta ce ta kai hari kan irin waɗannan sansanoni guda bakwai a ranar Asabar ɗin da ta gabata, tana mai cewa mazaunansu sun aikata ta'asa na baya-bayan nan a Pakistan tare da zargin hukumomin Taliban na Afghanistan da ba su mafaka.
Ƙungiyar Taliban a Kabul ta yi alla-wadai da hare-haren.
Ta ce an kashe ko jikkata fararen hula da dama kuma ta sha alwashin mayar da martani.
Cikin makonni da suka gabata an samu ƙaruwar hare-haren ƴan bindiga a Pakistan ciki har da wanda aka kai a wani masallacin ƴan Shi’a a Islamabad, inda aka kashe sama da mutane 30.

Asalin hoton, Reuters
Fursunonin siyasa 1,557 a Venezuela ne suka nemi a yi musu afuwa a ƙarƙashin wata sabuwar dokar da aka kafa ranar Alhamis, in ji shugaban majalisar dokokin ƙasar.
Jorge Rodríguez, ɗan uwan shugaban rikon ƙwarya na Venezuela Delcy Rodríguez kuma na hannun daman tsohon shugaban ƙasar Nicolás Maduro, ya kuma ce an riga an saki "ɗaruruwan" fursunoni.
Daga cikin su har da ɗan siyasa Juan Pablo Guanipa, ɗaya daga cikin ƴan adawa da dama da suka soki dokar kan ware wasu fursunoni.
Amurka ta buƙaci Venezuela da ta gaggauta sakin fursunonin siyasa tun bayan da sojojin Amurka suka sace Maduro a wani samame da suka kai a ranar 3 ga watan Janairu.
Gwamnatin Venezuela dai ta daɗe ta na musanta cewa ta na tsare fursunonin siyasa.

Asalin hoton, Reuters
Tsohon Firaministan Birtaniya Boris Johnson ya ce kamata ya yi Birtaniya da ƙawayenta su tura dakarun soji da ba na yaƙi ba zuwa Ukraine, don yin abin da ya kira ''sauya tunanin" shugaban Rasha Vladimir Putin.
A wata hira da ya yi da BBC ranar Lahadi, Johnson ya ce ya kamata a tura sojoji zuwa yankunan da ake zaman lafiya domin gudanar da ayyukan da ba na faɗa ba.
A halin yanzu dai gwamnatin Birtaniya tana aiki ne tare da ƙawayenta don haɗa wata "gamayyar masu niyya" don samar da dakaru da za su tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Ukraine, amma sai dai idan an cimma yarjejeniyar kawo ƙarshen yaƙin.
Yayin da yake magana kwanaki kaɗan gabanin cika shekaru huɗu da fara yaƙin, Johnson, wanda ya kasance firaminista a lokacin da aka fara rikicin, ya kuma ce tun da farko akwai yiwuwar iya daƙile rikicin da ƙawancen ƙasashen Yammacin duniya sun mai da hankali kan karuwar cin zalin da Putin ke yi tun bayan da ya mamaye yankin Crimea a shekara ta 2014.

Dalibai a jami'o'i da dama da ke faɗin kasar Iran sun gudanar da zanga-zangar nuna adawa da gwamnati, wanda hakan ne gangami na farko tun bayan wanda aka gudanar a watan da ya gabata da hukumomi suka yi.
BBC ta tantance bidiyon masu zanga-zangar da suka yi tattaki a harabar jami'ar fasaha ta Sharif da ke Tehran babban birnin ƙasar a ranar Asabar inda daga baya aka ga an yi arangama tsakanin su da magoya bayan gwamnati.
An gudanar da zaman dirshan a wata jami'ar Tehran, kuma an yi wani gangami a yankin arewa maso gabashin ƙasar inda ɗalibai ke karrama dubban mutanen aka kashe a zanga-zangar da aka yi a watan Janairu.
Amurka dai na ci gaba da ƙara yawan sojojinta da ke jibge a kusa da Iran, kuma shugaba Donald Trump ya ce yana tunanin kai wa Iran takaitaccen harin soji.
Amurka da ƙawayenta na Turai na zargin cewa Iran na yunkurin ƙera makamin nukiliya, lamarin da Iran ta daɗe ta na musantawa.
Masu bin shafin BBC Hausa-kai tsaye barkanmu da safiyar wannan rana ta Lahadi, da fatan kun wayi gari lafiya.
Ku ci gaba da biyo domin samun labarai da rahotonnin abubuwan da ke faruwa a faɗin duniya.