Rufewa
Jama'a a nan muka kawo ƙarshen wannan shafin na labaran kai-tsaye na wannan rana.
Sai kuma Laraba idan Allah ya kai mu.
Da fata kun ji daɗin kasancewa tare da mu.
A madadin sauran abokan aiki, ni Isiyaku Muhammed nake cewa mu kwana lafiya.
Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Talata 20 ga watan Janairun 2026.
Daga Aisha Babangida, Haruna Kakangi da Ahmad Bawage
Jama'a a nan muka kawo ƙarshen wannan shafin na labaran kai-tsaye na wannan rana.
Sai kuma Laraba idan Allah ya kai mu.
Da fata kun ji daɗin kasancewa tare da mu.
A madadin sauran abokan aiki, ni Isiyaku Muhammed nake cewa mu kwana lafiya.

A Najeriya, yau aka shiga rana ta biyu a yajin aikin sai baba-ta-gani da ma'aikatan hukumar yankin babban birnin tarayya Abuja suka shiga tun jiya.
Ma'aikatan sun shiga yajin aikin ne bisa neman a biya masu wasu muhimman bukatu da suka ce sun dade suna bibiyar a biya masu su, amma suna zargin hukumomin da abin ya shafa sun yi biris da lamarin.
Sai dai wani mai magana da yawun ministan babban birnin tarayyar ya ce an biya wa ma'aikatan bukatu goma cikin sha hudu da suke korafi kan su.
Amma shugabanin kungiyar kwadagon sun musanta wannan ikirari.


Asalin hoton, Getty Images
Gwamnatin Syria ta sanar da cimma yarjejeniyar tsagaita wuta ta kwanaki huɗu da ƙungiyar SDF ta Ƙurɗawa, bayan an cimma matsaya kan makomar yankin Hasakeh wanda akasari Kurɗawa ne a yankin.
Ƙungiyar SDF ta ce ta duƙufa wajen tabbatar da tsagaita wutar, muddin ba ta fuskanci wani hari nan gaba ba.
Wakilin Amurka na musamman a Syria Tom Barrack, ya ce wannan shirin ne dama mafi muhimmanci da Kurɗawa ke da ita a yanzu a Syria.
Tun da farko a yau, SDF ta ce ta janye dakarunta daga sansanin Al Hol, inda ake riƙe da dubban mata da yaran mutanen da ake zargi ƴan ƙungiyar IS ne.

Asalin hoton, Getty Images
Kasuwar hannun jarin Amurka ta samu koma-baya bayan masu zuba jari sun fara jan kafa, saboda batun Greenland da kuma fargabar ɓarkewar yaƙin kasuwanci a tsakanin ƙasashen da ke maƙwabtaka da tekun Atalantika.
Kasuwar ta karye da kusan kashi ɗaya da rabi a yau, bayan an rufe kasuwar a jiya Litinin saboda hutun aiki.
Kasuwannin Turai kuma sun samu koma-baya a rana biyu a jere. Darajar dala ta faɗi, a daidai lokacin da zinare da azurfa suke cigaba da samun tagomashi.

Asalin hoton, AMNESTY INTERNATIONAL
Ƙungiyar kare hakkin ɗan'adam ta Amnesty International, ta buƙaci hukumomin Najeriya da su gaggauta ceto mutum 166 da aka yi garkuwa da su a wani coci a karamar hukumar Kajuru na jihar Kaduna.
Lamarin dai ya faru ne ranar Lahadi lokacin da mutanen ke ibada, inda aka ɗauki mutanen ciki da kananan yara da kuma masu juna biyu.
Sanarwar da ƙungiyar ta fitar, ta ce lamarin ya sake nuna gazawar gwamnatin Najeiya wajen kawo karshen matsalar kashe-kashe da kuma garkuwa da mutane a ƙasar.
"Mazauna yankin sun faɗa mana cewa ƴanbindiga sun kutsa cikin ƙauyen - inda suka riƙa bin coci-coci suna fitar da masu ibada a wasu majami'u uku da aka kai wa samame. Abin fargaba ne cewa har yanzu ƴanbindiga na cin karensu babu babbaka a arewacin Najeriya," in ji Amnesty.
Ƙungiyar ta kuma yi Alla-wadai da musanta batun garkuwan da ƴansanda da kuma gwamnatin jihar Kaduna suka yi.
Ta buƙaci hukumomi su ɗauki matakan da suka dace wajen magance matsalar garkuwa da mutane da ta addabi arewacin ƙasar.

Asalin hoton, Getty Images
Masu aikin ceto na ta ƙoƙarin kawar da ɓaraguzan wani babban kanti a Karachi, birnin mafi girma a Pakistan, bayan samun wata mummunar gobara, inda har yanzu ake neman mutum fiye da saba'in.
Masu aikin ceto na gaggawa sun ce suna aiki ne cikin tsanaki saboda akwai fargabar wani gefe na ginin Gul Plaza da ya lalace na iya ruguje wa.
Mahukunta sun ce zuwa yanzu an gano aƙalla gawarwaki 23 tun bayan da ginin ya kama wuta a ranar asabar.
Wani mutum da ya tsira ya ce wutar da hayaƙin sun yi saurin yaɗuwa, inda hayaƙin ya sumar da shi a lokacin da yake ƙoƙarin tserewa, sai dai ya farka ya ganshi a gadon asibiti.
Ya kuma ce har yanzu ba a ga ƴan uwan shi ba.

Rahotanni da ke fitowa sun nuna cewa an kama tsohon shugaban mulkin soja na Burkina Faso, Paul-Henri Sandaogo Damiba, a ƙasar Togo sannan aka kore shi zuwa Ouagadougou.
Sai dai har zuwa yanzu babu wata sanarwa a hukumance daga gwamnatocin Togo ko Burkina Faso da ke tabbatar da wannan rahoto.
An kifar da Damiba, tsohon laftanar kanal a juyin mulki a watan Satumban 2022, kuma tun daga lokacin yana zaman gudun hijira a birnin Lomé na Togo.
Gwamnatin sojin Burkina Faso ta sha zarginsa da shirya makarkashiyar tayar da hankula da yunƙurin kifar da gwamnatin da ke mulki a halin yanzu.
Wasu rahotannin kafafen yaɗa labarai, suna ambaton majiyoyin tsaro da cewa an kama Damiba tare da korar sa daga Togo, kodayake ba a bayyana ainihin inda aka kai shi ba amma kuma wasu na hasashen cewa mai yiwuwa an mayar da shi Burkina Faso.
An ce matakin ya biyo bayan sabbin zarge-zargen da gwamnatin Ouagadougou ta yi cewa Damiba yana da hannu a wani sabon yunƙurin juyin mulki da aka gano a farkon wannan watan.

Asalin hoton, INEC
Hukumar Zaɓe mai zaman kanta INEC, ta sanar da fara rabon katunan zaɓe na dindindin ga masu zaɓe gabanin zaɓen kananan hukumomi da za a gudanar ranar 21 ga Fabrairu a babban birnin tarayya, Abuja.
A cikin wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafinta na X, ta yi kira ga dukkan ’masu zaɓe da suka cancanta a Abuja da su yi amfani da damar don karɓar katunan su.
An bayyana cewa rabon katin zaɓen zai gudana a kowanne wurin rajistar zaɓe daga ranar 22 zuwa 26 ga Janairu.
INEC ta ƙara da cewa masu zaɓe da ba za su iya karɓar katin su a wurin rajista ba a lokaci, za su iya yin hakan a ofisoshin INEC da ke faɗin ƙananan hukumomin babban birnin tarayya.
Jam’iyyun siyasa 17 ne za su fafata a zaɓen wajen neman kujeru a mazaɓu 62 na Abuja.

Asalin hoton, Malami
Hukumar tsaro ta farin kaya a Najeriya, DSS ta kama tsohon attoni janar kuma ministan shari'a, Abubakar Malami.
Wata majiya mai tushe daga hukumar ta tabbatar da cewa DSS ɗin ta kama shi ne bisa zargin tallafa wa ta'addanci, bayan gano makamai da harsasai a gidansa da ke birnin Kebbi.
Kazalika, BBC ta zanta da wani makusanci tsohon ministan, Honorable Abubakar B Sabo, tsohon ɗan majalisar Birnin Kebbi, inda shi ma ya tabbatar da kamen.
An kama Malami wanda ake tuhuma a gaban wata babbar kotun tarayya a Abuja kan zargin halasta kuɗin haram, ranar Litinin jim kaɗan bayan sake shi daga gidan yarin Kuje da ke Abuja.
Jami'an gidan gyaran halin sun tabbatar da sakin Malami bayan cika sharuɗan beli.
A ranar 7 ga watan Janairu, Kotun Tarayya da ke Abuja ƙarkashin jagorancin alƙali Emeka Nwite ta amince da bayar da belin tsohon ministan shari’a Abubakar Malami da iyalinsa kan kuɗi naira miliyan 500 da kuma mutum biyu da za su tsaya musu.
A cewar alƙalin, mutanen da za su tsaya musu sai sun kasance suna da filaye a yankunan Asokoro da Maitama ko Gwarinpa, sannan kuma sai sun miƙa dukkan takardun tafiyarsu ga kotu.

Asalin hoton, Getty Images
Fadar Mai Alfarma Sarkin Musulmi a Najeriya, Sa'ad Abubakar III, ta ce yau Talata 20 ga watan Janairun, 2026 ita ce 1 ga watan Sha'aban na Hijira 1447.
Matakin ya biyo bayan ganin sabon wata da aka yi a yammacin jiya Litinin bayan watan Rajab ya cika kwana 29.
A kalandar Musulunci, kowane wata yana da kwana 29 amma idan ba a ga sabon wata ba za a ƙara kwana ɗaya zuwa 30.
Hakan na nufin saura wata ɗaya cif kafin fara watan Azumin Ramadana mai tsarki.
Al'ummar Musulmi kan wuni tun daga assalatu zuwa almuru ba tare da sun ci ko shan wani abu ba a Ramadana.
Da zarar an kammala Azumin Ramadana kuma sai bikin Ƙaramar Sallah ya biyo baya, wanda ake kira Eid al-Fitr.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X

Asalin hoton, AFP
Tsohuwar ministar harkokin man fetur ta Najeriya, Diezani Alison-Madueke, ta bayyana a gaban Kotun Southwark Crown da ke birnin Landan, kan shari’ar da ake yi mata na tuhumar cin hanci na fam 100,000 kamar yadda gidan talabijin na Channels ya ruwaito.
Alison-Madueke, wadda ta riƙe mukamin minista daga shekarar 2010 zuwa 2015, ita ce mace ta farko da ta rike mukamin ministar man fetur a Najeriya kuma ita ce mace ta farko da ta shugabanci ƙungiyar mai ta duniya, OPEC..
An gurfanar da Diezani kan laifuka guda shida da ta musanta, bayan da hukumar NCA ta Birtaniya ta tuhume ta a shekarar 2023 da karɓar cin hanci daga 2011 zuwa 2015.
Kamar yadda hukuncin ya nuna, Alison-Madueke ta ci moriyar ko karɓan tsabar kuɗi akalla fam 100,000 da motocin alfarma da tafiye-tafiye a jiragen haya na alfarma da ma amfani da kadarori da dama a London.
An tsara fara shari’ar a ranar Litinin, 26 ga Janairun 2026, wadda ake sa ran za ta ɗauki makonni 10 zuwa 12.

Asalin hoton, AFP via Getty
Japan ta ce ta samu adadi na masu yawon buɗe ido miliyan 42 da suka ziyarci ƙasar a shekara ta 2025.
Hakan na nufin shekara biyu kenan a jere ƙasar na samun irin alkaluman.
Lamarin ya ƙara bunƙasa tattalin arzikin ƙasar, inda masu buɗe ido suka kashe kuɗin da ya kai dala biliyan 60 a shekara da ta wuce.
Yawan masu zuwa ziyara daga China ya ragu da kashi 45 a watan da ya gabata.
Hakan ya zo ne bayan samun tsamin dangantaka tsakanin ƙasashen biyu, inda Beijing ta shawarci ƴan ƙasarta su kauce wa zuwa Japan.

Isra’ila na barazanar rushe filin kwallon ƙafa na yaran Falasdinawa a yammacin kogin jordan da ta mamaye, duk da yaƙin neman tallafi daga ƙasashen duniya domin kare filin.
Masu goyon bayan kada a rushe filin sun ce filin yana ba yara ƴan Falasdinawa damar samun horo a wasanni, abin da ba kasafai ake samu ba a wannan yanki mai fama da rikici.
Sai dai Isra’ila ta jaddada cewa an gina filin nei ba tare da samun izinin da ya dace ba.
An fara gina filin a gefen birnin Bethlehem a shekarar 2020, kuma a yau yana bai wa sama da yara 200 daga sansanin ’yan gudun hijira na Aida damar yin atisaye da horo.
A ranar 3 ga Nuwamba bara ne aka bayar da takardar sanarwana rushe filin wanda ke bayyana cewa ba bisa doka ba ne aka gina filin wasan lamarin da ya ja hankalin ƙasashen duniya saboda alaka da wasan ƙwallon ƙafa,

Asalin hoton, FACEBOOK/Abba Kabir Yusuf
Gwamnatin jihar Kano ta fitar da wata sanarwa domin yin ƙarin haske kan ganawar da gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf ya yi da shugaban Najeriya Bola Tinubu.
A yammacin Litinin ne gwamnan, wanda aka daɗe ana raɗe-raɗin komawarsa jam'iyyar APC mai mulki daga jam'iyyar NNPP ya gana da Bola Tinubu, inda ake sa ran cewa tattaunawar ta ƙunshi batun cimma yarjejeniya kan sauya sheƙar gwamnan.
Sai dai a sanarwar da gwamnatin ta fitar ta hannun mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature, ta ce gwamnan da shugaban ƙasa sun tattauna ne kan muhimman abubuwa da suka shafi tsaro da samar da ayyukan more rayuwa.
Sanarwar ta ce ganawar, wadda aka yi a asirce, "ta bai wa gwamnan damar yi wa shugaban ƙasa bayani kan manyan ƙalubale da jihar Kano ke fuskanta musamman taɓarɓarewar tsaro a wasu ƙananan hukumomi.
"Gwamna Yusuf ya kuma yi wa shugaban ƙarin bayani kan matar da aka kashe da ’ya’yanta shida kwanan nan, yana mai jaddada buƙatar gaggawar tallafin gwamnatin tarayya domin ƙarfafa ayyukan tsaro da kare rayukan fararen hula.
"Ya kuma bayyana rawar da Rundunar Tsaro ta Jihar Kano ke takawa wajen taimaka wa hukumomin tsaro, tare da neman ƙarin haɗin gwiwa da hukumomin tsaron tarayya.
"A ɓangaren raya ƙasa, gwamnan ya tattauna manufar ci gaban Kano, inda ya mayar da hankali kan manyan ayyukan gine-gine.
"A nasa ɓangaren, Shugaba Tinubu ya tabbatar wa gwamnan cewa "gwamnatin tarayya a shirye take ta yi aiki kafaɗa da kafaɗa da Kano domin shawo kan matsalolin tsaro da kuma tabbatar da ci gaba mai ɗorewa," kamar yadda sanarwar ta bayyana.

Asalin hoton, Getty Images
Wata kotu a Najeriya ta ɗage sauraron shari’ar wani mutum da ake zargi shi ne direban da ya tuƙa motar Anthony Joshua, ɗan damben duniya da ya yi hatsari a Najeriya, wanda ya yi sanadin mutuwar mutum biyu.
Mista Joshua dai ya tsallake rijiya da baya da ƙananan raunuka, a hatsarin da ya faru a kan babban titin Legas zuwa Ibadan a kudu maso yammacin Najeriya.
Kotun ta ce za a ci gaba da shari’ar a ranar 25 ga watan Fabrairu mai zuwa.
Direban, Adeniyi Kayode, ya bayyana a gaban kotun majistare da ke Sagamu a Jihar Ogun a ranar Talata tare da lauyansa.
An ɗage shari’ar bayan masu gabatar da ƙara sun nemi ƙarin lokaci domin tura kundin shari’ar zuwa ofishin Babban Lauyan Jihar domin neman shawarwarin shari’a.
Ana tuhumar direban da laifuka huɗu da suka haɗa da haddasa mutuwa ta hanyar tuƙi cikin ganganci da tuƙi ba tare da kula ba, da kuma ba tare da lasisi ba.
Kotu ta ba da belinsa kan naira miliyan biyar.

Asalin hoton, Getty Images

Asalin hoton, Getty Images
Ƙungiyar Likitoci ta kasa da kasa MSF ta yi kiran gaggawa domin faɗaɗa ayyukan samar da abinci mai gina jiki, da yaƙin samar da riga-kafi da ayyukan samar da tsaftataccen ruwa a Somaliya'
Ƙungiyar ta yi gargaɗin cewa in har ba a samu hadin gwuiwar sassa daban-daban na Duniya ba, ba za a iya dakatar da asarar rayuka masu yawa ba.
Yayin da yanzu ake tsaka da lokacin rani na Jilaal, MSF tana kira ga masu ba da tallafi da hukumomin Somaliya da su gaggauta sakin kudaden gaggawa domin bayar da agajin ceto rayyuka.
Somalia na fuskantar mummunar matsalar lafiya sakamakon fari tare da raguwar tallafin jin ƙai.
A watan Nuwambar shekarar da ta gabata, gwamnatin Somalia ta ayyana dokar ta-baci kan fari.
A cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Litinin, MSF ta ce cibiyoyinta a yankunan Baidoa da Mudug na fuskantar ƙaruwar yara masu fama da tsananin yunwa da kuma ɓarkewar cututtukan da za a iya kauce musu, ciki har da sankarau da cutar mashaƙo da gudawa.
MSF ta ce fari na lalata hanyoyin samun abinci da abin dogaro, tare da tilasta wa iyalai guduwa zuwa sansanonin ’yan gudun hijira inda ake fama da ƙarancin ruwa mai tsafta.

Asalin hoton, Getty Images
Majalisar wakilan Australia ta kaɗa ƙuri'ar amincewa da wani shirin ƙasa na sayen bindigogi daga hannun jama'a, da kuma fara sabon tsarin gudanar da bincike kafin bada izinin mallakar makami a ƙasar.
An zartar da ƙudirin dokar ne bayan wakilai 96 suka kaɗa ƙuri'ar amincewa da shi, yayin da 45 suka nemi a soke shi.
Yanzu dai ƙudirin dokar zai ƙarasa majalisar dattawa, inda a can ma ake sa ran ya samu tsallakewa.
Matakin na zuwa ne wata guda bayan mummunan harin gaɓar tekun Bondi, inda wasu mahara suka buɗe wuta kan Yahudawa masu biki a wajen, suka kuma kashe mutane 15.

Asalin hoton, Reuters
Jagoran ƴan adawan Uganda Bobi Wine, ya yi kira ga jama'ar ƙasar su tashi tsaye domin yin turjiya ga abin da ya kira mulkin kama-karya na shugaba Yoweri Museveni.
A wata hira da BBC, Mista Wine ya ce zai ci gaba da ƙalubalantar Museveni duk da hatsarin da hakan ke da shi ga rayuwarsa.
Ya ce: Mun ga yadda jama'ar Uganda ke ci gaba da yaƙi da abubuwan da ake masu, domin a zahiri ta ke mutane za su yi turjiya ga cin zarafi.
Ya dai jaddada iƙirarin cewa jami'an tsaro a Uganda na son kama shi domin cutar da shi, amma gwamnatin ƙasar ta musanta wannan zargi.

Asalin hoton, Getty Images
Shugaban Amurka Donald Trump ya sha alwashin aiwatar da barazanar da ya yi na lafta ƙarin haraji kan ƙasashen Turai da ke adawa da buƙatarsa ta karɓe ikon yankin Greenland.
Ana sa ran shugabannin Turai za su tafka muhawara kan makomar yankin Greenland a wajen taron tattalin arzikin duniya da ke gudana a birnin Davos na Switzerland, duk da barazanar shugaban Amurka a kai.
Shugaban Faransa, Emmanuel Macron, da shugabar hukumar Tarayyar Turai, Ursula von der Leyen, za su fara gabatar da jawabai a yau Talata, kwana ɗaya kafin isowar shugaba Trump Switzerland, inda taron ke gudana.
Ƙasashen Turai sun bayyana aniyarsu ta haɗa kai domin fuskantar shugaban Amurka, inda suka sha alwashin mayar da martani kan duk wani yunƙurinsa na lafta musu ƙarin haraji.
A jiya Litinin, shugaban Amurka ya ce a shirye yake ya sanya ƙarin haraji kan ƙasashen Turai da ke adawa da yunƙurinsa na mayar da Greenland a matsayin wani yanki na Amurka.

Asalin hoton, Getty Images
Batun kisan da aka yi wa wata mata tare da ƴaƴanta shida a jihar Kano na ci gaba da razana al'ummar ciki da wajen jihar.
Wasu matasa ne dai ɗauke da makamai suka kutsa gidan matar da ke unguwar Dorayi Charanci da tsakar rana inda suka halaka ta tare da duka ƴaƴanta nata.
Lamarin na zuwa ne ƙasa da watanni bayan da wasu matasan suka shiga wani gida a unguwar Tudun Yola da ke birnin na Kano suka kuma kashe matan gidan biyu tare da ƙona gawarwakinsu.
Waɗannan kashe-kashe sun tayar da hankula tare da ƙara jefa tsoro da fargaba a zukatan al'ummar jihar - waɗanda ke ganin rayuwarsu na cikin barazana.
Kan haka ne masana tsaro ke ci gaba da bayar da shawarwari na matakan da ya suka mutane su ɗauka domin kauce wa wannan matsala.