Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 01/12/2024

Wannan shafi ne da ke kawo muku muhimman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 01/12/2024

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza da Badamasi Abdulkadir Mukhtar

  1. Shugaba Assad ya gana da ministan Iran kan rikicin Syria

    Assad

    Asalin hoton, EPA

    Shugaban Syria, Bashar al-Assad ya gana da ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi a Damascus, tare da yin maraba da tallafi domin yaƙi da ƴantawayen da suka ƙawace iko a wasu sassan ƙasarsa.

    Mr Assad ya ce taimako daga abokan huɗɗarsa abu ne mai mihimmancin gaske wajen tunkarar abin da ya kira taron ƴan ta'adda.

    An daɗe ba a ganin shugaban na Syria, duk da cewa ƴantawaye sun ci gaba da kutsawa arewacin Ƙasar a makon nan.

    Rasha ta bai wa Assad tallafin kayan yaƙi ta sama, inda ya riƙa kai wa ƴantawayen hari a Idlib da kuma Hama.

    Ma'aikatar tsaron Syria ta ce an kashe gomman mayaƙan ƴantawayen.

    Masu sanya ido sun ce an samu rahoton kisan fararen hula a wurare, ciki harda birnin Aleppo da ƴantawayen suka ƙwace.

  2. Trump ya naɗa mai taimaka masa kan harkokin Gabas ta Tsakiya

    Trump

    Donald Trump ya sanar da naɗin Massad Boulos a matsayin babban mai bashi shawara a kan ƙasashen larabawa da yankin gabas ta tsakiya.

    Hamshaƙin ɗan kasuwar Amurkan mai tsatson Lebanon yana cikinwaɗanda suka taimakawa Trump wajen yaƙin neman zaɓe a wajen Larabawan Amurka da kuma al'ummar musulmi, musamman a jihar Michigan.

    Mr Boulos shi ne ɗan cikin gida na farko da aka naɗa muƙami a gwamnatin Trump mai jiran gado.

    Shi ne mahaifin mijin ɗiyar zaɓaɓɓen shugaban Amurkan, Tiffany.

    A ranar Asabar Mr Trump ya sanar da naɗin Charles Kushner, mahaifin sirikinsa, Jared Kushner, domin naɗa shi jakadan Amurka a Faransa.

  3. An kasa cimma matsaya kan rage amfani da robobi a duniya

    Global plastic talks

    Asalin hoton, Getty Images

    An kasa cimma matsaya a kan tattaunawar ƙasashen duniya game da yadda za a rage amfani da robobi masu gurɓata muhallai.

    Shugaban taron da aka yi a Koriya ta Kudu, Luis Vayas Valdivieso, ya ce nan gaba za su sanar da lokacin da za a koma tattaunawar domin cimma matsaya.

    Tun da farko dai sai da aka samu jinkiri a zauren taron a birnin Busan, bayan gardama ta ɓarka a kan ko za a sanya dokokin da za su rage yawan robobin da ake samarwa a duniya.

    Wasu ƙasashe masu arzikin mai da ake yin robobin da shi, sun nemi a ɗauki matakin ƙulla yarjejeniyar da ba za ta kawo koma baya ga ayyukan su ba.

    Ƙasashe aƙalla 200 ne ke cikin wannan tattaunawa da aka shafe shekaru biyu ana yi.

  4. Firaiministan Georgia ya musanta zargin jingine ƙoƙarin shiga EU

    Georgia

    Asalin hoton, GIORGI ARJEVANIDZE/AFP

    Firaiministan Georgia ya musanta cewa gwamnatinsa ta jingine yunƙurin ƙasar na shiga ƙungiyar tarayyar Turai, a wani mataki da ya banbanta da kalamansa na ranar Alhamis da suka janyo zanga-zanga.

    Irakli Kobakhidze ya zargi ƴan adawar Georgia da yaɗa ƙarya, yana cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da ƙoƙarin ganin ƙasar ta shiga tarayyar Turai.

    Kwana uku kena da Firaiministan ya sanar da cewa za a dakatar da neman shiga ƙungiyar tarayyar Turai har zuwa nan da shekara huɗu.

    Kalaman nasa sun janyo bore daga masu neman ƙasar ta ci gaba da zama a Turai.

    Masu zanga-zangar suna kuma ƙalubalantar sakamakon zaɓen majalisar dokokin ƙasar na watan Oktoba, wanda ya bai wa jam'iyyar Georgian Dream damar ci gaba da mulki.

  5. 'Yansanda sun ƙaddamar da bincike kan garkuwa da wani ɗan siyasa a Tanzaniya

    Shugaban matasa na jam'iyyar hamayya

    Ƴansanda a Tanzania sun ƙaddamar da bincike a kan rahoton sace wani jagoran matasan ƴan adawa, Abdul Nondo wanda ake zargin an sace a wata tashar mota a birnin Dar es Salaam.

    Sanarwar da ƴansandan ska fitar a yau Lahadi ta ce da misalin ƙarfe 5 na asuba wasu mutane biyu suka kama wani mutum, suka kuma tilasta masa shiga wata farar mota ƙirar Land Cruiser mai lamba T 249 CMV, tare da yin awon gaba da shi.

    Duk da cewa har yanzu babu tabbacin ko wanene mutanen suka kama, ƴansanda sun ce mutumin ya bar wata jaka a wajen, kuma a cikin ta akwai kayyaki mallakin Mr Nondo, jagoran matasan jam'iyyar ACT Wazalendo.

    Tun da farko da safiyar Lahadi, jam'iyyar ACT Wazalendo ta sanar da cewa an yi garkuwa da shugaban matasan nata jim kaɗan bayan ya dawo daga yammacin ƙasar, inda ya shiga yaƙin neman zaɓen ƴan takarar jam'iyyar a zaɓukan ƙananan hukumomi da aka kammala ranar Alhamis.

  6. Gwamnatin Syria ta ce jiragenta da na Rasha sun yi luguden wuta kan 'yantawaye

    Ma'aikatar tsaron Syria ta ce jiragen yaƙin ƙasar da haɗin gwiwar ƙasar Rasha sun kai hare-hare ta sama kan dakarun 'yantawaye a arewacin lardunan Idlib da Hama.

    Shugaba Bashar al-Assad ya sha alwashin amfani da ƙarfi wajen murƙushe abin da ya kira ''ayyukan ta'addanci''.

    Rundunar sojin ƙasar ta ce ta ƙwace garuruwa masu yawa da 'yantawayen suka ƙwace tun da farko.

    Tuni aka ƙara ƙarfafa cibiyoyin gwamnati a lardin Hama.

    Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi - wanda ya ziyarci Damascus a yau - ya ce gwamnatin Tehran na goyon bayan Mista Assad.

    Sauran ƙasashe ƙawayen gwamnatin Assad ciki har da Masar da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa na ƙoƙarin ƙulla ƙawance da ma'aikatar tsaronta.

  7. MDD ta dakatar da ayyuka a kan iyakar Isra'ila da Gaza saboda rashin tsaro

    Motar MDD

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar Majalisar Dinkin Duniya da ke tallafa wa Falasɗinawa, UNRWA ta ce ta dakatar da kai kayan agaji zuwa yankunan da ke iyakar Isra'ila da Gaza saboda da ƙaruwar matsalar tsaro.

    Shugaban hukumar ya ce a baya-bayan nan wasu masu ɗauke da makamai sun daka wa wasu tawagar ayari motoci biyu a mashigar Kerem Shalom, wadda ita ce mashiga mafi girma da ake kai kayan agaji ga Falasɗinawa fiye da miliyan biyu a Gaza.

    Philippe Lazzarini ya zargi gwamnatin Isra'ila da haifar da mummunan yanayin da ake ciki, sannan ya yi kiran tsagaita wuta domin bayar da dama a riƙa kai kayan agaji ba tare da yankewa ba.

    A baya Isra'ila ta ce ta bayar da damar shigar da kayan agajin, inda ta dage cewa Gaza na da wadataccen abinci.

  8. 'Rayuwata da HIV tamkar rayuwarku ce ta masu lafiya'

    A yau 1 ga watan Disamba, rana ce da Majalisar Dinkin Duniya ta ware kan fadakarwa game da cuta mai karya garkuwar jiki, wato HIV/AIDS.

    A bana Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO ta ɗaura damarar haɗa gwiwa da abokan hulɗa da sauran al'ummomi daban-daban na ƙasashen duniya, domin fadakarwa game da hanyoyin tabbatar da kare haƙkin masu fama da wannan cuta.

    Dangane da wannan rana muka tattauna da wata matashiya mai suna Fatima Abdullahi Tunau - mai ɗauke da cutar, kuma take fafutikar wayar da kan jama'a game da cutar a Najeriya.

    Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon
  9. Tinubu ya kama hanyar Afirka ta Kudu daga Faransa

    Shugaba Tinubu

    Asalin hoton, Bayo Onanuga/X

    Shugaban Najeriya, Bola Tinubu zai wuce ƙasar Afirka ta Kudu daga Faransa, inda yake ziyarar aiki.

    Cikin wata sanarwa da kakakin shugaban ƙasar, Bayo Onanuga, ya fitar, ya ce Shugaba Tinubu zai zarce A firka ta Kudu ne a gobe Litinin, domin ya jagoranci taron kwamitin haɗin kai tsakanin Najeriya da Afirka ta Kudu karo na 11, tare da shugaba Cyril Ramaphosa.

    "Taron wanda aka shirya gudanarwa a ranar Talata, 3 ga Disamba, zai kasance gabanin taron ministocin ƙasashen a ranar 2 ga Disamba, 2024, a zauren majalisar dokokin Afirka ta Kudu da ke birnin a Cape Town,'' in ji Onanuga.

    Sanarwar ta ci gaba da cewa shugabannin biyu za tattauana batutuwa da dama da suka shafi dangantakar ƙasashen biyu da batutuwan da suka shafi Afirka da ƙasashen duniya.

    “Shugabannin za su ɗora kan alƙawuran da suka yi a ranar 20 ga watan Yuni, 2024, a ganawar da suka yi a birnin Johannesburg jim kaɗan bayan rantsar da shugaba Ramaphosa a wa'adin mulki na biyu'', in ji sanarwar.

    A ranar Laraba ne Shugaba Tinubu ya tafi ziyarar aiki ta kwana uku zuwa ƙasar Faransa.

  10. Kada a cutar da wasu jihohi a sabuwar dokar haraji - Atiku

    Atiku Abubakar

    Asalin hoton, Atiku Abubakar/Facebook

    Jagoran adawar Najeriya, Atiku Abubakar ya yi kira ga majalisar dokokin ƙasar ta yi aiki bisa gaskiya da riƙon amana wajen shirya taron jin ra'ayin jama'a kan sabon ƙudirin harajin ƙasar da ya tsallake karatu na biyu a zauren majalisar.

    A makon da ya gabata ne majalisar dattawan ƙasar ta yi wa ƙudirin karatu na biyu, inda kuma yanzu ta miƙa shi ga kwamitin kuɗi na majalisar domin shirya taron jin ra'ayin jama'a kan ƙudurin.

    Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X ranar Lahadi, tsohon mataimakin shugaban Najeriya, ya ce kan 'yan ƙasa ya haɗu wajen yin kira a samar da tsare-tsaren kuɗi bisa adalci da daidaito ga kowane yanki.

    ''Mun faɗa da babbar murya cewa bai kamata tsare-tsaren kuɗi da gwamnatin ƙasar ke son ingantawa ya fifita wasu jihohin ƙalilan ta hanyar ruguza sauran ba'', in ji Atiku Abubakar.

    ''A matsayina na mai ruwa da tsaki, na yi imanin cewa gaskiya da adalci da riƙon amana da kyakkyawan shugabanci, na da matuƙar muhimmanci wajen tsara manufofi''.

  11. Rasha ta ƙaddamar da hare-hare a Syria

    Rasha ta ƙaddamar da jerin hare-hare ta sama a Syria a da safiyar yau Lahadi, yayin da 'yantawaye suka danna zuwa kudancin ƙasar, kamar yadda ƙungiyar kare haƙƙin bil'adama ta 'Syrian Observatory for Human Rights' ta bayyana

    Hare-haren sun faɗa a yankunan karkara a yankunan Idlib da Hama, inda 'yantawayen suka zafafa hare-hare a baya-bayan nan.

    Gwamnatin Syria ta rasa iko da birnin Aleppo a karon farko tun bayan fara yaƙin basasar ƙasar, kamar yadda masu sanya idanu suka shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP.

  12. An gano gawarwaki 54 a kifewar kwale-kwalen jihar Kogi - NEMA

    Alhaji Ahmed Usman Ododo

    Asalin hoton, Alhaji Ahmed Usman Ododo/Facebook

    Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Najeriya ta ce ta gano aƙalla gawarwaki 54 a wurin da hatsarin kwale-kwalen jihar Kogi ya auku ranar Juma'ar da ta gabata.

    Ana dai kyautata zaton cewa har yanzu ba a ga fiye da mutum 100 ba, yayin da aka ceto wasu 24 da ransu.

    Ƙwararrun ninƙaya da masu iyo na ci gaba da neman sauran mutanen, sai dai fatan samun ragowar mutanen da rai na ci gaba da raguwa a zukatan al'umma.

    Kwale-kwalen ɗauke da fasinjoji fiye da 200 ya kife a cikin ruwan Kogin Neja tsakanin jihohin Kogi da Neja da ke tsakiyar Najeriya, yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa kasuwar Katcha.

    Shugaban Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) mai kula da ofishin Kogi Mista Justin Uche ya shaida wa BBC cewa rashin ingantaccen tsari ya sa har yanzu ba a kai ga gano cikakkun bayanai game da fasinjojin ba.

    "Matsalar ita ce, babu tsarin adana bayanin fasinjoji, don haka bayar a cikakkun bayanan fasinjojin ke da matuƙar wahala'', in ji Mista Uche.

    Gwamnan jihar Kogi, Usman Ododo ya bayar da umarni ga Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar (SEMA) ta samar da kayayyakin agaji ga iyalan mutanen da abin ya shafa,” in ji wata sanarwa daga ofishin gwamnan.

    Haka kuma gwamnan ya buƙaci asibitocin da aka kwantar da mutanen da aka ceto da rai, su ba su kulawar da ta dace.

    Gwamnan na Kogi ya kuma koka kan yadda ake yawan samun haɗurran a harkar sufurin ruwa a Najeriya, sannan ya buƙaci a tsaurara matakan da suka dace don ganin an kauce wa samun irin waɗannan haɗurran a nan gaba.

  13. Hikayata 2024: Labarin 'Amon 'Yanci' da ya zo na ɗaya

    A yau ne muka fara kawo muku labaran gasar rubutun mata zalla ta Hikayata ta BBC Hausa ta 2024 a madadin filinmu na Taba Kidi Taba Karatu.

    Za dai mu kwashe makonni 15 muna kawo muku labaran da suka hada da ukun da suka zama gwaraza da kuma 12 da alƙalan gasar suka ce su ma sun cancanci yabo.

    A yanzu ga labarin Amon Ƴanci wanda ya zo na ɗaya a gasar ta bana wanda kuma Hajara Ahmad Hussain da ke garin Hadejar jihar Jigawa ta rubuta ta kuma karanta.

    Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin sauraron labarin
  14. Dakarun Syria sun janye daga birnin Aleppo bayan dannawar 'yantawaye

    Sojojin Syria

    Asalin hoton, Getty Images

    Sojojin gwamnatin Syria sun janye daga birnin Aleppo bayan dannawar 'yantawaye masu adawa da gwamnatin Bashar al-Assad a birnin.

    Sojojin sun yarda cewa ‘yantawaye sun shiga “muhimman'' sassan birnin - wanda shi ne na biyu mafi girma a ƙasar, amma sun sha alwashin kai musu harin turjiya.

    Farmakin ya kasance mafi muni a yaƙin basasar ƙasar a shekarun baya-bayan nan.

    Fiye da mutum 300 ciki har da fararen hula aƙalla 20 aka kashe tun a ranar Larabar da ta gabata, a cewar ƙungiyar kare hakkin dan'adam ta 'Syrian Observatory for Human Rights' (SOHR).

    Da yake jawabi a jiya Asabar, shugaba Assad ya sha alwashin kare martaba da mutuncin Syria da duka yankunanta daga jare-haren 'yantawaye da duka masu goya musu baya.

  15. Trump ya zaɓi sabon shugaban hukumar tsaro ta FBI

    Sabon shugaban FBI da Trump ke son naɗawa

    Asalin hoton, Getty Images

    Zaɓaɓɓen shugaban Amurka, Donald Trump ya zaɓi fitaccen mai biyayya a gare shi, Kash Patel, a matsayin shugaban hukumar tsaro ta FBI.

    Mista Patel, wanda tsohon mai gabatar da kara ne, ya rubuta wani littafi mai suna ‘Government Gagsters', inda a ciki a yi kaca-kaca da hukumar ta FBI, da ya kira da 'maƙiyar jama'a', da ya ce ya kama a 'shafe ta'.

    Ya kuma taɓa kiran a rufe hedkwatar ofishin FBI da ke Washington a wani yunƙuri na daƙile tasirin hukumar - wanda shi da Mista Trump ke kallo a matsayin "karen farautar siyasa".

    Naɗin na Mista Patel ka iya fuskantar turjiya a majalisar dattawan ƙasar

    Tun da farko Mista Trump ya bayyana ƙarara cewa yana buƙatar daraktan hukumar FBI na yanzu, Christopher Wray, ya sauka daga muƙaminsa.

    A wa'adin mulkinsa na farko ne, Donald Trump ya naɗa mista Wray a matayin shugaban hukumar.

  16. 'Yantawayen Syria sun kashe gomman sojojin ƙasar

    Sojojin Syria

    Asalin hoton, Getty Images

    Sojojin Syria sun ce mayaƙan 'yan tawaye da masu ikirarin jihadi sun kashe gwamman sojinsu a lokacin fatawar da ta kai 'yan tawayen karɓe iko da Aleppo, birnin na biyu mafi girma a ƙasar.

    Tun daga lokacin ne kuma masu iƙirarin jihadin ke dannawa zuwa wajen Hama - a kan hanyarsu ta ƙwace Damascus, babban birnin ƙasar - to sai dai sojojin sun suna shirya wani hari domin hana su shiga birnin.

    Ministan harkokin wajen Iran -- babbar ƙawar Syria - na kan hanyar kai ziyara ƙasar domin tattaunawa kan rikicin.

    Ana kuma sa ran Abbas Aragchi zai ziyarci Turkiyya, wadda ke mara wa 'yan tawayen baya.

    A martaninta na farko tun bayan ɓarkewar rikicin, Amurka ta ce babu abin da za ta iya yi a wannan sabon rikici.

    Kakakin Fadar White House ya ɗora alhakin faruwar lamarin kan gwamnatin Assad da ta riƙa dogarar da ƙasashen Rasha da Iran.

  17. Assalamu alaikum

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye yau ma Abdullahi Bello Diginza ke fatan kasancewa da ku.

    Barkanmu da hutun ƙarshen mako, tare da fatan kawo muku irin abubuwan da ke faruwa a sassan duniya.

    Ku biyo mu....