Pedri ya ji rauni a wasan Slavia Praque a Champions League, Barcelona

Asalin hoton, Getty Images
Barcelona ta fitar da sabon bayani kan ɗan wasa, Pedri bayan raunin da ya ji a Champions League a wasan da ƙungiyarsa ta je ta ci Slavia Prague 4-2 ranar Laraba.
Saboda haka Barcelona ta sanar cewar Pedri zai yi jinyar mako huɗu kafin ya koma taka mata leda.
Hakan babban koma baya ga ne ga koci Hansi Flick a kokarin da yake na gannin Barcelona ta ci gaba da samun nasarori a karawar kakar bana.
Kawo yanzu Pedri ba zai buga wasan La Liga da Real Oviedo da Elche da Real Mallorca da Girona da kuma Levante.
Haka kuma ba zai buga wa Barcelona Champions League da za ta kara da Copenhagen ba da kuma zagayen kwata fainal a Copa del Rey da Albacete ba.



















