Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Lahadi 01/03/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Lahadi 01/03/2026

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza

  1. OPEC za ta ƙara yawan man da take haƙowa saboda yaƙin Iran

    OPEC

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƙungiyar ƙasashe masu arzikin man fetur ta OPEC ta sanar da aniyar ƙara yawan man da take haƙowa sakamakon yaƙin Isra'ila da Iran da kuma Amurka.

    Ƙungiyar - wadda ta ƙunshi manyan ƙasashe masu arzikin man fetur, kamar Saudiyya da ƙasashen yankin Gulf da ke cikin fargabar harin ramuwar gayyar Iran - ta amince ta ƙara yawan man da take haƙowa da ganga 260,0000 a kowace rana.

    Ƙungiyar na son maye gurbin man da aka rasa a kasuwar mai ta duniya, daga ƙasashen Amurka da Kanada da kuma Brazil.

    Ana sa ran yaƙin ya kawo tsaikon tono mai a Iran, lamarin da ka iya tayar da farashin man.

  2. Kisan Ayatollah kaɗai ba zai wadatar ba - Reza Pahlavi

    Getty Images

    Asalin hoton, Getty Images

    Ɗan gidan tsohon Shah na ƙarshe a Iran, Reza Pahlavi ya ce kisan jagoran addinin Iran kaɗai ba zai wadatar ba.

    Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafnsa na X, Reza Pahlavi ya yi kira ga Iraniyawa su hamɓarar da gwamnatin Jamhuriyar Musulunci a ƙasar.

    Ya ƙara da cewa dole ne Iraniyawa su ''shirya wa zanga-zanga a kan manyan titunan biranen ƙasar,'' sannan su riƙa magana daga gidajensu cikin dare.

    A lokacin zanga-zangar kin gwamnati da aka gudanar aƙasar a baya-bayan nan, an riƙa ambata sunan Mista Pahlavi a wasu yankunan.

  3. An kashe sojojin Amurka uku a yaƙin Iran da Amurka

    sojojin amurka

    Asalin hoton, Getty Images

    Rundunar sojin Amurka mai kula da yaƙe-yaƙen ƙasar, Centcom, ta ce an kashe dakarun ƙasar uku a yaƙin da Amurka ke yi da Iran.

    Sojojin uku ne na farko da aka kashe wa Amurka tun bayan fara kai hare-haren a ranar Asabar.

    Rundunar sojin ta ce an kuma ji wa wasu biyar ''munanan raunuka''.

    Centcom ta kuma ce ba za ta wallafa sunayen sojojin da aka kashe ba sai bayan kwana guda da sanar wa iyalansu.

    A lokacin da yake bayyana far wa Iran da yaƙi, Shugaba Trump ya yi gargaɗin cewa Amurka za ta yi asasar sojoji.

  4. Shugaban Hezbollah ya yi alhinin mutuwar 'shahidi' Khamenei

    Shugaban Hezbollah

    Asalin hoton, Reuters

    Shugaban ƙungiyar Hezbollah, Naim Qasem ya yi alhinin mutuwar jagoran addinin Iran, Ali Khamenei, wanda ya bayyana da shahidi da ya bar miliyoyin mabiya a faɗin duniya.

    Qasem ya bayyana kisan Khamenei a “a harin Amurka da Isra'ila'' a matsayin babban laifi.

    Ya kuma alƙawarta ''kammala aikinsu na fuskantar faɗan, tare da neman neman taimako da nasasar ubangiji''.

    Ƙungiyar Hezbollah - ta ƴan shi'a a lebanon, ɗaya daga cikin manyan ƙungiyoyin da ake tunanin Iran na ɗaukar nauyinsu a yankin - za ta yi wani ggarumin taron alhini da nuna goyon bayan Khamenei da Iran.

  5. 'Mutum shida sun mutu a Isra'ila bayan harin Iran'

    Masu aikin ceto

    Asalin hoton, AFP/Getty Images

    Mutum shida sun mutu a birnin Beit Shemesh da ke tsakiyar Isra'ila bayan harin makamai masu linzamin Iran, a cewar hukumar bayar da agajin gaggawa ta ƙasar.

    Hukumar ta ce likitoci na yi wa mutum 23 magani da suka samu raunka a harin.

    Hukumar bayar da agajin ta ce cikin waɗanda suka jikkatan da ke asibitu, biyu daga cikinsu na cikin mawuyacin hali.

  6. Babu abin da mutuwar Khamenei za ta sauya - Araqchi

    Aragchi

    Asalin hoton, EPA

    Gwamnatin Iran ta ce babu abin da zai sauya dangane da aƙidar ƙasar bayan mutuwar jagoran addinin ƙasar.

    Yayin wani saƙon ta'azziya da ministan harkokin wajen ƙasar, Abbas Aragchi ya wallafa a shafinsa, ya ce ''za mu ci gaba da karewa tare da martaba aƙidarka.

    ''Wannan alhaki ne da kan kowane ɗan Iran'', in ji shi.

    Ya ƙara da cewa ''tutar da Ali Khamenei ya ɗaga ba za ta taɓa faɗuwa ƙasa ba, za mu ci gaba da ɗagata har zuwa matakin ƙoli''.

  7. Kashe Khamenei ya saɓa wa dokokin duniya - Putin

    Putin

    Asalin hoton, EPA

    Shugaban ƙasar Rasha, Vladimir Putin ya aike da saƙon ta'aziyyarsa kan mutuwar jagoran addinin Iran, Ayatollah Ali Khamenei.

    Kamfanin dillancin labaran Rasha na TASS ya ambato Shugaba Putin na bayyana kisan Khamenei da ''Kisan gillar da ya saɓa wa dokokin duniya da mutunta ɗan'adam''.

    Rasha ta kasance babbar ƙawa ga Iran.

    A shekarar da ta gabata ne ƙasashen biyu suka amince da yarjejeniyar hadin gwiwar soji.

  8. Ayatollah jarumin namiji ne da baya tsoro - Dr Gumi

    Dr. Ahmad Abubakar Mahmud Gumi

    Asalin hoton, Dr. Ahmad Abubakar Mahmud Gumi/FB

    Fitaccen malamin addinin musuluncin nan a Najeriya, Dr Ahmad Mahmud Gumi ya nuna alhininsa kan mutuwar jagoran addinin Iran, Ayatollah Ali Khamenei.

    Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Dr Gumi ya ce jagoran addinin ya yi sa'a ya yi shahada.

    ''Ya mutu sakamakon harin waɗanda suka kashe ƙananan yara da matan da ba su ji ba su gani ba a Gaza da sauran wurare'', kamar yadda ya wallafa.

    Ya bayyana shi a matsayin jarumin namiji da jininsa zai samar da sauyi ga alumma.

    ''A tsaye yake don tabbatar da adalci, kuma ba ya ɓuya a ƙarƙashin ƙasa ba'', in ji shi.

    Dr Gumi ya ce ga waɗanda suka kashe shi, ''ga duniyar nan ya bar musu, sai su zuba ruwa a ƙasa su sha''.

  9. Ƙusoshin gwamnatin Iran da suka mutu a hare-haren Amurka da Isra'ila

    Iran

    Asalin hoton, Reuters

    Hare-haren da Amurka da Isra'ila suka ƙaddamar kan Iran a ranar Asabar ya yi snadin mutuwar manyan ƙusoshin gwamnatin ƙasar da suka haɗa da:

    • Ayatollah Ali Khamenei, Jagoran addinin ƙasar, wanda aka kashe ranar Asabar da safe a ofishinsa.
    • Gidan talbijin na ƙasar ya bayar da rahoton cewa an kashe shugaban rundunar sojin ƙasar, Abdolrahim Mousavi a hare-haren.
    • Haka ma Tehran ta tabbatar da mutuwar babban kwamandan dakarun juyin juha halin ƙasar, Janar Mohammad Pakpour
    • Sannan kafofin yaɗa labaran ƙasar sun bayar da rahoton mutuwar ƴar jagoran addinin ƙasar, da kuma surukinsa da jikansa.
    • Wata majiyar sirri da soji ta shaida wa kafar yaɗa labaran CBS News cewa jami'an gwamnatin Iran 40 ne suka mutu a hare-haren.
  10. Iran ta naɗa Alireza Arafi jagoran addinin ƙasar na riƙo

    sabon jagoran addinin Iran

    Asalin hoton, intanet

    Hukumomin Iran sun sanar da naɗin, Ayatollah Alireza Arafi matsayin jagoran addinin ƙasar na riƙo, kafin a zaɓi sabo.

    Majalisar manyan malaman ƙasar mai mambobi 88 ce za ta za bi sabon jagoran addinin.

    Al'ummar kasar ne dai ke zabar mambobin majalisar bayan kowace shekara takwas.

    A ƙarƙashoin dokokin Iran, waɗannan manyan malaman ne ke da alhakin zaɓen sabon jagoran addini da zarar wanda yake kan muƙamin ya kau, to sai dai ana ganin hakan zai yi wahala kasancewar babu kwanciyar hankali a ƙasar da ke cikin yanayi na yaƙi.

  11. An kai hari kan ofishin jakadancin Amurka a Pakistan

    Hoto

    Asalin hoton, Getty Images

    Aƙalla mutum takwas ne suka mutu a zanga-zangar goyon bayan Iran da aka gudanar a kusa da ofishin jakadancin Amurka da birnin Karachi na kasar Pakistan.

    kakakin hukumar bayar da agajin gaggawa na yankin, Muhammad Amin ya shaida wa kamfanin dilalncin labarai na AFP cewa mutum 20 ne suka jikkata yayin zanga-zangar.

    Wasu rahotonni sun bayyana cewa jami'an tsaron Amurka da ke harabar ofishin jakadncin ne suka buɗe wuta kan masu zanga-zangar, sannan daga baya ƴansandan Pakistan suka harba yahaƙi mai sa hawaye.

    A cewar AFP wasu fusatattun matasa ne suka haura katangar domin shiga harabar ofishin jakadancin ya yi da wasu suka karya tagogin ginin.

    Bidiyoyin da aka yaɗa sun nuna yadda matasan suka riƙa karya tagogin.

    Dubban mutane suka fantsama kan titunan Lahore da Skerdi, domin guidanar da zanga-zangar, yayin da ake sa ran yin zanga-zangar a kusa da ofishin jakadancin Amurka da Islamabad, babban birnin ƙasar.

  12. Hotunan ɓarnar da hare-haren Iran suka yi kan sansanonin sojin Amurka

    Hotuna na ci gaba da bayyana na yadda baƙin hayaƙi ke tashi bayan harin ramuwar gayyar Iran kan sansanonin sojin Amurka da ke Gabas ta Tsakiya.

    An ɗauki wasu daga cikin hotunan cikin dare, wasu kuma da safe a ƙasashen Bahrain da Haɗaɗdiyar Daular Larabawa.

    hoto

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, An ga baƙin yahaƙi a birnin Doha na Qatar bayan harin Iran
    Hoto

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Harin jirgin Iran maras matuƙi ya shafi wani gini tare da ƙona shi a Manama, babban birnin Bahrain.
  13. Harin Iran ya lalata wani gini a birnin Tel Aviv na Isra'ila

    Wani gida da Iran ta ruguza a Tel Aviv

    Asalin hoton, EPA/Shutterstock

    Harin makami mai linzamin Iran ya lalata wani gida a tsakiyar Tel Aviv, babban birnin Isra'ila.

    Rahotonni daga ƙasar sun ce harin ya yi sanadin mutuwa mace guda, wadda ita ce mutuwa da farko da aka bayar da rahotonta a Isra'ila tun bayan fara wannan yaƙi.

    Isra'ila ta kakkaɓo kusan duka makaman linzami da Iran ta harba cikinta.

    Amma duk da haka wasu sun samu faɗawa ciki, musamman bayan tarwatsewa a sama.

  14. Iraƙi ta ayyana makokin kwana uku bayan kisan Khamenei

    Gwamnatin ƙasar Iraƙi ta ayyana makokin kwana uku a fadin ƙasar domin nuna alhini kan kisan jagoran addainin Iran Ayatollah Ali Khamenei.

    Cikin wata sanarwar da gwamnatin ƙasar ta fitar, ta aike da saƙon jaje ga al'ummar Iran, kan kisan jagoran addinin ƙasar, wadda ta bayyana da ''aikin takalar faɗa''.

  15. Dubban Iraniyawa na jimamin mutuwar jagoran addinin ƙasar

    mutane

    Asalin hoton, Getty Images

    Dubban Iraniya sun taru a birnin Tehran domin yin alhinin mutuwar jagoran addinin ƙasar, Ayatollah Ali Khamenei da Amurka da Isra'ila suka kashe a hare-harensu.

    wasu mata

    Asalin hoton, Getty Images

    Tuni dai hukumomin ƙasar suka sanar da makokin kwanaki 40 a faɗin ƙasar

    wasu mata

    Asalin hoton, Getty Images

    Ayatollah Ali Khamenei na da farin jini da ƙarfin faɗa a ji a ƙasar Iran

    Hoto

    Asalin hoton, Getty Images

    Ya shafe fiye da shekara 35 yana jan ragamar ƙasar, mai ƙarfin faɗa a ji a yankin Gabas ta Tsakiya.

  16. 'Jiragen Iran sun yi ruwan boma-bomai kan sansanonin sojin Amurka'

    gini ya kama da wuta

    Asalin hoton, Reuters

    Kamfanin dillancin labaran Iran, IRNA ya ce jiragen yaƙin ƙasar sun yi ruwan boma-bomai kan sansanonin sojin Amurka da ke yankin Gulf da yankin Kurdistan na Iraƙi.

    Dakarun sojin Iran sun ce jiragen yaƙin ƙasar sun samu nasarar kai munanan hare-hare kan sansanonin.

    Sojojin sun ƙara da cewa ''duka sansanonin maƙiya'' a yankin ba su gagari jiragen yaƙin mu ba.