Matakan da gwamnatin Tinubu ke ɗauka wajen daƙile matsalar tsaro ba sa aiki - Amnesty

Asalin hoton, AMNESTY INTERNATIONAL
Ƙungiyar Amnesty International ta ce yadda garkuwa da mutane domin karɓar kuɗin fansa da kashe-kashe ke ƙaruwa a arewacin Najeriya na jefa mutane cikin matsananciyar rashin tsaro da firgici.
Ƙungiyar ta ce matsalar ta ƙara fito da rashin ƙoƙarin gwamnati, wadda a cewarta ta gaza wajen kara rayuwa da dukiyar ƴan Najeriya.
A wata sanarwa da ƙungiyar ta Amnesty International ta fitar a ranar Litinin, ta ce: "yadda hare-haren Lakurawa da Mamuda da Boko Haram da ƴanbindiga ke sake zama ɗanye sun nuna cewa matakan da gwamnatin Tinubu ke ɗauka wajen daƙile matsalar tsaro ba sa aiki," kamar yadda sanarwar ta bayyana.
Bola Tinubu ya zama shugaban Najeriya ne a watan Mayun shekarar 2023, "da alƙawarin tabbatar da tsaro. Amma maimakon haka, sai matsalar ta ƙara ruruwa, inda hukumomi suka gaza kare rayuka da mutuncin dubban ƴan Najeriya," in sanarwar.
Sanarwar ta ƙara da cewa dokokin Najeriya tana nauyi a wuyanta na kare rayuka da dukiyar al'umma, "tare da tabbatar da kamawa tare da hukunta waɗanda suke aikata waɗannan laifuka, sannan a tabbatar an yi wa waɗanda aka illata adalci."















