Mu kwana lafiya
Mun zo ƙarshen rahotonni a wannan shafi na ranar Asabar.
Muna nan tafe da wasu sababbi gobe da safe.
Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da makwabta da kuma sauran sassan duniya na ranar Asabar 25 ga watan Oktoba, 2025.
Isiyaku Muhammed da Umar Mikail
Mun zo ƙarshen rahotonni a wannan shafi na ranar Asabar.
Muna nan tafe da wasu sababbi gobe da safe.

Asalin hoton, Reuters
Rahotanni daga Kamaru na cewa an kama manyan jagororin 'yanhamayya biyu da ke ƙawance da ɗantakarar shugaban ƙasa na hamayya Issa Tchiroma Bakary.
Haɗakar 'yanhamayya mai sunan Union for Change ta ce wasu zaratan sojoji cikin ɗamara da suka rufe fuskokinsu ne suka tsare Anicet Ekane da Djeuka Thcameni a gidajensu jiya Juma'a, daga nan kuma suka tafi da su wani wuri da ba a bayyana ba.
Majalisar tsarin mulkin ƙasar ta yi watsi da ƙararrakin da ke ƙalubalantar zaɓen, abin da ya janyo zanga-zanga a kan zargin maguɗi.
Tuni Tchiroma Bakary ya yi iƙirarin samun nasara a zaɓen, kodayake kafafen yaɗa labarai na ƙasar sun nuna cewa Shugaba mai-ci Paul Biya mai shekara 92 ne ke kan gaba.
A jibi Litinin ake sa ran fitar da sakamakon zaɓen na hukuma.

Asalin hoton, Reuters
An rufe rumfunan zaɓe a zaɓen shugaban ƙasar Ivory Coast, wanda shugaba mai ci Alassane Ouattara ke neman wa'adi na huɗu na shekara biyar.
An kaɗa ƙuri'a lami lafiya a mafi yawan yankuna, ban da 'yan rahotonni ƙalilan na tashin hankali da aka samu a wasu wurare da aka lalata akwatinan zaɓe.
Ana sa ran samun sakamakon zaɓen nan da ranar Alhamis, inda dole sai ɗantakara ya lashe fiye da kashi 50 cikin 100 na ƙuri'un kafin ya yi nasara.
The final result is expected to be declared by Thursday at the latest and the winner will have to secure over 50% of the votes.
Wasu daga ciki masu katin zaɓe sun bi umarnin 'yan'adawa Lauren Gbagbo da Tidjane Thiam na ƙin fita kaɗa ƙuri'a, wanda ake ganin ya taimaka wajen ƙarancin yawan masu kaɗa ƙuri'ar.
Ana ganin hana manyan 'yan'adawar biyu shiga zaɓen, da kuma kama masu zanga-zanga ya ƙara masa zafi.

Asalin hoton, Getty Images
Wata kotu a jihar Legas da ke kudancin Najeriya ta ɗaure wami direban jirgin ƙasa wata 18 a gidan yari saboda kama shi da laifin satar kuɗi.
Mai Shari'a Rahman Osodi na kotun da ke Ikeja ta kama Christopher Ekene Ofielu mai shekara 39 da laifin satar naira miliyan 6.9 a ranar Litinin da ta gabata, kamar yadda hukumar EFCC mai yaƙi da cin hanci ta ruwaito a yau Asabar.
Ɗaya daga cikin laifuka uku da kotun ta kama shi da su na tuhumar sa da tura kuɗin zuwa asusun ajiyarsa na banki daga dandalin HabariPay Ltd ba bisa ƙa'ida ba.
Lauyansa ya nemi alƙalin ya sassauta masa kasancewar ya yi nadama kuma shi ne karon farko da aka gurfanar da shi a gaban kotu.
Wannan ta sa mai shari'ar ya yanke masa hukuncin wata 18 a gidan yari, ko kuma biyan tarar naira miliyan ɗaya da rabi bisa sharaɗin sai ya mayar da kuɗin da ya sata cikin mako ɗaya.

Asalin hoton, EPA
An lalata akwatinan zaɓe da sauran kayayyaki a rumfunan zaɓe da dama da ke Zaguiéta a yankin tsakiyar Ivory Coast yayin da ake kaɗa ƙuri'a a zaɓen shugaban ƙasa.
Hukumomi sun ce masu adawa da sakamakon zaɓen ne suka tarwatsa kayayyakin zaɓe.
Tuni aka saka dokar hana fita a Yamoussoukro babban birnin ƙasar, inda masu zanga-zanga suka ƙona ofisoshin hukumar zaɓe a farkon makon nan. A ranar Juma'a aka saka dokar kafin ta daina aiki a ranar Lahadi bayan kammala jefa ƙuri'a.
Jami'an tsaro kusan 44,000 ne aka girke a sassan ƙasar domin kula da harkokin zaɓen.

Asalin hoton, @HilalALsudan_FC
Ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa uku na Sudan na fatan sun samu tudun tsira a Rwanda sakamakon yaƙin basasar da ake tafkawa a ƙasarsu.
Babbar gasar ƙwallon ƙafa ta Rwanda ta karɓi abokan hamayya Al-Hilal da Al-Merrikh da kuma as Al-Ahli Wad Madani a kakar wasa ta bana, abin da zai sa su ci gaba da taka leda da kuma bai wa magoya bayansu ƙwarin gwiwa.
Ƙungiyoyin biyu Al-Hilal and Al-Merrikh na garin Omdurman sun buga babbar gasar Mauritania ne a kakar da ta gabata, inda Al-Hilal ta yi ƙoƙari matuƙa a gasar zakarun nahiyar Afirka ta African Champions League.
Yanzu za a jira amincewar hukumar ƙwallon ƙafa ta Afirka Caf kafin su fara taka leda.

Asalin hoton, AFP
Ministan tsaron Pakistan Khawaja Asif ya ce ya yi amannar cewa gwamnatin Taliban na Afghanistan na son a samu maslaha, amma ya yi gargaɗin cewa rashin samun matsaya na nufin shiga yaƙi ka'in da na'in ne a tsakaninsu.
Wannan jawabin na zuwa ne a daidai lokacin da wakilan ƙasashen biyu ke zagaye na biyu tattaunawa domin nemo hanyoyin samar da zaman lafiya ta hanyar tsara yarjejeniyar tsagaita wuta, wadda ake ki yi a birnin Istanbul na ƙasar Turkiya.
A farkon wannan watan ne ƙasashen biyu suka amince su ɗan tsagaita bayan wata ƴar tattaunawa da suka yi.
Afghanistan dai ta dage kai ta fata cewa ba ta ba mayaƙan Pakistan maɓoya domin kai mata hare-hare daga cikin ƙasarta, kamar yadda gwamnatin Pakistan ɗin ke zargi.

Asalin hoton, Getty Images
Amurka ta kakaba takunkumi kan shugaban Colombia, wanda a baya ke ɗasa wa da Washington.
Amurka ta ce shugaba Petro ya bari ana fataucin miyagun kwayoyi a kasarsa kuma shugaba Trump na daukar matakai ne domin kare Amurka.
Jekadan Colombia a Amurka Daniel Garcia Pena ya shaida wa BBC cewa a cikinsu babu wanda ya taba tunani a kwakwalwasa cewa Mr Petro yana taimaka wa masu fataucin miyagun kwayoyi bayan ya shafe daukacin rayuwarsa yana yaki da su

Asalin hoton, Reuters
China da Amurka sun fara sabuwar tattaunawar kasuwanci tsakaninsu, inda manyan jami'an tattalin arzikin kasashen biyu ke tattaunawa a Malaysia.
Bangarorin biyu na tattaunawa ne kan barazanar da kasashen biyu ke yi wa juna musamman bayan shugaba Trump ya yi barazanar lafta wa China karin haraji kashi 100 na kayayyakin da ta ke shigar wa a Amurka.
Waklan kasashen biyu kuma na neman ganin ganawa tsakanin Donald Trump da Xi Jinping ta tabbata kamar yadda aka tsara a ranar Alhamis ba tare da wani cikas ba.

A yau Asabar al'ummar kasar Ivory Coast ke zaben shugaban kasa wanda ya raba kan kasar inda wasu ke son shugaba Alassane Ouattara ya yi tazarce, wasu kuma na ganin lokaci ne na samar da sabon shugabanci a kasar.
Zuwa yanzu dai zaɓe ya yi nisa, kuma masu sa ido daga ƙasashe, ciki har da tawagar tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan sun isa ƙasar domin tabbatar da sahihancin zaɓen.
Ga yadda take kayawa nan a zaɓen a cikin hotuna.






Asalin hoton, Borno State
Gwamnan jihar Borno Babagana Zulum ya yi kira ga gwamnatin Najeriya da ta ɗauki matakin gaggawa wajen nazari tare da gyara harkokin tsaron sararin samaniyar ƙasar domin daƙile amfani da jirage marasa matuƙa wajen kai hare-hare a ƙasar.
Zulum ya bayyana haka ne a ranar Juma'a a garin Mafa bayan wani hari da ƴan Boko Haram suka kai kamar yadda tashar Channels ta ruwaito.
"Babban abin da nake so in yi magana a nan shi ne amfani da jirage marasa matuƙa. An faɗa min cewa sun yi amfani da jirage marasa matuƙa a Dikwa. Wannan abin tashin hankali ne matuƙa."
"Yawaitar jirage marasa matuƙa a hannun maƙiya abu ne mai matuƙar haɗari. Dole mu haɗa ƙarfi da ƙarfe wajen daƙile wannan sabon salon," in ji Zulum.
Gwamnan ya ce akwai buƙatar a ƙara tsaurara matakan kariya a bakin iyakokin ƙasar, "sannan akwai buƙatar a ƙara inganta tsaron sararin samaniyarmu. Wannan mataki ne da ya kamata a ɗauka cikin gaggawa ba tare da ɓata lokaci ba."
Zulum ya yi kira ga al'ummar jihar da su riƙa ba jami'an tsaro haɗin kai ta hanyar kai su bayana sirri da za su taimaka musu wajen magance matsalolin tsaro.
"Maganar gaskiya mun samu labarin za a kai hari a Mafa, kuma dukkan hukumomin da suka cancanci sani an faɗa musu. Wannan ne ya sa nake tunanin akwai zagon-ƙasa a harkar. Shi ya sa nake a zo a duba tare da yin gyara."

Asalin hoton, Reuters
Shugaban Venezuela, Nicolas Maduro, ya zargi Amurka da abin da ya kira "kirkirar wani sabon yaki " ta hanyar aika dakaru masu yawa na ruwa zuwa yankin Caribbean.
Ma'aikatar tsaron Amurka ta Pentagon ta ce ta tura jiragen yaki ne domin karfafa abin da ta kira farmakin fatattakar masu safarar miyagun kwayoyi daga Venezuela.
Trump kenan ke cewa babu bukatar neman ayyana yaki illa kashe mutanen da ke fataucin kwayoyi Akwai karuwar fargaba kan cewa a zahiri Amurka na shirin hambarar da shugaba Maduro.
Hare-haren Amurka a yankin sun kashe mutum sama da 40 kawo yanzu - ba tare da wata hujja ba da ke tabbatar da cewa suna safarar miyagun kwayoyi.

Asalin hoton, Getty Images
A yau Asabar al'ummar kasar Ivory Coast ke zaben shugaban kasa wanda ya raba kan kasar inda wasu ke son shugaba Alassane Ouattara ya yi tazarce, wasu kuma na ganin lokaci ne na samar da sabon shugabanci a kasar.
Fargaba ta karu sosai tun bayan cire manyan 'yan takara biyu na jam'iyyun hamayya - wato tsohon shugaban kasar Laurent Gbagbo da Tidjane Thiam, wani jigo a fagen siyasa kuma abokin kawancen Ouattara kafin ya zama abokin hamayya.
Wakiliyar BBC ta ce Shugaba Ouattara ya yi kira ga magoya bayansa su fito su zabe shi duk da yan kasar da dama na tunanin shi zai lashe zaben kafin zaben an samu rikici a sassan kasar da dama inda aka kama daruruwan mutane
Alassane Ouattara mai shekara 83 yana takara ne domin neman mulkin kasar a zango na hudu.

Asalin hoton, Getty Images
Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Najeriya NEMA ta ce adadin waɗanda suka rasu a sanadiyar fashewar tankar man fetur a babban titin Bida zuwa Agaie a ƙaramar hukumar Katcha na jihar Neja sun ƙaru zuwa 45.
Hukumar ta ƙara da cewa zuwa yanzu akwai kusan mutum 63 da suke ci gaba da jinyar raunukan da suka samu, kamar yadda babban jam'in hukumar na shiryar jihohin Kwara da Neja ya bayyana wa tashar Channels a ranar Juma'a.
"Mun tabbatar da mutuwar mutum 45, maza 12 mata 27, sannan a akwai ƙananan yara guda shida. A ɓangaren waɗanda suka jikkata kuwa akwai kusan mutum 63, maza 24 mata 32 da ƙananan yara shida," in ji shi.

Asalin hoton, Getty Images
Sakataren harkokin wajen Amurka, Marco Rubio, wanda a halin yanzu yake ziyara a Isra'ila, ya nada wani gogaggen jami'in diflomasiyyar Amurka a matsayin wanda zai jagoranci mataki na gaba na yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza.
Stephen Fagin wanda wakilin BBC ya bayyana a matsayin kwararre zai jagoranci tawagar da ta kunshi wata cibiyar jami'an farar hula da na soji da za ta yi aiki a wajen Gaza.
Wakilin BBC ya ce Mataki na gaba na yarjejeniyar tsagaita wutar ya kunshi yadda Hamas za ta ajiye makamai - wanda masana ke ganin zai yi wahala har sai an tura wata runduna ta musamman ta kasa da kasa zuwa Gazaa

Asalin hoton, EPA
Rahotanni sun ce Isra'ila ta kashe mutum biyu a wasu hare-hare ta sama da ta kai a kudancin Lebanon.
Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta kai hari ne kan mambobin Hezbollah kuma ta kashe daya daga cikin manyan kwamandojinta Abbas Hassan Karky.
Isra'ila ta dade tana kai harin bama-bamai a kudancin Lebanon duk da yarjejeniyar da ta kulla da Hezbollah kusan shekara daya.
Barkanmu da safiya masu bibiyar wannan shafin na labaran kai-tsaye.
A yau ma za mu ci gaba da kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
Da fata za ku kasance tare da mu.