Isra'ila ta jinkirta rusa filin ƙwallon ƙafa na yaran Falasdinawa

Isra'ila ta ɗage rusa filin wata ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta yaran Falasɗinawa a birnin Bethlehem, da ke yankin gaɓar yamma da kogin Jordan da ta mamaye.
Isra'ila ta ce an gina filin na Aida Youth Centre ba tare da izinin da ya dace ba.
Ta ce rushe filin ya zame dole saboda dalilai na tsaro.
Da alama dai wani yunƙurin da ƙasashen duniya ke yi na ceto filin, ciki har da takardar koke mai dauke da sa hannun sama da mutane dubu ɗari biyar,ya tilastawa hukumomi sake tunani.
Sai dai ƙungiyar ta ce har yanzu ba ta samu wata sanarwa a hukumance ba.
A cikin sanarwar ta baya-bayan nan, rundunar sojin Isra'ila ta sake nanata iƙirarinta na cewa filin wasan kwallon kafar na haifar da matsalar tsaro.



























