Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 23/11/2024

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 23/11/2024

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza da Muhammad Annur Muhammad

  1. Rufewa

    Jama'a masu bibiyarmu a wannan shafin na BBC Hausa, da ke kawo muku labaran abubuwan da ke wakana a Najeriya da sauran sassan duniya kai tsaye, a nan za mu rufe shafin na yau Asabar 23/11/2024.

    A madadin kowa da kowa ni Muhammad Annur Muhammad nake fatan za ku kasance da mu gobe Lahadi.

    Mu rufe da wannan karin maganar da ke cewa - Danyen kasko ba ya kai ruwan wanka banɗaki

  2. Tattaunawar taron ƙoli na duniya kan sauyin yanayi ka iya rugujewa - Rahoto

    Taron sauyin yanayi

    Asalin hoton, OTHERS

    Mai masaukin bakin taron kolin sauyin yanayi na Majalisar Dinkin Duniya a Azerbaijan sun bukaci wakilan da suka halarci taron da su yi watsi da rashin jituwar da ke tsakaninsu domin cimma matsaya.

    Ana ci gaba da ce-ce-ku-ce kan muhimmin batun nawa ne kasashe masu arziki za su biya kasashe masu tasowa, don taimaka musu wajen shawo kan tasirin sauyin yanayi.

    Wakilin BBc ya ce akwai yarjejeniya a kasa da ta ce kasashe masu arziki za su biya dala biliyan dari amma wannan yarjejeniyar za ta kare ne a shekara mai zuwa kuma akwai bukatar a cimma wata sabuwar matsaya.

    Tuni dai wasu kasashe masu tasowa suka fice daga taron da ake yi a Baku, kuma tattaunawar na iya rugujewa

  3. Rasha ta zafafa hare-haren ƙwato wani yanki a Ukraine kafin Trump ya hau mulki - Zelensky

    Volodymyr Zelensky

    Asalin hoton, OTHERS

    Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya yi ikirarin cewa a yanzu Rasha ta bayar da fifiko ne wajen kwato yankunan Kursk da ke hannun sojojin Ukraine.

    Fiye da watanni uku kenan tun da Kyiv ta mamaye yankin kuma Mista Zelensky ya ce Moscow na son nuna cewa ta dawo da iko kafin ranar ashirin ga watan Janairu, ranar da za a rantsar da Donald Trump.

    Ba a san takamaimain adadin kashin yankin da Ukraine ke rike da shi ba - amma an ruwaito majiyar sojan Ukraine a yau Asabar tana mai cewa ta rasa kusan rabin yankin.

  4. Hamas ta ce harin Isra'ila ya kashe wata mata da ta yi garkuwa da ita a Gaza

    Masu zanga-zanga

    Asalin hoton, Reuters

    Kungiyar Hamas ta ce an kashe wata mace Ƴar Isra'ila da ta yi garkuwa da ita a yayin wani harin bam da Isra'ila ta kai a arewacin Gaza amma dai ba ta bayyana sunan matar ba.

    Kungiyar ta kara da cewa wata mace da aka yi garkuwa da ita tare da wadda aka kashen tana cikin hadari.

    Wannan ikirari ya biyo bayan gazawar cimma yarjejeniyar tsagaita wuta da aka kwashe watanni ana yi wadda za ta tabbatar da sakin mutanen da aka yi garkuwa da su.

    Jami'an kiwon lafiya na Gaza sun ce akalla Falasdinawa 120 ne aka kashe a fadin yankin cikin sa'o'i 48 da suka gabata.

  5. Hare-haren Isra'ila sun kashe mutum aƙalla 30 da rauna sama da 70 a Lebanon

    Ma'iakatan agaji da jama'a

    Asalin hoton, Reuters

    Ma'aikatar lafiya ta kasar Labanon ta ce akalla mutum 30 ne suka mutu yayin da sama da saba'in suka jikkata sakamakon hare-haren da Isra'ila ta kai.

    Yanzu dai an tabbatar da cewa mutum 15 ne suka mutu a wani harin da aka kai a tsakiyar birnin Beirut wanda ya rusa wani gini mai hawa takwas.

    Wasu rahotanni na cewa harin yunkuri ne na kashe wani babban jami'in kungiyar Hezbollah - wanda aka ce ya tsira.

    Ma'aikatar ta ce an kashe wasu mutum 15 da suka hada da uwa da 'ya'yanta hudu a hare-haren da Isra'ila ta kai a kusa da birnin Baalbek da ke gabashin ƙasar.

  6. Gwamnatin Oyo ta yi barazanar ƙwace kadara ko ɗaure duk wanda ya ƙi biyan haraji

    Gwamna Seyi Makinde

    Asalin hoton, SEYIMAKINDE/FACEBOOK

    Gwamnatin jihar Oyo da ke kudu maso yammacin Najeriya ta gargaɗi masu harkokin kasuwanci da mazauna jihar a kan ƙin biyan haraji, inda ta yi barazanar ɗaukar matakin shari'a a kan mutum.

    Shugaban hukumar tara kuɗaɗe ta jihar, Mista Olufemi Awakan ne ya yi gargaɗin a wata sanarwa da hukumar ta fitar, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito a ranar Asabar.

    Sanarwar ta ce lokaci ya yi da za a biya duk wani haraji da ba a biya ba, kamar yadda doka ta yi tanadi dukkanin wani mazaunin jihar ya sauke nauyin da ya rataya a wuyansa na haraji.

    Mista Awakan ya ce, biyan haraji ba zaɓi ba ne abu ne da ya zama wajibi kamar yadda yake a sashe na 24 na kundin tsarin mulki Najeriya.

  7. Gwamnonin PDP sun bai wa shugabancin jam'iyyar wa'adin shirya taro

    Taron gwamnonin PDP

    Asalin hoton, PDP Governors' Forum

    Gwamnonin babbar jam'iyyar hamayya ta Najeriya, PDP sun bai wa kwamitin gudanarwar jam'iyyar da ke karkashin shugabancin Umar Damagum wa'adin zuwa watan Fabarairu ya shirya taron kwamitin zartarwa.

    Kungiyar gwamnonin ta sanar da wa'adin ne a takardar bayan taronta wadda shugabanta kuma gwamnan jihar Bauchi Bala Mohammed ya karanta wa manema labarai, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito a yau Asabar.

    Tun a watan Agusta kwamitin gudanarwar yake ta daga babban taron kwamitin zartarwar, wanda a lokacin za a tattauna matsalollin da ke addabar jam'iyyar tare da gabatar da sabon shugaban da zai maye Damagum, don kammala wa'adin Iyorchia Ayu da aka dakatar

    A sanarwar gwamnonin sun ce suna la'akari da damuwar 'yan Najeriya da ta wadanda suka kafa jam'iyyar ta PDP da dattijai da kuma 'yan jam'iyyar kan rarrabuwar kan da aka samu a jam'iyyar.

    Gwamnonin na PDP sun kuma nuna takaicinsu kan sakamakon zaben gwamnonin EDo da Ondo, wadanda APC ta ci inda suka yi kira ga bangaren shari'a da ya ceto dumukuradiyyar kasar.

  8. Rasha za ta sake amfani da mugun sabon makami mai linzami idan ta kama - Putin

    Vladimir Putin

    Asalin hoton, EPA

    Rasha tana da tarin sababbin makamai masu linzami da za ta iya amfani da su da zarar bukatar hakan ta taso in ji Shugaban kasar Vladimir Putin.

    Shugaban ya bayyana hakan ne kwana daya bayan da Rashar ta harba wani mugun makami mai linzami a kan birnin Dnipro na Ukraine.

    A wani jawabi da ya gabatar ta talabijin kwatsam ba tare da sanarwa ba, Putin wanda ya yi alkawarin sake gwajin wannan makami ciki har da a fagen daga, ya ce makamin ba za a iya tare shi ba.

    Amfani da sabon makamin da Rashar ta yi ya zo ne bayan da Ukraine ta yi amfani da makamai masu linzami da ke cin dogon zango na Amurka da na Birtaniya zuwa cikin yankunan Rashar a karon farko.

    Shugaba Zelensky na Ukraine ya yi kira ga shugabannin duniya da su mayar wa da Rasha mummunan martani da ya ce Putin zai dandana kudarsa.

  9. 'Yansanda sun kama magoya bayan Real Madrid kan zargin nuna wa 'yan wasan Barcelona wariyar launin fata

    'Yan wasan Barcelona

    Asalin hoton, Getty Images

    'Yansanda a Sifaniya sun ce sun kama wasu magoya bayan ƙwallon ƙafa uku bisa zargin alaƙa da nuna wariyar launin fata da aka yi wa 'yan wasan Barcelona lokacin wasan ƙungiyar da Real Madrid a watan da ya gabata.

    Wasu magoya bayan Mardid sun nuna wa Lamine Yamal da Alejandro Balde wariyar launin fata a lokacin wasan da Barcelona ta doke Madrid har gida da ci 4-0.

    An zargi mutanen uku, manya biyu da ƙaramin yaro guda ta yin kalaman ƙyama, an kuma gano suna amfani da wayoyin hannu wajen yaɗa kalaman.

    Hukumar ƙwallon ƙafar Sifaniya na ƙoƙarin kakkaɓe matsalar wariyar launin fata, inda a shekarun baya-bayan aka samu irin waɗannan matsaloli.

    A baya-bayan nan ɗan wasan Real Madrid Vinicius Junior ya zama mutumin da ya ɓullo da wayar da kan jama'a game da yadda za a magance matsalar.

  10. Hukumar Hisbah a Kano za ta ci gaba da rufe shagunan caca a jihar

    Aminu Ibrahim Daurawa

    Asalin hoton, Aminu Ibrahim Daurawa/X

    Hukumar Hisbah ta jihar Kano a Najeriya ta ce za ta ci gaba da bin tsarinta na rufe shagunan masu caca bayan hukunci wata kotu.

    A ranar Juma'a kotun ƙolin ƙasar ta rushe dokar 2005, da ta amince da kafa hukumar kula da caca da halasta cacar wasanni a ƙasar.

    Kotun ta ce hukuncin na nufin gwamnatocin jihohi ne ke da wuƙa da nama game da dokokin da suka shafi caca.

    Daraktan hukumar Hisbah na jihar Kanon, Dakta Abba Sufi ya ce hukuncin kotun na nufin hukumarsu za ta ci gaba da kai samame tare da rufe shagunan caca a faɗin jihar, saboda haramcin sana'ar a ƙarƙashin dokokin Musulunci.

    Abba Sufi ya ce iyayen yara na yawan ƙorafi game da yadda yaransu ke ci gaba da faɗawa komar wannan mummunar sana'a a daidai lokacin da matsin rayuwa da talauci ke ƙaruwa tsakanin al'umma.

    Jihar Kano na ɗaya daga cikin jihohin Najeriya da ake amfani da dokokin addinin Musulunci baya da dokokin ƙasa.

    A watan da ya gabata hukumar Hisbar jihar ta kai samame tae da rufe gomman shagunan caca a faɗin birnin Kano.

    To sai dai an dakatar da samamen sakamakon ƙarar da wasu ƙungiyoyi suka shigar, dogaro da cewa caca ba laifi ba ne a ƙarƙashin dokokin Najeriya.

  11. EU ta janye jakadanta daga Jamhuriyar Nijar

    Shugaban mulkin sojin Nijar

    Asalin hoton, ORTN

    Ƙungiyar Tarayyar Turai ta ce ta janye jakadanta a Jamhuriyar Nijar bayan da gwamnatin mulkin sojan ƙasar ta nuna shakku kan yadda ƙungiyar ke kai agaji ga waɗanda ambaliyar ruwa ta shafa a Nijar.

    A ranar Juma'a ma'aikatar harkokin wajen Nijar ta zargi ƙungiyar EU ta raba kuɗaɗe kai tsaye ga ƙungiyoyi masu zaman kansu, maimakon bi ta hannun hukumomin da ke sa ido kan yadda ake raba tallafin.

    Hukumomin na Nijar sun zargi jakadan na EU a ƙasar, Salvador Pinto Da Franca da almubazzaranci da kuɗaɗen.

    Tun bayan juyin mulkin da ya hamɓarar da shugaba Mohamed Bazoum a shekarar da ta gabata ake samun ƙaruwar takun saƙa tsakanin ƙasar da ƙungiyar ta EU.

    Shugabannin sojin ƙasar sun juya wa tsohuwar uwargijiyarsu - Faransa - baya, sannan suka rage ƙawance ga ƙasashen Turai.

  12. Jiragen Isra'ila sun ci gaba da luguden wuta a Lebanon

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Jiragen yaƙin Isra'ila sun ci gaba da luguden wuta a Beirut babban birnin ƙasar Lebanon bayan harin da ta kai kan wani bene mai hawa takwas da ke tsakiyar birnin

    Ma'aikatar lafiya ta ƙasar Lebanon ta ce aƙalla mutum 11 ne suka mutu, tare da jikkata wasu fiye da 60, a wasu hare-hare da aka kai a faɗin birnin.

    Masu aikin ceto na ci gaba da neman waɗanda suke da sauran rai a maƙale cikin baraguzai.

    An kuma bayar da rahoton tashin wasu manyan bama-bamai a wata unguwa da ke kudancin ƙasar.

    Sojojin Isra'ila sun ce sun kai hari wasu wuraren da ke da alaƙa da ƙungiyar Hezbullah cikin cikin kwana guda.

    Kafofin yada labaran kasar Labanon sun ruwaito cewa wani kwamandan ƙungiyar Hezbullah na ɗaya daga cikin waɗanda aka nufata da harin.

    A cikin 'yan watannin baya-bayan nan, hare-haren da Isra'ila ta kai ta sama sun kashe wasu shugabannin Hezbullah a Beirut.

  13. Gwamnatin Sokoto ta sake kafa hukumar Hisbah

    Ahmad Aliyu

    Asalin hoton, Ahmad Aliyu/ X

    Gwamnatin jihar Sokoto ta sake ƙaddamar da hukumar Hisbah a faɗin jihar, domin yaƙi da gurɓacewa tarbiyyar al'umma a jihar.

    Cikin wani saƙo da gwamnan jihar, Ahmad Aliyu ya wallafa a shafinsa na X, ya ce ya sake kafa hukumar ne saboda irin gudunmowar da take bayarwa wajen yaƙi da gurɓacewar tarabiyya.

    Gwamna Ahmad Aliyu da Daurawa

    Asalin hoton, Ahmad Aliyu/ X

    Bayanan hoto, Shugaban hukumar Hisbah na jihar Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daura na daga cikin mutanen da suka halarci taron ƙaddamarwar

    Gwamnan ya kuma ya buƙaci sabbin jami'an hukumar da su gudanar da ayyukansu bisa doka ba tare da cin zarafin kowa ba.

    Ahmad Aliyu ya ce sabuwar hukumar da ya kafa ba wai za ta maye gurbin sauran hukumomin tsaro ba ne, sai ma dai ta taimaka musu wajen gudanar da ayyukansu na kare rayuka da dukiyoyi.

    Jami'an Hisbah na Sokoto

    Asalin hoton, Ahmad Aliyu/ X

    Dokokin jihar sun bai wa hukumar damar kama masu laifi tare da hannun ta su ga jami'an 'yansanda domin a gurfanar da su a gaban Kotun Shari'a.

    Gwamnan ya kuma yi kira ga al'ummar jihar su bai wa sabuwar hukumar goyon bayan datake buƙata wajen gudanar da ayyukanta.

  14. Tarayyar Turai ta alƙawarta ƙara kuɗin tallafin magance sauyin yanayi a taron COP29

    COP29

    Asalin hoton, Getty Images

    Rahotanni daga wurin taron ƙolin kan sauyin yanayi na COP2 da ke gudana ƙasar Azerbaijan na cewa ƙungiyar Tarayyar Turai ta yi alƙawarin ƙara yawan kuɗaɗen da kasashe masu arziki ke bayar wa don taimaka wa ƙasashe masu tasowa wajen tunkarar sauyin yanayi.

    Tarayyar Turai ta alƙawarta ƙara dala biliyan hamsin a shekara.

    Batun bayar da tallafin dai na zaman wani babban batu wajen cimma matsaya a taron na bana, inda ƙasashe matalauta suka yi watsi da tayin dala biliyan 250 tun da farko.

    Ƙungiyar EU na kiran a riƙa gudanar da bita a kowace shekara kan ƙoƙarin da duniya ke yi na kawar da gurɓataccen hayaƙi, amma rahotanni sun ce Saudiyya na adawa da hakan.

    Tun da farko an shirya kammala taron a ranar Juma'a.

  15. Taron G20 ya sake fito da damar haɗin kan duniya don kawar da yunwa da talauci - Tinubu

    Bola Ahmed Tinubu

    Asalin hoton, Bola Ahmed Tinubu/Facebook

    Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya ce tattaunawar da aka yi a taron G20 a Brazil, ta sake bayyana babbar damar haɗin kai tsakanin ƙasashe don tunkarar ƙalubalen da duniya ke fuskanta gaba ɗaya.

    Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinta na Facebook bayan gabatar da jawabi a taron, Shugaba Tinubu ya ce a taron G20 na bana, Najeriya ta amince da yunƙurin shugaban ƙasar Brazil na neman haɗin kan duniya domin kawar da babbar barazanar da duniya ke fuskanta, wato yunwa da talauci.

    ''Wannan ƙuduri ya yi daidai da muradin Najeriya na yaƙi da yunwa da talauci, da samar da ci gaba mai ɗorewa ta hanyar samar wa 'yan Najeriya ayyukan yi'', in ji shi.

    Shugaban na Najeriya ya sake jaddada shawarar ƙasashen Afirka na sake fasalin cibiyoyin duniya, ciki har da Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya da ƙungiyar G20, don tabbatar da adalci da tafiya da kowa ta yadda Najeriya da ƙasashen Afirka za su shiga a dama da su wajen ɗaukar matakai a waɗanann cibiyoyi.

    ''A kan sauye-sauyen tattalin arziki, na jaddada ƙudurin Najeriya na tabbatar da adalci a tsarin haraji na duniya da tsarin hada-hadar kuɗi wanda zai cike giɓin da ke tsakanin manyan da ƙananan ƙasashen duniya''.

    Shugaba Tinubu ya kuma a yayin da gwamnatinsa ke neman faɗaɗa haraji ta Najeriya ba tare da ƙara wa 'yan ƙasa wahala ba, gwamnatin ta mayar da hankali kan rage wahalhalu da ɓullo da ƙarin damarmaki da inganta ayyukan more rayuwa, da ƙarfafa ilimi da cibiyoyin tsaro da zamantakewa, waɗanda ya ce suna da mahimmanci don sake farfaɗo da ci gaban ƙasar.

  16. Tinubu ya nemi majalisa ta amince ya tabbatar da Janar Oluyede babban hafsan sojin ƙasa

    Janar Oluyede

    Asalin hoton, Nigerian Army/X

    Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya aike wa majalisar dattawan ƙasar buƙatar neman amincewarta don tabbatar da naɗin Laftanar Janar Olufemi Olatubosun Oluyede a matsayin cikakken babban hafsan soji ƙasa na Najeriya.

    Cikin wata sanarwa da kakakin shugaban ƙasar, Bayo Onanuga ya fitar ranar Juma'a ya ce Shugaba Tinubu ya aike da wasiƙar ne kamar yadda kundin tsarin mulkin ƙasar da na dokar aikin sojin ƙasar suka tanada.

    A ranar 30 ga watan Oktoba ne Shugaba Tinubu ya naɗa Janar Oluyede a matsayin muƙaddashin babban hafsan sojin ƙasan, bayan rashin lafiyar Latfanar Janar Taoreed Lagbaja, wanda ya mutu ranar 5 ga watan Nuwamban da muke ciki.

    Sanarwar ta ce shugaban ƙasar na da ƙwarin gwiwa kan jagoranci da ƙwarewar Laftanar Janar Oluyede, don haka ne yake son majalisar ta tabbatar da shi, don ya jagoranci rundunar sojin ƙasa ta Najeriya domin tabbatar da zaman lafiya da tsaron ƙasar.

  17. Kane ya kafa tarihin zira ƙwallo 50 cikin wasanni ƙalilan a Bundesliga

    Kane

    Asalin hoton, Rex Features

    Kaftin ɗin tawagar Ingila, mai taka leda Bayern Munich, Harry Kane ya kafa tarihin cin kwallo 50 cikin wasannin ƙalilan a babbar gasar tamola ta Jamus.

    Dan wasan gaban ya ci ƙwallo uku rigis a wasan da Bayern Munich ta doke Augsburg da ci uku da nema a ranar Juma'a a Bundesliga a wasansa na 43 da ya buga wa ƙungiyar a gasar.

    Da wannan bajinta Kane ya goge tarihin da Erling Halland ya kafa na cin wallo 50 a wasa 50 da ya buga wa Borussia Dortmund.

    A shekarar da ta gabata ne Bayern ta sayi Kane daga Tottenham Hotspur ta Ingila kan kuɗi dala miliyan 150, wani abu da bai yi wa da dama daga cikin magoya bayan Hotspur daɗi ba.

  18. 'Za mu yi amfani da dabarun zamani don magance rikicin manoma da makiyaya'

    Shugaban Najeriya

    Asalin hoton, Bola Tinubu/X

    Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa na baƙin ƙoƙarinta wajen lalubo hanyoyin magance rikice-rikicen manoma da makiyaya.

    Yayin da yake jawabi bayan sanya hannu da wasu kamfanin sarrafa nama na JBS a birnin Rio de Janeiro na ƙasar Brazil, Shugaba Tinubu ya ce rikicin manoma da makiyaya ya jima yana haifar da asarar dukiyoyi a wasu yankunan Afirka.

    ''Rikici tsakanin manoma da makiyaya da ke haifar da asarar rayuka da zubar da jini, idan aka yi amfani da dabarun zamani da wayewa wajen magancenta, zai kawo ci gaban tattalin arzikinmu'', in ji shugaban ƙasar.

    Bayan ƙulla yarjejeniyar kamfanin sarrafa nama na JBS ya amince da zuba jarin dala miliyan 2.5 domin gina kamfanonin sarrafa nama shida a faɗin Najeriya.

    Kamfanin ya ce uku daga cikin kamfanonin za su mayar da hankali wajen sarar naman kaji, ayayin da biyu za su sarrafa jan nama, sai kuma guda wanda zai sarrafa nama aladu.

    Shugaba Tinubu ya ce gwamnatinsa za ta mayar da hankali wajen gayyato masu zuba jari daga ciki da wajen ƙasar a ɓangaren kiwon dabbobi da noma, lamarin da ya ce zai taimaka wajen magance rikici tsakanin manoman da makiyaya, tare da yaƙar yunwa da talauci da inganta ci gaban tattalin arziki.

  19. Trump ya naɗa ƙarin muƙamai huɗu

    Trump

    Asalin hoton, Reuters

    Zaɓaɓɓen shugaban Amurka Donald Trump ya ci gaba da naɗin manyan muƙaman gwamnatinsa.

    A ranar Juma'a Mista Turm ya sanar da naɗin 'yar majalisa Republican, Lori Chavez-DeRemer a matsayin sakatariyar ƙwadago.

    Sai kuma tsohon dan gidan Dave Weldon da ya naɗa shugaban hukumar lafiya matakin farko.

    Shi kuwa Dr Marty Makary ya samu muƙamin kwamishinan hukumar kula da ingancin abinci da magunguna.

    Mista Trump ya kuma zaɓi tsohon ɗan ƙwallon Amurka Scott Turner a matsayin sakataren gidaje da birane da karkara.

  20. Mutum huɗu sun mutu, fiye da 20 sun jikkata bayan mummuman hari a Beirut

    hari

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Masu aikin ceto na duba cikin ɓaraguzan babban ginin da ya ruguje a Beirut

    Ma'aikatar lafiyar Lebanon ta ce mutum huɗu sun mutu yayin da fiye da 20 suka jikkata bayan Isra'ila ta ƙaddamar da wani mummunan hari a tsakiyar birnin Beirut.

    Harin makamai masu linzami da jirgin yaƙin Isra'ilar ya kai sun faɗa kan wani ginin farar hula mai hawa takwas a tsakiyar birnin na Beirut.

    An ji mummunar ƙarar fashewar a ɗaukacin birnin da safiyar yau Asabar.

    Kamfanin dillancin labaran Lebanon ya ce makamai masu linzami biyar da aka harba kan ginin da ke unguwar Basta a birnin sun ruguza ilahirin benen.

    Tun da fari jami'ai a Lebanon sun ce sama da mutum 60 ne suka mutu, yayin da wasu da dama suka jikkata a harin da Isra'ila ta kai a wajen birnin Beirut a ranar Juma'a.