Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 25/02/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Laraba 25 ga watan Fabrairun 2026.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Daga Aisha Babangida da Isiyaku Muhammad

  1. Sabon sufetan ƴansandan Najeriya ya kama aiki

    xxx

    Asalin hoton, X/Nigeria Police

    Sabon sufetan ƴansandan Najeriya Olatunji Ridwan Disu ya kama aiki a matsayin babban sufetan ƴansandan ƙasar na 23.

    Ya karɓi ragama ne daga Kayode Adeolu Egbetokun wanda ya ajiye aiki a ranar jiya Talata, 24 ga watan Fabarairu.

    Hakan na zuwa ne bayan shugaban Najeriya Bola Tinubu ya laƙa wa Disu muƙamin sufetan ƴansanda a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.

    xxx

    Asalin hoton, X/Nigeria Police

    A jiya Talata ne shugaban na Najeriya ya sanar da nadin Olatunji Disu a matsayin sufetan ƴansandan ƙasar bayan Egbetokun ya miƙa takardar ajiye aiki bisa da dalilai na ƙashin kai.

  2. Mutum bakwai sun mutu a harin da Ukraine ta kai kan wata masana'anta a Rasha

    ...

    Asalin hoton, Social Media

    Jiragen saman yaƙi marasa matuƙa na Ukraine sun kai wa wata masana'antar sarrafa takin zamani da ke yammacin Rasha hari, inda suka kashe mutane bakwai tare da jikkata aƙalla wasu mutum goma.

    Kwamitin bincike na Rasha ya ce jiragen sama marasa matuƙa 30 ne suka kai hari a masana'antar a yankin Smolensk mai tazarar kilomita 290 daga kan iyaka da Ukraine.

    A wani saƙon da ya wallafa a shafukan sada zumunta, gwamnan yankin Vasily Anokhin ya ce "maƙiyanmu sun kai hari... wata cibiya ta farar hula", a wani abin da ya kira "mummunan harin ta'addanci na dakarun sojin Ukraine."

    Masana'antar - wadda ke cikin birnin Dorogobuzh - tana samar da ammonium nitrate da nitric acid waɗanda ake amfani da su wajen samar da taki, amma kuma ana iya amfani da su wajen haɗa abubuwa masu fashewa.

  3. Somaliland ta naɗa jakadanta na farko zuwa Isra'ila

    Somaliland's president Abdirahman Mohamed Abdullahi

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Shugaban Somaliland Abdirahman Mohamed Abdullahi

    Somaliland ta naɗa babban jami'in diflomasiyya Mohamed Omar Hagi Mohamoud a matsayin jakadanta na farko a Isra'ila, bayan hukuncin da Isra'ila ta yanke a watan Disamban da ya gabata na amincewa da jamhuriyar da ta ayyana kanta a matsayin ƙasa mai cin gashin kanta.

    Wata wasiƙar da aka wallafa a shafin Facebook na fadar shugaban ƙasar Somaliland ta tabbatar da cewa shugaba Abdirahman Mohamed Abdullahi ya naɗa Mista Hagi a matsayin "Jakada mai cikakken iko."

    Jami'in diflomasiyyar a baya ya taɓa zama mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin waje kuma ya kasance wakilin Somaliland a Taiwan.

    A ranar 26 ga watan Disambar 2025 ne Isra'ila ta amince da ƙasar Somaliland a hukumance, inda ta zama ƙasa ta farko da ta amince da hakan fiye da shekaru talatin bayan da yankin ya ayyana ɓallewa daga Somaliya.

    Firaminista Benjamin Netanyahu ya bayyana matakin a matsayin goyon bayan "yancin cin gashin kai" na Somaliland tare da tsare-tsaren haɗin gwiwa a fannin noma da kiwon lafiya da fasaha.

  4. Ziyarar Modi zuwa Isra'ila za ta yi nuni da muradun India a Gabas ta tsakiya - Masana

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Firaministan Indiya Narendra Modi ya kai ziyarar kwanaki biyu a Isra'ila, wadda ita ce ta farko tun bayan da aka fara yaƙin Gaza.

    Ana sa ran Modi zai yi jawabi ga majalisar dokokin Isra'ila, wato Knesset, sannan ya gana da firaminista Benjamin Netanyahu da shugaba Isaac Herzog.

    Ba adi shirya wata ganawa tsakaninsa da shugabannin Falasdinawa ba.

    Ziyarar ta zo ne a daidai lokacin da ƙasashen biyu ke ƙoƙarin ƙarfafa alaƙa a fannin tsaro, fasaha da kasuwanci - dangantakar da ta samu ci gaba sosai tun bayan hawan Modi kan karagar mulki fiye da shekaru goma da suka gabata.

    Manazarta, sun ce ziyarar za ta kuma kasance manuniya ga manufofin ƙasashen ƙetare na Indiya yayin da take ƙoƙarin daidaita alaƙar ta da Isra'ila da sauran ƙasashen gabas ta tsakiya.

  5. Ambaliya ta kashe mutum 32 a Brazil

    ...

    Asalin hoton, Andre Coelho/EPA

    Aƙalla mutum 32 ne suka mutu sakamakon zaftarewar ƙasa da ambaliyar ruwa sakamakon mamakon ruwan sama a jihar Minas Gerais na ƙasar Brazil.

    Birane biyu da lamarin ya fi shafa su ne Juiz de Fora, inda gidaje 12 suka ruguje sakamakon zaftarewar laka, da kuma Ubá, inda wani kogi ya tumbatsa.

    Masu aikin ceto na neman aƙalla mutane 38 da har yanzu ba a san inda suke ba, an kuma tanadi matsugunai ga dubban mutanen da suka rasa gidajensu.

    Masana yanayi sun ce ruwan sama da aka yi a yankin a wannan watan ya riga ya ninka na matsakaicin da ake sa ran za a yi a watan Fabrairu, kuma ana hasashen ƙarin ruwan sama a kwanaki masu zuwa.

  6. Tinubu ya naɗa wa Tunji Disu muƙamin sufetan ƴansanda

    ...

    Asalin hoton, Stae House

    Shugaba Bola Tinubu ya ɗaurawa Tunji Disu mukami a matsayin mukaddashin Sufeto-Janar na ƴan sandan Najeriya.

    Bikin dai ya gudana ne a ranar Laraba a fadar gwamnati da ke Abuja.

    Naɗa wa Disu mukamin dai na zuwa ne kwana guda bayan da Tinubu ya sanar da shi a matsayin babban ɗan sandan ƙasa.

    Nadin nasa ya biyo bayan murabus ɗin da tsohon Sufeto-Janar na ƴan sanda, Kayode Egbetokun ya yi, wanda fadar shugaban ƙasa ta tabbatar a ranar Talata.

    Ya zuwa lokacin da aka naɗa shi, Disu ya taɓa kasancewa mataimakin babban sufeto-Janar mai kula da sashen binciken manyan laifuka na rundunar (FCID) Annex, Alagbon, Legas.

    An ƙara masa girma zuwa muƙamin mataimakin sufeto-Janar na ƴan sanda a bara.

    Kafin nan ya taɓa zama kwamishinan ƴan sanda a jihar Ribas kafin daga bisani Egbetokun ya tura shi Abuja a matsayin kwamishinan ƴan sanda na babban birnin tarayya.

  7. Jami'o'i da dama na sake shiga zanga-zangar adawa da gwamnatin Iran

    ...

    Asalin hoton, Telegram/EEAUT

    Wasu sabbin Bidiyo da aka tantance sun nuna zanga-zangar da dalibai ke jagoranta a Iran sun gudana aƙalla jami'o'i 13 tun daga ranar Asabar.

    Daga cikinsu akwai Jami'ar Fasaha ta Sajjad da ke Mashhad, birni na biyu mafi girma a Iran.

    Wani bidiyo ya nuna wasu gungun dalibai a babbar farfajiyar jami'ar suna rera waƙa suna nuna adawa da dakarun sa kai na Basij, wani ɓangare na rundunar kare juyin juya halin Musulunci (IRGC) na sojojin Iran, waɗanda mambobinsu suka yi arangama da ɗalibai masu zanga-zanga a wannan mako.

    An ji ɗalibai masu adawa da gwamnati suna rera taken "Allah Ya ja zamanin Shah", yayin da ɗalibai masu goyon bayan gwamnati ke ɗaga tutar Jamhuriyar Musulunci.

  8. An sanya wa jagororin RSF takunkumai kan kashe-kashe a garin El Fasher na Sudan

    ...

    Asalin hoton, Anadolu via Getty Images

    Kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya sanar da sanya wasu sabbin takunkumai kan wasu jagororin rundunar RSF huɗu kan ta'asar da aka aikata a garin El Fasher.

    Mataimakin kwamandan dakarun RSF, Abdul Rahim Hamdan Dagalo da Abu Lu-lo da aka yiwa laƙabi da Butcher of El Fasher watau wanda ya rika kashe kashe a garin El fasher na cikin waɗanda aka sanyawa takunkuman

    MDD ta ce Abdulrahim Da-ga-lo shi ne ya jagoranci farmakin da mayakan RSF suka kai garin na Elfasher a lokacin da ya faɗa hannunsu inda suka aiwatar da kisan kiyashi kan waɗanda ba larabawa bane.

    A makon da ya gabata wata tawagar masu bincike ta Majalisar Dinkin Duniya ta yanke hukuncin cewa farmakin ya kunshi alamomin kisan kare dangi.

  9. An samu gagarumin sauyin da aka daɗe ba a gani ba a shugabanci na - Trump

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaba Donald Trump ya gabatar da jawabi na fito na fito a zauren Majalisar dokokin Amurka inda ya yaba da abinda ya ce gagarumin sauyin da aka samu a cikin ƙasar wanda an shafe tsawon shekaru ba a taɓa ganin irinsa ba

    Wannan na zuwa ne a dai dai lokacin da ƙuriar jin ra'ayoyin jama'a ke nuna cewa Amurkawa da dama sun nuna rashin gamsuwa da shugabancin Trump, sai dai shugaban na Amurka bai nuna alamun ya sauya ra'ayinsa ba.

    Ya kare manufarsa na sanya haraji kan kayayakin da ake shigowa da su cikin Amurka.

    Ya kuma ce iyakokin Amurka sun samu tsaron da ba a taba ganin irinsa ba kuma zai cigaba da shirinsa na kai samame kan bakin haure da masu aikata miyagun laifuka.

    Yan jamiyyar adawa ta Democrats sun zarge shi da karya da ɗora laifi akan waɗanda basu ji basu gani ba yayinda ta ke azurta kansa da iyalinsa

  10. Bam ya tashi kan hanyar Gusau zuwa Funtuwa

    Gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal

    Asalin hoton, FB/Dauda Lawa

    Wata nakiya da ake jin ‘yan fashin daji ne suka dasa ta tashi da wata motar tirela da ke ɗauke da siminti a kan babbar hanyar Gusau zuwa Funtua a jihar Zamfara a yau Laraba.

    Lamarin da ya haifar da cunkoson ababen hawa na wani ɗan lokaci.

    Lokacin da ya tabbatar wa BBC faruwar lamarin, mai magana da yawun rundunar ƴansandan Najeriya a jihar Zamfara DSP Yazid Abubakar ya ce "muna zargin cewa ƴan bindiga ne suka dasa abin amma muna ci gaba da bincike domin sanin ko mene ne aka dasa."

    DSP Abubakar ya bayyana cewa babu wanda ya rasa rai a sanadiyyar al'amari, sannan kuma jami'an tsaro sun tssefe yankin domin tabbatar da cewa babu sauran wani abin fashewa da aka dasa.

    Fashewar ta faru ne a kauyen Unguwar Mai Chida a karamar hukumar Tsafe daidai lokacin da motar wadda ta taso daga Sokoto zuwa Kaduna, ta bi kan nakiyar. Kodayake dai motar ta yi kaca-kaca babu wanda ya rasa ransa a lamarin.

    A baya-bayan nan, Zamfara, wadda jiha ce da ta daɗe tana fama da matsalar rashin tsaro na ƴan bindiga, na fuskantar hare-hare na ababen fashewa a kan hanya, lamarin da ke barazana ga sufurin al'umma na yau da kullum.

  11. Tinubu ya biya wa ɗalibai 50,000 kuɗin rajistar jarabawar JAMB

    ...

    Asalin hoton, Tinubu/X

    Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ta shirinsa na renewed hope ya tallafa wa ɗalibai dubu hamsin a yankin Kudu maso Gabashin ƙasar ta hanyar biya musu kuɗin rajistar jarabawar shiga jami’a wato JAMB da kuma jarabawar Mock kamar yadda gidan talabijin na gwamnati NTA ya ruwaito

    Rahoton NTA ɗin ya ce an raba tallafin ne ga ɗalibai dubu goma a kowace jiha daga cikin jihohin yankin biyar.

    Matakin na zuwa ne a daidai lokacin da iyalai da dama ke kokawa da tsadar rayuwa, abin da ke hana wasu matasa damar biyan kuɗin rajistar jarabawar shiga manyan makarantu.

    Masu shirya shirin sun ce manufar ita ce rage wa iyaye nauyin biyan kuɗin jarabawar tare da ƙarfafa matasa su ci gaba da neman ilimi.

  12. Atiku ya zargi hannun gwamnatin APC a harin da aka kai kan jagororin ADC a Edo

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, kuma jigo a jamʼiyyar haɗaka ta ADC, Atiku Abubakar ya soki gwamnatin APC bayan wani harin da aka kai wa wasu jagororin ADC, ciki har da Peter Obi a jihar Edo.

    Atiku ya zargi APC da hannu a lamarin kuma ya yi kira ga shugaba Bola Tinubu da "ya kare rayuwar alʼumma a Najeriya ba tare da nuna bambanci ba."

    Ya ce "Najeriya ta shiga wani babi mai haɗari inda ba a iya muzguna wa ƴan adawa kawai aka tsaya ba, yanzu har hari ake kai mana"

    Atiku ya yi kira ga shugaban kasa Bola Tinubu da sauran manyan jami’an tsaro na ƙasa su ɗauki matakan da suka dace domin kare rayukan shugabannin adawa da magoya bayansu ba tare da nuna bambanci ko son zuciya ba.

    Ya ce "tsaron rayuka da dukiyoyin ‘yan siyasa haƙƙi ne na dimokuradiyya.

    Ya ce, wajibi ne a tabbatar da cewa siyasa a kasar na tafiya ne cikin lumana, adalci, da kariya ga rayukan dukkan ‘yan kasa, ba tare da nuna bambanci ba.

  13. Kotu ta ɗage sauraron ƙarar El-Rufai kan tauye masa haƙƙi

    ...

    Asalin hoton, El-Rufai/X

    Babban kotun tarayya da ke Abuja ta ɗage sauraron ƙarar da tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, ya shigar kan tauye masa haƙƙi zuwa 27 ga Fabrairu.

    An ɗage shari’ar ne domin bai wa ɓangaren da ake tuhuma damar shigar da takardunsu na amsa ƙarar.

    A yau ne kuma Kotun ta ɗage shari'ar da ake yi wa El-Rufai zuwa 23 ga watan Afrilun 2026 bayan da aka kasa gabatar da shi a gaban babban kotun.

    Mai ba shi shawara kan harkokin yaɗa labarai, Muyiwa Adekeye ne ya sanar da hakan a wata sanarwar da ya fitar a shafinsa na X.

    Har yanzu daI El-Rufai na tsare a hannun hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta ICPC.

  14. Mutum miliyan 6.5 na fuskantar matsananciyar yunwa a Somaliya - MDD

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadi cewa matsalar yunwa na kara tsananta a Somalia, inda kimanin mutum miliyan 6.5 ke fuskantar matsananciyar ƙarancin abinci, adadi kusan ninki biyu idan aka kwantata da shekarar da ta gabata, a cewar sabon rahoton binciken matsalar abinci.

    Rahoton ya nuna cewa sama da mutum miliyan biyu na cikin matakin gaggawa na yunwa, mataki guda kafin a kai ga yunwar da ake kira bala’i.

    Jami’an agaji sun ce taɓarɓarewar ta samo asali ne daga haɗuwar fari mai tsawo da rikice-rikice da hauhawar farashin abinci, lamarin da ya jefa iyalai masu rauni cikin mawuyacin hali.

    Matsalar yunwan ta ƙara tsananta ne sakamakon rashin ruwan sama a kakar daminar Oktoba zuwa Disamba, wanda ya rage yawan amfanin gona tare da busar da makiyaya.

    Wannan lamarin ya fi shafar manoma talakawa da makiyaya, yayin da rashin tsaro ya katse hanyoyin kasuwanci tare da takaita kai agaji a wasu yankuna.

    Rahoton ya kuma yi gargadin cewa fiye da yara miliyan 1.8 ‘yan ƙasa da shekara biyar na cikin hadarin kamuwa da matsananciyar rashin abinci mai gina jiki a watanni masu zuwa.

    Matsalar tsananin yunwa a Somalia na daga cikin babbar matsalar yankin Ƙahon Afrika inda ƙasashen makwabta kamar Kenya da Ethiopia ke fama da fari da sauyin yanayi da suka bar miliyoyin mutane na bukatar taimako.

  15. Kotu ta ɗage shari’ar direban Anthony Joshua zuwa 17 ga Maris

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Wata kotu a kudu-maso-yammacin Najeriya ta ɗage shari’ar Adeniyi Kayode, direban da ya tuƙa motar ɗan damben duniya, Anthony Joshua da ya yi hatsari a Najeiya a watan Disambar da ya gabata.

    Direban ya bayyana a gaban Kotun Majistare ta Sagamu a jihar Ogun ranar Laraba, tare da lauyan shi, Otunba Olalekan Abiodun.

    Mai shari’a ya ɗage shari’ar zuwa 17 ga Maris ne bayan da sashen gabatar da ƙara ya ce zai karɓi jagorancin shari’ar a madadin jihar.

    Ana tuhumar Kayode da laifuka hudu da suka haɗa da haifar da mutuwa ta hanyar tuƙi cikin gagganci da tukin banza da rashin kulawa da tuki ba tare da kula da dokoki ba, da kuma tukin ba tare da lasisi mai inganci ba.

    An bai wa direban belin naira miliyan biyar kuma an sake shi ne bayan ya cika sharuɗɗan belin.

  16. Kotu ta ɗage shari'ar El-Rufai zuwa watan Afrilu

    ...

    Asalin hoton, El-Rufai/X

    Mai bai wa tsohon gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai shawara kan harkokin yaɗa labarai, Muyiwa Adekeye, ya bayyana cewa kotu ta ɗage shari’ar da ake yi da tsohon gwamnan zuwa ranar 23 ga Afrilu, 2026, bayan da aka kasa gabatar da shi a gaban babban kotun tarayya da ke Abuja.

    Sanarwar da ya fitar ya ce mai gabatar da ƙara ya buƙaci kotu ta ba da wa’adin makonni biyu domin bai wa jami’an DSS damar gabatar da El-Rufai wanda ke hannu hukumar ICPC.

    Sai dai lauyan El-Rufai, Wole Iyamu, ya shaida wa kotu cewa babu wani uzuri da zai hana DSS gabatar da shi tun da yake yana hannun wata hukuma ta gwamnati, yana mai cewa ba sai an nemi ƙarin lokaci ba.

    Daga bisani alƙalin, Mai shari'a Joyce Abdulmalik, ta amince da ɗage shari’ar har zuwa watan Afrilu, wanda a cewar Muyiwa ya zarce buƙatar da lauyoyin nasu suka nema.

    Rahotanni sun nuna cewa El-Rufai yana tsare tun ranar 16 ga Fabrairu, lokacin da ya amsa gayyatar EFCC da kansa, kafin daga bisani ICPC ta karɓe shi a daren 18 ga watan, kuma har yanzu ba a ba da belinsa ba.

    A gefe guda kuma ana sauraron ƙarar da El-Rufai ya shigar kotu kan tauye haƙƙinsa.

  17. Ko za a iya dakatar da Shari'ar Musulunci a Arewacin Najeriya?

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    A ranar Talata, 24 ga watan Fabrairu ne majalisar wakilan Amurka ta miƙa rahoton binciken da ta ce ta yi kan zargin muzguna wa Kiristoci a Najeriya, bayan watanni lamarin na tayar da ƙura.

    Ɗanmajalisar wakilan Amurka, Riley M. Moore ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar, wadda ta ƙunshi cikakken bayanin kan binciken da hanyoyin da suka bi, da abubuwan da suka gano da ma shawarwari.

    Bayan ayyana Najeriya a matsayin ƙasar da ke buƙatar sa ido da Trump ya yi ne, sai ya kafa kwamitin majalisar domin binciken matsalar a ranar 31 ga watan Oktoban 2025, sannan ya buƙaci Moore da shugaban kwamitin kasafin kuɗi na majalisar Amurka Tom Cole su jagoranci kwamitin.

    Sai dai babban abin da ya fi jan hankali shi ne batun soke shari'ar Musulunci da dokar kisa kan ɓatanci, daga cikin matakai aƙalla shida da majalisar ta buƙaci Trump ya ɗauka.

    Tu a baya dai Majalisar Ƙoli ta addinin Musulunci da sauran ƙungiyoyin Musulmi na arewacin Najeriya sun yi kakkausan martani dangane da batun.

    Wannan ne ya sa BBC ta yi nazari kan Shari'ar ta Musulunci a tsarin kundin Mulkin Najeriya da kuma ko akwai yiwuwar cire ta daga kundin.

  18. Ba mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin Najeriya

    ...

    Asalin hoton, Bayo Onaunuga/X

    Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa ba ta taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba ko nuna wariyar addini ba, bayan rahoton bincike kan zargin muzgunawa da kashe Kiristoci da Majalisar Wakilan Amurka ta fitar.

    Gwamnatin ta ce "duk da ƙalubalen tsaro da wasu yankuna ke fuskanta, matsalolin sun samo asali ne daga ta’addanci da fashi da makami, da rikice-rikicen al’umma."

    Ministan yaɗa labarai da wayar da kan jama’a, Mohammed Idris ne ya bayyana hakan a wata sanarwar da ya fitr a ranar Talata, inda ya ce ƙundin tsarin mulkin ƙasa ya tanadi ‘yancin addini da ibada ga kowane dan kasa, kuma gwamnati na nan daram wajen kare waɗannan haƙƙoƙi da tabbatar da adalci ga kowa.

    Ministan ya ƙara da cewa "gwamnati ta ƙarfafa ayyukan haɗin gwiwar jami’an tsaro a yankunan da matsalar ta fi ƙamari, tare da fadada farmakin yaki da ta’addanci da lalata hanyoyin masu garkuwa da mutane, da kuma kama manyan masu aikata laifi."

    Haka kuma gwamnatin Najeriya ta inganta haɗin gwiwar hukumomi domin saurin ɗaukar mataki musamman a yankunan karkara masu rauni in ji sanarwar.

    Sanarwar ta kuma jaddada muhimmancin dangantaka tsakanin Najeriya da Amurka, tana mai cewa ƙasar na maraba da tattaunawa da haɗin kai bisa mutunta juna da mutunta ikon ƙasashe.

    Ta ce gwamnati za ta ci gaba da aiki da abokan hulɗar ƙasa da ƙasa ta hanyoyin diflomasiyya yayin da take mai da hankali kan babban nauyinta na kare rayuka da dukiyoyin dukkan ‘yan kasa.

    A jiya ne ƴan majalisar wakilan Amurka suka gabatar da rahoto ga shugaban Amurka Donald Trump kan binciken da suka kammala game da zargin cin zarafin Kiristoci da musguna musu a Najeriya.

  19. DSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a Edo

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Jami’an hukumar tsaro ta farin kaya DSS sun kama mutum na shida da ake zargi da hannu a kitsa harin da aka kai a cocin Katolik na St. Francis da ke Owo a jihar Edo a shekarar 2022, wanda ya yi sanadiyar mutuwar fiye da masu ibada 40 tare da jikkata wasu da dama kamar yadda gidan talabijin na gwamnati NTA ya ruwaito.

    Tun da farko, hukumar ta riga ta kama mutum 5 da, inda suke fuskantar shari'ar aikata laifukan ta’addanci, yayin da mutum na shida da aka kama na baya-bayan nan, mai suna Sani Yusuf, ya shafe kusan shekara huɗu yana ɓuya kafin a kama shi a wata unguwa mai suna Iguosa da ke ƙaramar hukumar Ovia North Local Government Area a jihar Edo.

    Wata majiyar tsaro ta bayyana cewa Yusuf wani babban kwamanda ne a ƙungiyar ISWAP kuma bayan harin Owo ya tsere zuwa Kano kafin daga bisani ya koma ɓuya a yankin na Edo.

    Rahotanni sun ce ya amsa laifin yana da hannu a harin da aka kai cocin da kuma wasu hare-haren ƙungiyar, ciki har da farmakin da aka kai a barikin sojoji na Suleja a watan Yulin 2022 da kuma sace-sacen mutane a Kaduna da kewaye.

    "Ya kuma amince yana da hannu a harin da aka kai a shinge sojoji na Zuma Rock kusa da Suleja, wanda ya yi sanadin mutuwar sojoji biyar, tare da bayyana cewa ya taɓa aiki a ƙarƙashin wani babban jagoran ƙungiyar mai suna Abu Ikirimah wanda aka kama a 2024." in ji majiyar kamar yadda NTA ta ruwaito.

    Jami’an tsaro sun ce kama Yusuf wani gagarumin ci gaba ne a ƙoƙarin tabbatar da adalci ga waɗanda harin ya rutsa da su, da kuma kara tabbatar da yaki da ta’addanci a fadin Nigeria..

  20. Ƙasashe fiye da 100 sun amince da ƙudurin tsagaita wuta a Ukraine

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaba Zelensky ya miƙa godiyarsa ga ƙasashe fiye da 100 da suka amince da wani ƙuduri a babban taron zauren Majalisar Dinkin Duniya da ya yi kira da tsagaita wuta da kuma samar da dawwamamman zaman lafiya a Ukraine.

    Matakin wanda aka ɗauka a yayin da Rasha ke bikin cika shekaru hudu da mamaye Ukraine ya samu goyon bayan babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres.

    To amma Amurka ta sake ƙauracewa matakin.

    An yi maraba da buƙatar Majalisar na tsagaita wutar, to amma kudurin ya ƙunshi wasu kalamai waɗanda za su iya kawar da ƙoƙarin da ake na kawo ƙarshen yaƙin.