Champions League: Benfica za ta ƙara fafatawa da Real Madrid a wasan cike gurbi

Asalin hoton, Getty Images
Benfica za ta sake karawa da Real Madrid a wasannin cike gurbi na gasar cin kofin zakarun nahiyar Turai, mako uku bayan karawar da suka yi a wasannin cikin rukuni.
A ranar Laraba, mai tsaron ragar ƙungiyar Benfica Anatoliy Trubin ya zura ƙwallon ta huɗu a ragar Madrid cikin minti na 98, lamarin da ya sa ƙungiyar, wadda Jose Mourinho ke horaswa ta yi nasara kan Real da ci 4-2.
Ga cikakken jadawalin karawar:
- Bodo/Glimt v Inter Milan
- Benfica v Real Madrid
- Monaco v Paris St-Germain
- Qarabag v Newcastle
- Galatasaray v Juventus
- Club Brugge v Atletico Madrid
- Borussia Dortmund v Atalanta
- Olympiacos v Bayer Leverkusen



















