An fitar da jadawalin zagayen ƴan 16 na Gasar Champions League
Asalin hoton, Getty Images
An kammala haɗa ƙungiyoyin da za su kece raini a zakayen ƴan 16 na Gasar Zakarun Nahiyar Turai ta Uefa Champions League, inda mai kare kambi PSG za ta kara da Chelsea.
Ga cikakken jadawalin karawar zagayen na ƴan 16:
Paris St-Germain v Chelsea
Galatasaray v Liverpool
Real Madrid v Manchester City
Atalanta v Bayern Munich
Newcastle United v Barcelona
Atletico Madrid v Tottenham
Bodo/Glimt v Sporting CP
Bayer Leverkusen v Arsenal
Lindblad zai zama matashin da zai yi tsere a Formula 1, Tseren motocin Formula 1
Asalin hoton, Getty Images
Gasar Formula
One da za a fara ta kakar bana a farkon makon watan Maris a Australian
Grand Prix, za ta zama a
karon farko da matashin direba, Arvid Lindblad mai shekara 18 zai fafata.
Lindblad zai
zama matashin direba mafi karancin shekaru daga Birtaniya da zai shiga wasan Formula
One.
Ana kallon batun
a matsayin sabon babi ga matasan matuka daga Turai, zai jawo hankalin masoya wasanni daga
Birtaniya, Indiya da Sweden.
Australian
Grand Prix da za a yi a birnin Melbourne za ta zama labulen bude sabuwar kakar bana daga watan
gobe,
An samu sauran ƙungiyoyin da suka kai zagaye na biyu a Champions League, Champions League
Asalin hoton, Getty Images
An samu sauran kungiya huɗun da za su ci gaba da zagayen ƴan 16 a Champions League
da ya hada da Atalanta da Galatasaray da Paris St Germain da kuma Real Marid a wasannin da suka buga ranar Laraba.
Kungiyar
Spaniya ta doke Benfica 2-1, kenan gida waje 3-1.
Ranar Juma’a
za a raba jadawalin zagaye na biyu a gasar cin kofin Zakarun Turan.
Ana sa ran
za a iya haɗa Atalanta da ko dai Arsenal ko Bayern Munich – Watakila a haɗa
Galatasar da ko dai Liverpool ko kuma Tottenham –
Paris St
Germain mai rike da kofin bara za ta iya fuskantar ko dai Barcelona ko Chelsea,
yayin da ake sa ran Real Madrid a haɗa ta da ko dai Manchester City ko kuma
Sporting.
Haka kuma
Atalanta ta ceci gasar Seri A da yin abin kunya, bayan da ta zama tilo daga
Italiya da ta kai zagaye na biyu a Champions League.
Rabon da ace
an buga zagaye na biyu a wasannin ba tare da ƙungiya daga gasar Serie A ba tun
bayan shekara 40.
Bolivia na fatan samun tsaro a Mexico a wasan cike gurbi, Mexico
''Mexico za ta gudanar da gasar kofin duniya da bayar da tsaro'', Fifa
Asalin hoton, Getty Images
Shugaban
FIFA, Gianni Infantino, ya ce yana da tabbacin Mexico za ta iya karɓar bakuncin
wasannin gasar cin kofin duniya cikin tsaro da kwanciyar hankali, duk da ɓarkewar tashin hankali kusa da wasu biranen da za su shirya wasannin bana da
za a fara daga watan Yuni zuwa Yuli.
Wani gungun
masu safarar miyagun kwayoyi ne ya tayar da rikici a jihar Jalisco, bayan kashe
daya daga cikin shugabansu, Nemesio Oseguera da ake kira El Mencho a makon da ya gabata.
Babban
birnin jihar, Guadalajara, na daga cikin wuraren da zai karɓi bakuncin wasa
hudu na gasar,
Mexico za ta
shirya wasa 13 da za a fafatawar birnin Guadalajara
da Mexico City.
Ronaldo ya zama ɗaya daga cikin mamallakan Almeria, Almeria
Asalin hoton, Getty Images
Cristiano Ronaldo ya zama ɗaya daga cikin mamallakn ƙungiyar ƙwallon kafa ta Sifaniya, UD Almeria, bayan da ya sayi kaso 25 cikin 100 na hannun jarinta.
Ɗan wasan mai shekaru 41, wanda ke taka leda a Al-Nassr, ya sayi wannan kaso ne ta hannun sabon kamfaninsa mai suna CR7 Sports Investments.
A halin yanzu Almeria na karkashin mallakar wani kamfanin zuba jari daga Saudiyya da Mohammed Al-Khereiji ke jagoranta.
Ronaldo ya shafe shekaru tara a Sifaniya tare da Real Madrid, inda ya lashe La Liga biyu da ɗaukar Champions League hudu kafin ya koma Juventus a 2018.
Tun 2022 yake taka leda a gasar Saudiyya tare da Al-Nassr, kuma har yanzu shi ne ɗan wasan da ake biya albashi mafi tsoka a tarihin kwallon kafa, inda ake biyansa fam miliyan 177 a shekara.
An kafa Almeria a 1989, kuma a yanzu tana matsayi na uku a gasar Segunda, maki biyu kacal a bayan mai jan ragamar tebur, Real Racing Club, yayin da wasa 15 suka rage a kammala kakar bana.
An ci tarar Chelsea da West Ham kan hatsaniya tsakanin ƴanwasa, Premier League
Asalin hoton, Getty Images
An ci tarar Chelsea fam 325,000 da kuma West Ham fam 300,000, sakamakon wani rikici da ya barke tsakanin ƴan wasa karawar da suka yi a Premier League a watan Janairu a Stamford Bridge.
Lamarin ya faru ne a minti 95, inda ɗan wasan Chelsea, Joao Pedro ya kalubalanci Adama Traore na West Ham, saboda ture Marc Cucurella da ya yi.
Bayan da aka duba VAR, sai alkalin wasa Anthony Taylor ya bai wa Jean-Clair Todibo jan kati kai tsaye saboda shake wuyan Joao Pedro da ya yi.
Hukumar kwallon kafa ta Ingila ta bayyana cewa Chelsea da West Ham sun kasa tsawatar wa a lokacin yamutsin.
Tun farko dukkan ƙungiyoyin sun amince da tuhumar da aka yi musu.
Dukkan kungiyoyin biyu sun amince da laifin da ake tuhumarsu da shi.
Ƙungiyoyin Italiya na daf da yin abin kunya a Champions League, Champions League
Asalin hoton, EPA
Ƙwallon kafar Italiya na cikin wani yanayi mai matukar muni a gasar Champions League, inda akwai yiwuwar babu ko ɗaya daga Serie A da za ta kai zagayen na biyu wato na ƴan 16 a bana.
Tun bayan dawo da tsarin zagayen ƴan 16 a kakar 2003-04, a ko da yaushe akwai aƙalla wakili guda daga Italiya.
A lokuta 12 cikin shekaru 22 da suka wuce ma har ƙungiya uku ne suka kai wa wannan mataki.
Ba a taɓa samun kakar da babu ko ɗaya ba daga mai buga Serie A tun 1987-88, lokacin da Napoli ta fita a zagayen farko na European Cup a hannun Real Madrid.
A kakar bana Inter Milan ta yi ban kwana da gasar, sakamakon da Bodo/Glimt ta yi waje da ita, wasan da ya bayar da mamaki.
Inter ta fara rashin nasara 3-1 a wasan farko, sannan aka doke ta 2-1 a San Siro, kenan an yi mata 5-2 gida waje kenan.
Wannan ne karo na farko da Inter ta fita daga Champions League a hannun ƙungiya ba daga manyan lig-lig biyar na Turai ba, wato Ingila ko Sifaniya ko Jamus ko Italiya ko kuma ta Faransa.
Yanzu dai hankali ya koma kan Juventus, wadda aka ci 5-2 a wasan farko a Galatasaray - za ta karɓi bakuncin wasa na biyu ranar Laraba.
Ita kuwa Atalanta 2-0 aka doke ta a karawar farko a gidan Borussia Dortmund da za ta karɓi bakuncin karawa ta biyu.
Idan ƙungiyoyin biyu suka kasa kai wa zagaye na biyu, zai zama tarihi mafi muni da ba wata daga Serie A a zagaye na biyu a Champions League cikin shekara 40.
Wannan lamarin zai rage martabar Serie A a Turai da hasarar samun kuɗin shiga da karin matsin lamba ga kociyoyi da shugabanni, sannan za a iya rage ƙungiyoyin da za su shiga babbar gasar tamaula ta Champions League a baɗi.
, Daga Jaridu
Asalin hoton, Getty Images
Borussia Dortmund za ta buƙaci a biya ta Euro miliyan 70 kan ɗanwasan tsakiyar Jamus mai shekara 25 da Manchester United da Chelsea ke zawarci, Felix Nmecha. (Bild - in German)
Liverpool da Manchester United da kuma Tottenham na bibiyar ɗanwasan RB Leipzig da Ivory Coast, Yan Diomande amma cinikin zai fuskanci tangarɗa saboda rashin tabbacin ko wanene wakilin ɗanwasan mai shekara 19. (Telegraph - subscription required)
Manchester City da Liverpool da kuma Real Madrid na zawarcin ɗanwasan bayan Juventus mai shekara 26 kuma ɗan Italiya, Andrea Cambiaso. (Caughtoffside)
Barcelona ta shirya tattauna yadda Manchester United za ta sayar mata da ɗanwasan gaban Ingila Marcus Rashford amma tana neman a sake lale a cinikin ɗanwasan mai shekara 28 (Sport, via Mirror)
Za a samar da tsaro lokacin kofin duniya - Sheinbaum, Gasar kofin duniya 2026
Asalin hoton, Getty Images
Shugabar
Mexico, Claudia Sheinbaum ta ce akwai tabbacin samar da tsaro a lokacin gudanar
da gasar Cin Kofin Duniya a bana a kasar.
Bayan kama
da mutuwar shugaban ƙungiyar safarar miyagun ƙwayoyi, Nemesio Oseguera Cervantes, wanda ake kira “El Mencho da hakan ya haifar da tarzoma musamman mafi
girma a jihar Jalisco.
Ana sa ran
magoya baya da yawa za su ziyarci birnin Mexico da Monterrey da Guadalajara — Sheinbaum ta ce ba wani haɗari za a yi wasannin
lafiya lau.
Mexico na
shirin karɓar bakuncin wasa 13 cikin 104 da za a yi a haɗaka har da Amurka da
Canada.
Huɗu daga
cikinsu za a yi a birnin Guadalajara. Haka kuma kasar za ta karɓi bakuncin wasu
wasannin gwaji kafin bikin buɗe babbar gasar tamaula ta Afirka ranar 11 ga
watan Yuni.
Za a kammala wasannin cike gurbi a Champions League ranar Laraba, Champions League
Asalin hoton, Getty Images
Za a kammala wasa na bibiyu a zagayen cike gurbin ci
gaba da karawa ta biyu a Champions League da za a yi fafatawa huɗu ranar Laraba.
Wasannin da za a buga ranar Laraba:
Atalanta da Borussia
Atalanta da Borussia Dortmund
Juventus da Galatasaray
Paris St
Germain da Monaco
Sakamakon wasannin farko a makon jiya:
Borussia Dortmund 2 – 0 Atalanta
Benfica 0 – 1 Real Madrid
Galatasaray 5 – 2 Juventus
Monaco 2 – 3 PSG
An fara samun waɗanda suka kai zagaye na biyu a Champions League, Champions League
Asalin hoton, Getty Images
An fara samu huɗun da suka kai zagaye na biyu a gasar
ta zakarun Turai da ya haɗa da Newcastle da Bodo da Atletico Madrid da kuma
Bayern Leverkusen da za a raba jadawali ranar Juma’a
Ana kuma sa ran watakila Newcastle ta fuskanci Barcelona ko
Chelsea, ana sa ran Bodo za ta kara da ko dai Manchester City ko Sporting, Atletico
kuwa na iya fafatawa da Liverpool ko kuma Tottenham, sai Bayern Leverkusen da za
ta ɓarje gumi da ko dai Arsenal ko kuma Bayern Munich.
Za kuma a fara wasannin farko daga 10 zuwa 11 ga watan
Maris, a buga karawa ta biyu mako daya tsakani.
Mane na tsaka mai wuya kan wa zai wakilta tsakanin Portugal da Ingila, Premier League
Asalin hoton, Getty Images
Ɗan wasan Wolverhampton,
Mateus Mane na tsakiyar takaddama tsakanin Ingila da Portugal kan wadda zai
wakilta a fannin taka leda.
Matashin mai
shekara 18 na cikin jerin ƴan wasan da kocin Portugal Roberto Martinez ke son gayyata,
bayan da ya fara haskakawa a gasar Premier League.
An haifi
Mane a birnin Barreiro a Portugal, amma ya yi wa tawagar Ingila ƴan kasa da
shekaru 18 tamaula tun daga 2024.
Mane, wanda
ya koma Ingila yana da shekaru takwas, na iya karbɓr goron gayyata daga tawagar
Portugal ta ƴan kasa da shekara 21.
Raducanu ta ce ba ta gaggawar ɗaukar sabon koci, Tennis
Emma
Raducanu ta ce ba ta cikin gaggawar neman sabon koci, yayin da tsohuwar gwarzuwar US Open ke son komawa salon wasa mai cike da kai hari.
‘Yar wasan
Birtaniya ta canza kociyoyi da dama a cikin kankanin lokaci, inda Francisco
Roig ya zama na baya-bayan nan da ya bar aikin, bayan wata shida yana tare
da ita.
Raducanu mai
shekaru 23 ta ce tana son komawa kan ganiya, da salon kai hare-hare masu zafi a wasanninta.
, Daga Jaridu
Asalin hoton, Getty Images
Rashford ya zaɓi zama a Barcelona a madadin komawa Manchester United - duk da dai ya nemi a bashi damar riƙa fara wasa da shi a duk lokacin da ƙungiyar ke da wasa (Marca - in Spanish)
Manchester United ta mayar da hankali kan zawarcin ɗanwasan Napoli da Scotland Scott McTominay, mai shekara 29 (Teamtalk)
Barcelona ce kan gaba a jerin ƙungiyoyin da ke zawarcin ɗanwasan Bournemouth da Argentina, Marcos Senesi, mai shekara 28.(Football Insider)
Arsenal na shirin gabatar da tayin ɗanwasan bayan Ecuador mai shekara 24, Piero Hincapie daga Bayer Leverkusen (Teamtalk)
Man United ta sanar da cin riba, amma kuɗin bashi ya karu, Manchester United
Asalin hoton, Getty Images
Shugaban gudanarwa na Manchester United, Omar Berrada, ya ce sauye-sauyen da ƙungiyar ke yi din ke yi sun fara haifar da sakamako mai kyau ta fuskar kuɗi — duk da cewa bashi na kara kusantar fam biliyan 1.3.
Ƙungiyar ta sanar da samun ribaar fam miliyan 32.6 cikin wata shida zuwa 31 ga Disamba 2025.
Wannan ya bambanta matuka da asarar da aka samu a daidai wannan lokaci a shekarar da ta gabata, wadda ta kai hasarar fam miliyan 3.9 asara.
Wannan na nuna cewa an samu ci gaba a harkokin kasuwanci da tallace-tallace da karin kuɗin shiga daga bangaren talla da kasuwanci.
Duk da haka, an kuma kara cire fam miliyan 25 daga asusun bashin gaggawa, wanda yanzu ya kai fam miliyan 295.7.
An biya £13.9m a matsayin kudin ruwa, wanda ya ragu sosai idan aka kwatanta da fam miliyan 37.6 a shekarar da ta gabata — alamar cewa an ɗan rage tarin bashin a ɓangare guda.
A watan Agustan 2025, masani kan harkokin kuɗin kwallon kafa, Swiss Ramble ya sanya Manchester United a kasa da Everton da kuma Tottenham a jerin ƙungiyoyin da ke da yawan bashi.
Sai dai waɗannan ƙungiyoyi biyu sun karɓi bashi ne domin gina sababbin filayen wasa.
, Daga Jaridu
Asalin hoton, Getty Images
Manchester United na tunanin sake sayen dan wasan tsakiya na Scotland Scott McTominay kan Yuro miliyan 80 (£70m) a lokacin bazara, inda Napoli ke shirin karbar kudin dan wasan mai shekaru 29 shekaru biyu kacal bayan ya koma kungiyar ta Italiya daga Old Trafford. (Fichajes)
Real Madrid na sa ido sosai kan dan wasan tsakiya na Tottenham Micky van de Ven mai shekaru 24, yayin da ake ganin babu alamar cewa dan wasan Netherlands zai rabata hannu kan wata sabuwar yarjejeniya da kungiyar ta Premier League. (Teamtalk)
Brighton na fatan kammala yarjejeniyar sayen dan wasan gefe na Cologne mai shekaru 19 Said El Mala ta hanyar sayen dan uwansa, dan wasan gaba mai shekaru 20 Malek. (Times)
Manchester United na duba yiwuwar daukar ɗan wasan tsakiya na Ivory Coast na Nottingham Forest, Ibrahim Sangare, mai shekaru 28, a ƙoƙarinta na neman wanda zai maye gurbin ɗan wasan Brazil, Casemiro, mai shekaru 34. (GiveMeSport)
Za a buga gasar kofin duniya a Mexico duk da kalubalen tsaro - Sheinbaum, Gasar kofin duniya
Asalin hoton, Getty Images
Shugabar Mexico, Claudia Sheinbaum ta ce akwai tabbacin samar da tsaro a lokacin gudanar da gasar Cin Kofin Duniya a bana a kasar, bayan kama da mutuwar shugaban kungiyar safarar miyagun kwayoyi da ake ta nema ruwa a jallo da ya haifar da tarzoma da kafa shinge da kone-kone da ta jefa fargabar tsaro, musamman a jihar Jalisco.
Da aka tambaye ta ko gasar kwallon kafa — wadda ake sa ran magoya baya da yawa za su ziyarci birnin Mexico da Monterrey da Guadalajara — za ta iya zama barazana ga baki, Sheinbaum sai ta ce “babu wani hadari.”
Ta kara da cewa al’amura na komawa yadda suke bayan mambobin kungiyar safarar miyagun kwayoyi sun kai jerin hare-hare a ranar Lahadi, bayan wani sumame da aka kai domin kama shugaban Nemesio Oseguera, wanda aka fi sani da “El Mencho,” wanda ya mutu a sakamakon arangamar.
Shugabar ta ce an sake kafa wasu shingen a wasu hanyoyi da dare, amma jami’an tsaro na aiki domin dawo da zaman lafiya.
Mexico na shirin karɓar bakuncin wasa 13 cikin 104 da za a yi a gasar Cin Kofin Duniya.
Hudu daga cikinsu za a yi a birnin Guadalajara. Haka kuma kasar za ta karɓi bakuncin wasu wasannin gwaji kafin bikin buɗe babbar gasar tamaula ta Afirka ranar 11 ga watan Yuni.
Loftus-Cheek zai yi jinyar kusan mako takwas in ji Milan, Serie A
Asalin hoton, Getty Images
Watakila ɗan wasan AC Milan, Ruben Loftus-Cheek zai yi jinya kusan mako takwas bayan da aka yi masa tiyata sakamakon karya mukamuki bayan karo da ya yi da mai tsaron bayan Parma, Edoardo Corvi ranar Lahadi.
An fitar da ɗan wasan tawagar Ingila daga filin a kan gadon ɗaukar marasa lafiya bayan da ya ji raunin a kusan minti na 10 a gasar Serie A da suka buga a San Siro.
Milan, wadda ta sha kashi 1-0 a wasan, tana matsayi na biyu a teburin gasar, maki 10 tsakani da Inter Milan mai jagoranci, za kuma ta ziyarci Cremonese ranar Lahadi mai zuwa.
, Daga Jaridu
Asalin hoton, Getty Images
Casemiro zai sami damar komawa Amurka lokacin da kwantaraginsa a Manchester United zai kare, inda ɗan wasan tsakiyar zai iya komawa wata babbar kungiya a kasar ta Amurka (Telegraph)
Liverpool na iya duba bukatar yin musaya da Real Madrid, da za ta kai ta ga daukar ɗan wasan gefen Brazil, Rodrygo, mai shekaru 25, yayin da ita kuma za ta ba wa Madrid din ɗan wasan tsakiya na Hungary, Dominik Szoboszlai, mai shekaru 25. (Fichajes)
Kocin Chelsea, Liam Rosenior, ba ya son barin ɗan wasan gaba na Ingila mai shekara 23, Liam Delap ya tafi a wannan bazarar, a dai-dai lokacin da Everton ke sha'awarsa. (Football Insider)
Crystal Palace za ta ba wa kocin Austrian Oliver Glasner damar ci gaba da jagorantar ƙungiyar har zuwa ƙarshen kakar wasa. (Football Insider)