Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza

  1. Tinubu ya gana da shugabannin Tijjaniya na duniya

    d

    Asalin hoton, Presidency

    Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya ce akwai buƙatar haɗin kai tsakanin Shugabannin addini da na siyasa wajen ciyar da ƙasa gaba.

    Tinubu ya bayyana haka ne lokacin da yake karɓar baƙuncin shugabannin Ɗariƙar Tijjaniya na duniya wanda Khalifa Muhammad Mahe Niass, ya jagoranta.

    Tinubu ya ce gwamnatinsa a shirye take wajen ciyar da harkokin addini ga wadanda suke taimakawa wajen gida ƙasa.

    Ya ce burinsa " mayar da Najeriya ƙasar da za ta iya ciyar da kanta ta hanyar noma, har ma ta samu rarar da za ta iya fitar da ita kasashen ketare.

    Da yake nasa jawabin a madadin wakilcin masu ziyarar Khalifa Muhammad Mahe Niass ya yaba wa Gwamnatin Tinubu yajen ƙoƙarin da take yi na ganin an samu zaman lafiya mai ɗorewa a Najeriya.

    Yayin ziyarar tawagar ta yi addu'ar samun zaman lafiya da ci gaba mai ɗorewa a Najeriya da nahiyar Afrika da duniya baki ɗaya.

  2. An ga Sarki Abdallah na Jordan cikin masu aikin agaji a Gaza

    Gidan talabijin din ƙasar Jordan ya fitar da wani faifan bidiyo da ke nuna Sarki Abdallah ya na taimakawa wajen jigilar kayan agaji zuwa Gaza.

    Bidiyon ya nuna sarkin sanye da kayan sojoji a cikin wani jirgin saman sojin Jordan ya na watsa kayayyakin jinya harabar asibitoci a yankin Falasdin.

    Rahotanni sun ce wannan shi ne karo na goma sha daya da sojojin saman'kasar ta Jordan suka kai irin wannan agaji tun bayan fara yakin Gaza.

  3. Cikin Hotuna: Tinubu ya gana da Sheik Dahiru Bauchi

    Presidency

    Asalin hoton, Presidency

    Presidency

    Asalin hoton, Presidency

    Presidency

    Asalin hoton, Presidency

    Presidency

    Asalin hoton, Presidency

  4. UNICEF: Mun raba sabbin littattafai miliyan 7.5 ga ɗaliban Afghanistan

    H

    Asalin hoton, UNICEF

    Asusun Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya ya ce sabbin littattafai miliyan 7.5 ga ɗalibai a Afghanistan.

    A wani labarai da ya fitar, sashen UNICEF da ke Afghanistan ya ce ya raba littattafai da kayan karatu ga ɗaliban firaimare a ƙasar a bara.

    Yara mata na karatu zuwa mataki na shida, wanda nan ne ƙarshen karatunsu a Afghanistan, saboda Taliban ta haramta musu ci gaba da karatu.

  5. NATO ta mayarwa da Donald Trump martani

    A

    Asalin hoton, Getty Images

    Sakataren NATO Jens Stoltenberg ya mayar da kakkausan martani ga tsohon shugaban Amurka Donald Trump, kan kalamansa da ya yi na cewa zai taimakawa Rasha ta kai wa mamba NATO da bai biya kuɗi ba hari.

    Ya ce " Duk wani butu da ke cewa mambobinmu ba za su iya kare kansu ba, na raina ƙarfin sojinmu ne, ciki har da Amurka, idan ya yi tsammanin Amurka ko dakarun Turai za ta jefa kanta cikin haɗari."

    Fadar White House ta zargi Donald Trump da furta kalamai masu tayar hankali akan batun da ya shafi rashin ba da kariya ga mambobin kungiyar tsaro ta NATO daga duk wani hari na Rasha .

    Kakakin fadar ta White house Andrew Bates ya ce kalaman Mista Trump na barazana ga tsaron Amurka da ma duniya baki daya.

  6. Biyu daga fursunonin Taliban da ke Guantanamo za su koma Afghanistan

    A

    Ma'aikatar harkokin wajen Taliban ta ce biyu daga cikin fursinoninta da suka shafe shakara 14 a tsare a Guantanamo za su koma gida Afghanistan.

    Abdul Matin Qane kakakin ma'aikatar wajen Taliban, ya ce ɗaya daga cikinsu shi ne "Abdul Zahir Saber" daga lardin Logar wanda kakakin ya ce sojin Amurka ne suka kama shi a ranar 10 ga watan Mayun 2002 bayan kwashe watanni hudu a gidan yari.

    An mayar da Bagram zuwa Guantanamo sannan a 16 ga watan Janairu aka mayar da shi Oman.

    Mutum na biyu shi ne "Abdul Kareem" daga lardin Khost, wanda aka kama shi a Pakistan a ranar 14 ga watan Agustan 2002 watanni kaɗan a 2003 aka mikawa Amurka shi ta kai shi Guantanamo.

  7. Motocin agaji 115 sun isa Gaza daga Masar

    A

    Motocin agaji 115 dauke da kayan tallafi suka shiga zirin Gaza ta mashigar Rafah da ke arewacin Sinai a Masar.

    Wani jami'i daga tashar ruwan ya ce a ranar Lahadi motoci 110 na kayan agaji ne suka shiga yayin da masu ɗauke da man fetur biyar su ka shiga zirin na Gaza.

    A gefe guda kuma ya nuna wasu Falasɗinawa 65 d suka raunata ana duba lafiyar su a Masar.

    Waɗannan ƙari ne kan mutum 250 da ke da takardar shaidar 'yan zama ƙasa biyu da suka fice daga Gaza, akwai kuma 132 da suke da fasfo ɗin Masar su ma sun fice.

    Kungiyoyin agaji sun ce akwai buƙatar akai wadannan kayan cikin gaggawa domin buƙatarsu ba tare da wani shadi ba.

  8. Afcon 2023: Karon battar ƙarfe a wasan ƙarshe tsakanin Najeriya da Ivory Coast

    .

    Bayan yawan ƙwallaye da aka zura a raga, a yau za a kawo ƙarshen gasar da aka ƙwashe kusan wata guda ana gudanarwa.

    Inda za a ɓarje gumi tsakanin Najeriya da mai masaukin baƙin gasar, Ivory Coast, domi samun kambin Zakarun Afirka.

    Tawagar Super Eagles ta Najeriya na fatan ɗaukar kofin a karo na huɗu a fafatawar da za a yi a birnin Abidjan, yayin da a nata ɓangare Ivory Coast ke fatan lashe kofin a karo na uku bayan na 1992 da 2015.

    Kungiyoyin za su yi gumurzu ne a karo na biyu, a cikin wannan gasa da Ivory Coast ke karɓar bakunci, kwana 24 bayan Ivory Coast ta sha kashi a hannun Najeriya a wasan cikin rukuni.

    Tawagar Ivory Coast ita ce ƙungiyar da ke karɓar baƙuncin gasar ta farko da ta taɓa kai wa wasan ƙashe a gasar, tun bayan Masar a 2006, yayin da biyar daga cikin masu masaukin baki shida da suka kai wasan ƙarshe suka lashe kofin, in ban da Najeriya a shekarar 2000.

    Ba a dai taɓa doke Najeriya ba, tun fara gasar, kuma a halin yanzu ita ce babbar kungiya a cikin tawagogin biyu da suka kai wasan ƙarshe.

    Najeriya ce ƙasa ta shida a iya murza leda a Afirka, kuma ta 42 a duniya, yayin da Ivory Coast ke matsayi na 8 a Afirka kuma ta 49 a duniya.

    Najeriya - wadda ke fatan lashe kofinta na farko tun shekarar 2013 - ta kai wasan na ƙarshe ba tare da shiga wani matsi ba wasanninta, bayan da ta samu maki bakwai a matakin rukuni, sannan ta doke Kamaru da Angola da kuma Afirka ta Kudu a zagaye sili ɗaya ƙwale.

    Ita kuwa ivory Coast bayan kashin da ta sha a hannun Najeriya a matakin rukuni, ta sake shan kaye a hannun Equitorial Guinea da ci hudu da nema, sannan ta tsallake rijiya da baya a matsayin ta uku mafi kyau.

    A lokacin da suka shiga zagaye na 16, sun sake fitowa ƙarfi, inda suka fitar da Senegal mai rikƙe da kofin gasar sannan suka doke Mali, kafin su doke Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango a wasan kusa da na ƙarshe.

    Bayan ƙoƙari da mamakin da ƙungiyar ta bayar a gasar, a yanzu fatanta shi ne lashe kofin a wasan da za a buga gaban 'yan kallo kusan 60,000 a birnin Abidjan.

    Tuni dai shirye-shirye suka yi nisa a wasan da za a buga da misalin ƙarfe 8:00 na dare agogon ƙasar.

  9. Netanyahu ya sake jaddada ci gaba da kai hare-hare zuwa Rafah

    ..

    Asalin hoton, AFP

    Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya jaddada ƙudurin sojojin ƙasar na ci gaba da kai hare-hare zuwa birnin Rafah, duk kuwa da matsin lambar ƙasashen duniya.

    A wata hira da ya yi da gidan talbijin na ABC. mista Netanyahu ya ce fiye da Falasɗinawa fararen hula miliyan guda da suka fice daga Rafah da sauran yankunan Gaza, za su samu kariya.

    Da aka tambaye shi ko ina wadanna fararen hula za su koma? Sai ya ce Isra'ila na ''aiki kan haka''

    Wannan sanarwa na zuwa ne a daidai lokacin da Majalisar Dinkin Duniya ta ayyana cewa Falasɗinawa ba su da wata sauran kariya a Rafah.

    Ƙungiyar Tarayar Turai da Amurka da Birtaniya sun bayyana damuwarsu kan ci gaba da hare-haren.

    A nata ɓangare, ƙungiyar Hamas ta ce hare-hare ta sama da Isra'ila ta kai kwanaki huɗu da suka gabata sun kashe Isra'ilawa biyu da ƙungiyar garkuwa da su tare da jikkata takwas daga ciki.

  10. Shugabar ƙasar Hungary ta ajiye muƙaminta

    .

    Asalin hoton, Reuters

    Shugabar ƙasar HungaryKatalin Novak ta ajye aikinta saboda maganganun da suka taso bayan afuwar da ta yi wa wani mutum da aka samu da laifin alaƙa da zarafi ta hanyar lalata.

    A makon da ya gabata ne shugabar ƙasar ta yi wa mutumin da aka ɗaure a gidan ayarin ƙasar afuwa, bayan kotu ta same da laifin tilasta wa ƙananan janye iƙirarin cin zarafi ta hanyar lalata da suke yi wa wani daraktan gidan kula da ƙananan yara.

    Matakin afuwar ya janyo tarin zanga-zanga neman ta sauka daga muƙaminta.

    Misis Novak ta nemi afuwar 'yan ƙasar tana mai cewa ta yi ''kuskure'' wajen yin afuwar.

    Tsohuwar ministan shari'a Judit Varga - wadda ta sanya hannu kan takardar amincewa da afuwar - ita ta ajiye aikinta na jagorar yaƙin neman zaɓen jam'iyyar firaministan ƙasar Viktor Orban.

    Ce-ce-ku-cen da ya janyo ta ajiye muƙamin nata na zuwa ne bayan da a makon da ya gabata kafar yaɗa labaran ƙasar ta wallafa sunayen mutum 25 da Misis Novak ta yi musu afuwa a watan Afrilun shekarar da ta gabata, a wani ɓangare na ziyarar Fafaroma Fransis zuwa ƙasar.

    A cikin jerin sunayen ne aka ga sunan mataimakin daraktan gidan kula da ƙananan yara, da aka ɗaure shekara uku a gidan yari bayan samunsa da laifin tilasta wa ƙananan yara janye iƙirarin cewa daraktan gidan ya ci zarafinsu.

  11. Amsoshin Takardunku

    Bayanan sautiLatsa hoton da ke sama domin sauraron shirin
  12. An kashe sojojin UAE da na Bahrain a Somaliya

    .

    Asalin hoton, Getty Images

    An kashe sojojin Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa uku da na Bahrain ɗaya a wani sansanin soji da ke Mogadishu, babban birnin Somaliya.

    Cikin wata sanarwa da ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawar ta fitar, ta ce dakarun huɗu na cikin ayyukansu ne horas da sojojin Somaliya lokacin da aka kawo musu harin.

    Kafar yaɗa labaran intanet ta Garowe a ƙasar ta ce maharin ya samu shiga cikin sansanin, inda ya kashe masu horaswar, tare da jikkata wasu mutum biyu.

    Shugaban ƙasar Somaliya Hassan Sheikhya yi Allah wadai da harin da ya bayyana da ''harin ta'addanci na rashin imani''.

    Ya yaba da sadaukarwar da sojojin suka yi kan aikinsu na horas da jami'an Somaliya da nufin ƙarfafa su don ceto ƙasar daga barazanar ta'addanci.

    Gwamnatin Somaliya ta ƙarfafa faɗa da 'yan ta'adda a faɗin ƙasar, inda ta sha alwashin kawo ƙarshen ayyukan ƙungiyar Al Shabaab zuwa ƙarshen shekarar da muke ciki.

  13. Gwaji ya tabbatar da shugaban Laberiya ba ya ta'ammali da ƙwayoyi

    .

    Asalin hoton, EPA

    Gwajin da ka yi wa shugaban Laberiya Joseph Boakai ya nuna cewa ba ya ta'ammali da miyagun ƙwayoyi.

    Cikin makon da ya gabata ne shugaban ya yi gwajin da ya alƙawarta yi a lokacin da yake jawabi ga 'yan majalisar ƙasar ranar 29 ga watan Janairu, mako guda bayan rantsar da shi.

    Mista Boakai ya yi gwajin ne tare da mataimakinsa, Jeremiah Kpan Koung da sauran jami'an gwamnatinsa, ƙarƙashin kulawar ma'aikatar lafiyar ƙasar.

    Shugaban ƙasar ya ce : "Matakin na daga cikin alƙawuran da na ɗauka na ƙoƙarin kawar da ta'ammali da miyagun ƙwayoyi a faɗin Laberiya''.

    A lokacin da yake jawabi ga majalisar dokokin ƙasar, mista Boakai ya ayyana dokar ta ɓaci kan shan miyagun ƙwayoyi a ƙasar.

    Shugaban ya kuma buƙaci duka jami'an gwamnatinsa da su gudanar da gwajin ta'ammali da miyagun ƙwayoyin.

  14. An kammala bikin gargajiya na 'Rigata' a Yauri

    .

    Asalin hoton, Abba Villa

    An kammala bikin al'adun gargajiya daake yi wa lakabi an Rigata da aka saba gudanarwar a kowace shekera a masarautar Yauri da ke jihar Kebbi.

    .

    Asalin hoton, Abba Villa

    Kwanaki uku aka dauka ana gudanar da bikin, wanda ake nuna amfanin gona da ake nomawa a yanki Yauri da irin wasannin gargajiyar al'ummar yankin.

    .

    Asalin hoton, Abba Villa

    Bikin ya samu haralartar gwamnan jihar Alh. Nasir Idris da sarki Yauri, Dr Muhammad Zayyanu Abdullahi (C.O.N) da sauran manyan mutane daga ciki daga wajen jihar.

    A wannan bikin karon farko an kamo dorina da ranta, inda mai Martaba Sarkin Yauri ya bai wa gwamnan jihar kyautarta.

    ..

    Asalin hoton, Abba Villa

    Bayanan hoto, An gudanar da raye-rayen al'adu na al'ummar masarautar Yawuri da suka haɗar da Kambari da Dukkawa da Gunguwa da Fulani da Yarabawa da ƙabilar Igbo da Zabarmawa da dai sauran ƙabilun da ke rayuwa a yankin.
    .

    Asalin hoton, Abba villa

    Bayanan hoto, Sannan an gudanar da wasanni kamar tseren kwale-kwale na maza
    .

    Asalin hoton, Abba Villa

    Bayanan hoto, An kuma wasan tseen kwale-kwale na mata
    .

    Asalin hoton, Abba Villa

    Bayanan hoto, Ga kuma wasan ninƙaya
    .

    Asalin hoton, Abba villa

    Bayanan hoto, Da wasan ninƙayar gora da sauran wasannin.
    .

    Asalin hoton, Sani Two Effect Yauri

    Bayanan hoto, An kuma baje-kolin kayan amfanin gonar da ake nomawa a yankin
    .

    Asalin hoton, Sani Two Effect Yauri

    ,

    Asalin hoton, Sani Two Effect Yauri

    Bayanan hoto, Ana noma nau'o'in dawa daban-daban a yankin Yauri
    .

    Asalin hoton, Sani Two Effect Yauri

    Bayanan hoto, Haka kuma ana noma na'in daban-daban na gero da maiwa a yankin
    .

    Asalin hoton, Sani Two Effect Yauri

    Bayanan hoto, Haka kuma ana gudanar da gasar fiɗa na mahauta inda za a yi fiɗar akuya cikin wani ƙayyadajjen lokaci.
    .

    Asalin hoton, Sani Two Effect Yauri

    Bayanan hoto, Hakama ana gasar ɗinki na riga da wando a cikin wani lokaci da aka ƙayyade.
  15. Hanya shida da za ku kauce wa bugun zuciya a lokacin kallon wasan ƙarshe a gasar Afcon

    .

    Asalin hoton, BBC Sport

    Ma'aikatar lafiya ta jihar Legas ta buƙaci mazauna jihar su rungumi wasu shawarwarin kula da lafiyarsu a yayin kallon wasan ƙarshe na gasar Afcon da Najeriya za ta kara da Ivory Coast.

    Hukumar ta bayar da shawarwarin ne domin kaucewa samun matsalar lafiya daga masu kallo a lokacin kallon wasan.

    Aƙalla mutum uku ne dai rahotoni suka ce sun mutu a lokacin da suke kallon wasan da tawagar Super Eagles ta kara ta Afirka ta Kudu a wasan kusa da na ƙarshe, sakamakon bugun zuciya.

    Cikin wata sanarwa da kwamishinan lafiyar jihar Legas ya fitar, ya zayyana wasu shawarwari shida da ya ce mutane su yi ƙoƙarin kiyayewa a lokacin da suke kallon wasan, don kauce wa samun matsala.

    Shawarwarin sun haɗar da:

    1. Ka san matsayin zuciyarka: Yana da kyau ka son iya abin da zuciyarka za ta iya jurewa. Ka yi ƙoƙarin tuntuɓar likita domin sanin wannan, sannan ka yi ƙoƙarin kauce wa duk abin da zai sa ka ƙetare iya abin da zuciyarka za ta iya jurewa.

    2. Yawaita shan ruwa da cin lafiyayyen abinci: Ku kauce wa shiga taron cunkoson da ba a samun wadatacciyar iska, domin samun ingantacciyar iskar numfashi, sannan ku kauce wa yawaita shan basara, tare da tabbatar da shan ruwa mai yawa da lafiyayyen abinci, domin samun wadataccen ruwa a jikinku, musamman la'akari da tsawon lokacin da za a ɗauka a zaune ana kallon wasan.

    3. Yawaita miƙewa domin hutu: Ku yawaita tashi tsaye, kuna miƙe jikinku, inda hali ma a riƙa ɗan zagayawa don kauce wa gajiya da bai wa hanyoyin jini damar kewaya jini.

    4. Zama da kyau ba tare da taƙura ba: Yana da kyau ku samun wurin zama mai kyau ta yadda ba za ku takura ba. Hakan na rage yawan gajiya da ciwon gaɓoɓi.

    5. Kwantar da hankali da nutsuwa: Yana da kyau ku riƙa gwada abubuwan da za su sanya ku nutsuwa kamar riƙe numfashi, da ƙoƙarin danne damuwa da ɓoye fushi a tsawon lokacin da za a ɗauke ana wasan.

    6. Shiryawa buƙatar gaggawa: Yana da kyau ku kalli wasan a wuraren da ke kusa da jami'an lafiya da wuraren da ke da hanyoyin kulawar gaggawa.

    Daga ƙarshe hukumar lafiyar ta shawarci su tuntuɓi asibiti da zarar sun ji wasu alamun da ba su gamsu da su ba a lokacin da suke kallon wasan.

  16. Ƙoƙarin tallafa wa ‘yan mata a lokacin da suke jinin al’ada a Borno

    A ƙasashe masu tasowa dubban mata ne ba sa zuwa makaranta sakamakon rashin samun auduga idan suna jinin al’ada a duk wata.

    A yanzu haka waɗansu ƙungiyoyi na ƙoƙari tallafa wa ‘yan mata a kowane wata a jihar Borno domin ganin sun samu sukunin zuwa makaranta.

    Abokiyar aikinmu, Badariyya Tijjani Kalawari ta ziyarci wata cıbiya a Maiduguri inda ake horas da ‘yan mata.

    Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon
  17. Gwamnatin jihar Kaduna ta ɗauki nauyin nuna wasan Najeriya a wasu wurare

    .

    Asalin hoton, Abdallah Yunus Abdallah/X

    Gwamnan jihar Kaduna Uba Sani ya ɗauki nauyin nuna wasan ƙarshe na Kofin Afirka na (Afcon) da Najeriya za ta fafata da ƙasar ivory Coast mai masaukin baƙin gasar a yau Lahadi da maraice.

    Cikin wata sanarwar da mataimaki na musamman ga gwamnan jihar kan kafofin yaɗa labarai na zamani, Abdallah Yunus Abdallah ya wallafa a shafinsa na X ya ce za a nuna wasan a waɗansu wasu manyan makarantun jihar.

    Wuraren da za a nuna wasan kyauta sun haɗar ta wuraren nuna wasanni na jami'ar Ahmadu Bello da ke Zariya, da jami'ar jihar Kaduna, da Kwalejin fasaha ta KASU da Kwalejin ilimi na Gidan Waya da Kwalejin gwamnatin tarayya ta Zariya.

    Tuni dai shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya umarci mataimakinsa Kashim Shettima ya jagoranci tawagar shugaban ƙasa zuwa wasan ƙarshen.

    Najeriya na fatan lashe kofin na Afirka karo na huɗu a tarihi, idan ta yi nasara a kan Ivory Coast.

  18. MDD na fuskantar matsin lamba don tallafa wa Falasɗinawa a Gaza

    ..

    Asalin hoton, Antonio Gutteres

    Majalisar Dinkin Duniya ta ce tana fuskantar matsin-lamba domin zaƙulo hanyar tallafa wa Falaɗinawa fiye da miliyan ɗaya da yaƙi ya ɗaiɗaita a birnin Rafah da ke Kudancin Gaza.

    Wannan na zuwa ne bayan Isra’ila ta ce ta ƙaddamar da farmaki ta ƙasa a yankin.

    Shugaban hukumar ayyukan jin ƙai ta Majalisar Dinkin Duniya,Jamie McGoldrick, ya shaidawa BBC cewa lamura na ƙara rikicewa a Gaza.

    Mista McGoldrick ya ce tun da ya fara aiki, bai taɓa ganin munin yanayi irin wanda ake ciki a Gaza ba.

    Ya ce dole a ɗauki matakan gaggawa na kai agaji ga mabuƙata, da kuma tsagaita wuta a yaƙin.

    Firaiministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya yi kiran a tsara hanyar fitar da mutane daga birnin Rafah, amma hukumomin bayar da agaji sun yi gargaɗin ɓarkewar annoba.

    Can a Isra’ila, dubban Yahudawa sun taru a tsakiyar birnin Tel Aviv domin zanga-zanagr rashin gamsuwa da yadda gwamnati ke tafiyar da aikin ceto mutanen da Hamas ta yi garkuwa da su a Gaza.

    Masu zanga-zangar sun ce ya kamata gwamnati ta mayar da hankali ne wajen kuɓutar da jama’arta da ake tsare da suu, a madadin zage damtse wajen yaƙi da Hamas.

    Amma Mr Netanyahuya sha nanata cewa hanya mafi sauƙi ta ceto waɗanda Hamas ta yi garkuwa da su itace kawar da mayaƙan ƙungiyar baki ɗaya.

  19. Trump ya ce zai bar Rasha ta ci karenta babu babbaka

    .

    Asalin hoton, Getty Images

    Fadar White House ta zargi Donald Trump da furta kalamai masu tayar hankali akan batun da ya shafi rashin ba da kariya ga mambobin kungiyar tsaro ta NATO daga duk wani hari na Rasha .

    Kakakin fadar ta White house Andrew Bates ya ce kalaman Mista Trump na barazana ga tsaron Amurka da ma duniya baki daya.

    A wani gangamin yaƙin neman zaɓe a South Carolina, Mr Trump ya ce mambobin ƙungiyar tsaro ta NATO da ba su biya kasonsu na kuɗaɗen tsaro ba, Amurka ba za ta taimaka mu su ba daga duk wani hari na Rasha.

    Ya ce ɗaya daga cikin manyan shugabannin ƙasashen Turai ya yi man wata tambaya kan cewa ko Amurka za ta taimaka masu idan Rasha ta kai mu su hari ko da ba su biya kasonsu na tsaro ba, ni kuma fada masa cewa sam ba zan taimaka wa kasarsa ba.

    Mista Trump ya kuma faɗa wa magoya bayansa cewa zai bar Rashar ta ci karenta babu babaka

  20. Ana alhinin rasuwar shugaban bankin Access a Najeriya

    .

    Asalin hoton, Herbert Wigwe

    A Najeriya manyan mutane na ci gaba da nuna alhininsu kan rasuwar shugaban bankin Access na Najeriya, Herbert Wigwe wanda ya rasu a Amurka sakamakon hatsarin jirgi mai saukar ungulu da yake ciki tare da iyalansa.

    Mista Wigwe tare da matarsa da kuma ɗansa sun rasa rayukansa ne a cikin hatsarin jirgin saman mai saukar ungulu a ranar Juma'ar da ta gabata a jAmurka .

    Jagoran adawar ƙasar Atiku Abubakar ya aike da saƙon ta'aziyyarsa ga kan rasuwar mutumin da ya bayyana da fasihin mutum mai halin kirki da dattaku.

    Cikin saƙon ta'aziyyar da ya wallafa a shafnsa na X, tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya ce ya kadu matuƙa da labarin rasuwar mista Wigwe, wanda ko yaushe burinsa shi ne tunanin kawo ci gaba.

    Ita ma shugabar ƙungiyar kasuwanci ta duniya, Ngozi Okonjo Iweala, ta bayyana mutuwar Mista Wigwe mai shekara 57 da matarasa da dansa a matsayin babban rashi ga Najeriya baki ɗaya.

    Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani a nasa ɓangare ya bayyana marigayin da cewa ɗaya ne daga cikin mutanen da ke da fikirar ɓullo da sabbani abubuwa

    Tuni dai masu bincike a California suka fara bincike kan abin da ya janyo hatsarin jirgin.

    Haka kuma wasu mutane uku da ke ciki jirgin suma sun mutu yayin da jirgin ya fado a lokacin da yake kan hanyarsa ta zuwa garin Boulder daga Palm Springs a jihar Nevada.

    Rahotonni na cewa an samu yanayi mara kyau tare da ruwan sama da zubar dusar ƙanƙara a yankin.