Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku bubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

A'isha Babangida, Nabeela Mukhtar Uba, Haruna Kakangi and Abdullahi Bello Diginza

  1. Rufewa

    Masu bin mu a wanna shafi nan muka kawo ƙarshen labarai da rahotonnin abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu za mu sake dawowa domin ci gaba da kawo muku sabbin labarai.

    A madadin sauran abokan aiki, Abdullahi Bello diginza ke cewa mu kwana lafiya.

  2. Rasha ta aike wa Burkina Faso kyautar tan 25,000 na alkama

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Burkina Faso ta ce ta karɓi tan 25,000 na alkama kyauta daga Rasha. Hakan na zuwa ne yayin da ake ƙara samun yauƙaƙar dankon zumunta tsakanin Moscow da ƙasashen da ke ƙarƙashin mulkin soji.

    Burkina Faso - wadda ke fama da matsalolin tsaro, sakamakon ayyukan masu iƙirarin jihadi - ta yanke alaƙa da tsohuwar uwargijiyarta wato Faransa, tare da umartar dakarun Faransa su fice daga ƙasar.

    A lokacin wani taro ne da aka gudanar a birnin St Petersburg cikin shekarar da ta gabata, shugaban Rasha Vladimir Putin ya alƙawarta aike wa Burkina Faso da kyautar alkamar.

    To sai dai ana ganin kamar ba alkamar kaɗai ce aka yi safararta daga Rashar zuwa Burkina Fason ba. A ranar Laraba wasu rahotonni suka ce an ga dakarun Rasha sun sauka a ƙasar.

    Dalilan da sojojin Burkina Fason suka bayar na gudanar da juyin mulki har biyu a ƙasar a shekarar 2022 shi ne rashin magance matsalar mayaƙa masu iƙirarin jihadi, waɗanda rikicinsu ya raba fiye da mutum miliyan biyu da muhallansu.

    Kusan shekara guda bayan umartar sojojin Faransa su fice daga ƙasar, ana ganin sojojin ƙasar wadda ke da arzikin ma'adinar na ƙara mayar da hankalinsu zuwa ga Rasha wajen neman tallafi.

  3. Amurka da Qatar na tattaunawa don sakin waɗanda ake garkuwa da su a Gaza

    Masarautar Qatar ta bayyana cewa sarkin ƙasar, Sheikh Tamim bin Hamad Al Thani ya zanta da shugaban Amurka Joe Biden ta wayar tarho don tattauna batutuwan da suka shafi Zirin Gaza da sauran yankunan Falasɗinawa.

    A lokacin tattaunawar, shugabanin biyu sun tattauna kan yunƙurin sakin sauran mutanen da Hamas ke ci gaba da garkuwa da su.

    Shugaban Amurka ya bayyana jin daɗinsa kan ƙoƙarin da Qatar ke yi ta fuskar ayyukan diplomasiyya da na jin-ƙai dangane da yanayin da ake ciki a Gaza.

    A wani labarin kuma, sarkin na Qatar ya jaddada ƙarfafa buƙatar haɗin kan ƙasashen yankin gabas ta tsakiya da ma duniya baki ɗaya don gaggauta tsagaita wuta a Gaza, tare da buɗe iyakokin yankin don bai wa mazauna yankin damar shige da fice.

    Kafafen yaɗa labaran ƙasashen Yamma sun nuna cewa a halin yanzu Amurka da Qatar na kan wata tattaunawar shiga tsakanin domin cimma yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da Hamas da za ta kai ga sakin sauran mutanen da ke hannun Hamas, tare da bayar da damar shigar da kayan agaji zuwa Gaza.

  4. Wace ƙungiyar tsaro ce Miyetti-Allah ta kafa kuma mene ne ayyukanta?

  5. Amurka ta musanta zarge-zargen da ake yi wa Isra'ila na kisan kare dangi a Gaza

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Ma'aikatar cikin gida ta Amurka ta ce hukuncin da kotun duniya ta yanke kan Isra'ila ya yi daidai da ra'ayinta " cewa Isra'ila na da 'yancin daukar mataki domin tabbatar da cewa ba a maimaita harin da Hamas ta kai wa Isra'ila a ranar 7 ga watan Oktoban 2023."

    Mai magana da yawun ma'aikatar ya ce Amurka ta yadda da hukuncin da kotun duniya ta yanke na da matukar tasiri a kokarin samar da zaman lafiya.

    "Mun yi imanin cewa zarge-zargen kidan kare dangi ba su da tushe ballantana makama sannan ita kanta kotun ba ta samu alamun kisan kiyashin ba ko kuma ta nemi a tsagaita wuta."

    To sai dai ya ce Amurka ba ta yi kasa a gwiwa ba wajen shaida wa Amurka "daukar duk wasu matakan da suka dace wajen rage yawan kisan fararen hula sannan ta bari ".

    Amurka dai na daya daga cikin kawayen Isra'ila da ba sa kiran da a tsagaita wuta sai dai su rinka neman da a tsagaita wuta domin kai musu kayan agaji zuwa Gaza.

  6. Akwai fiye da mata 800 a gidajen yarin Afghanistan - Taliban

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Mataimakin shugaban hukumar kula da gidajen yarin Afghanistan, Habibullah Badr, ya ce akwai fiye da mutum 19,000 a gidajen yarin ƙasar, ciki har da mata fiye da 800.

    Cikin wata tattaunawa da wani gidan talbijin a ƙasar, Mista Badr ya ce daga ciki akwai fursunoni 25 'yan ƙasashen ƙetare waɗanda ke da manyan laifuka.

    Ya ƙara da cewa bayan karɓar mulki da ƙungiyar Taliban ta yi ta saki fursunoni kusan 100,000 ta hanyar sallama ko yi musu afuwa da gwamnatin ƙungiyar ta yi.

    Ya ce akwai dakarun ƙungiyar kusan 200 da ke zama a gidajen yarin.

    Kame mata da 'yan mata kan batun hijabi da ƙungiyar ke yi a baya-bayan nan ya janyo ce-ce-ku-ce mai yawa a ƙasar.

    A farkon watan Janairun 2023, babban daraktan gidajen yarin ƙasar, Mohammad Yusuf Mestri, ya shaida wa BBC cewa fiye da fursunoni 12,000 ne ke tsare a gidajen yarin ƙungiyar, wasu daga cikinsu mata ne da ƙananan yara.

  7. WHO ta musanta zargin cewa Hamas na amfani da asibitoci don kai hare-hare

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban hukumar lafiya ta duniya, WHO ya musanta ikrarin da Isra'ila ta yi cewa hukumar na dauke kai kan shaidun da ke nuna kungiyar Hamas na amfani da asibitoci domin fakewa su kai hare-hare.

    Jakadan Isra'ila, Ambasada Meirav Eilon Shahar yayin wani taro na shugabannin hukumar ta lafiya ranar Alhamis.

    To sai dai a wani martani, shugaban hukumar ta lafiya, Tedros Adhanom Ghebreyesus ya ce "wannan zargi ne maras makama sun yi muni kuma ka iya jefa ma'aikatanmu cikin hadari".

    "A matsayinmu na hukumar duniya, WHO ba ta nuna wani son-kai sannan kuma tana aiki ne wajen ganin ta inganta rayuwar al'umma".

    Isra'ila ta dade tana cewa Hamas na amfani da asibitoci a Gaza domin fakewa su kai hare-hare, kuma Isra'ilar ta ce wannan ne dalilanta na kai hare-hare a wuraren a gaza.

    Dama dai ko a watan Nuwamba sai dai Amurka ta ce ta samu bayanan sirri da ke nuna Hamas din na da cibiyar da take tsara hare-hare a karkashin asibitin Al Shifa da ke Gaza.

    Sai dai kuma kungiyar ta Hamas ta sha musantawa.

  8. An yi garkuwa da shugaban jam'iyyar PDP na Legas

    An yi garkuwa da shugaban jam'iyyar PDP na jihar Legas, Mr. Philip Aivoji. An dai yi garkuwar da shugaban ne a akan titin Lagos zuwa Ibadan da misalin karfe shida na yamma ranar Alhamis.

    Sakataren watsa labarai na jam'iyyar, Hon Hakeem Amode ya tabbatar da sace shugaban na jam'iyyar.

    Rahotanni dai sun ce an yi garkuwa da shugaban jam'iyyar ne lokacin da yake komawa gida bayan wata ganawa da gwamnan jihar Oyo, Seyi makinde da na jihar Osun, Ademola Adeleke.

  9. Jirgi ya zame daga titinsa a filin jirgin birnin Ibadan

    .

    Asalin hoton, Google

    An kara samun wani jirgin sama mallaki wani ya samu zamewa daga kan titunsa a filin jirgin birnin Ibadan da ke jihar Oyo.

    Mai magana da yawun hukumar da ke bincike kan ingancin ababan hawa ta Najeriya, Tunji Oketunmbi ya tabbatar da faruwar al'amarin kuma ya ce sun aike da ma'aikatansu zuwa wurin hadarin.

    Akalla akwai manyan mutane 10 a cikin jirgin sai dai rahotanni sun ce ba a samu rasuwa ko jikkata ba sakamakon hadarin.

    Wannan dai na zuwa ne watanni biyu bayan an samu irin wannan hadarin a filin jirgin na Ibadan.

  10. Kotu a Lagos ta yi wa wani fasto daurin rai da rai bisa laifin fyade

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Wata Kotu a birnin Legas da ke Najeriya ta yi wa mamallakin cocin Reign Christian Ministry, Oluwafeyiropo Daniels, daurin rai da rai bisa kama shi da laifin yi wa "wata mai halartar cocinsa fyade."

    Mai shari'a Rahman Oshodi na kotun da ke yanke hukunce-hukuncen laifukan da suka jibanci lalata ta Ikeja, ta samu Fasto Oluwafeyiropr Daniels da laifin yi wa mambar cocinsa fyade da kuma lalata.

    Dama dai gwamnatin jihar Legas ta gabatar da faston a gaban kuliya a watan Mayun 2023 bisa laifuka uku da suka jibanci fyade da lalata da mata guda uku.

    Wata shaida da ba a ambaci sunanta ba ya shaida wa kotun cewa mr Daniels ya yi mata fyade a lokacin gudanar da addu'o'i a gidan faston da ke unguwar Lekki da ke Legas.

    Kamfanin dillancin labarai na NAN ya rawaito wata shaida wadda ita ma mambar cocin ce ta ce faston ya yi mata fyade a wasu lokuta kuma har ta samu juna biyu amma sai cikin ya bare yayin wani hadari da ta samu a kan titin Ilorin zuwa Ibadan.

  11. 'Yan Isra'ila na tofa albarkacin bakinsu kan hukuncin kotin duniya a Gaza

    ..

    Hukuncin na kotun duniya dai na janyo martani da ra'ayoyi daga titunan manyan biranen kasar Isra'ila.

    Kotun ta duniya dai ta yanke cewa dole ne Isra'ila ta dauki dukkan matakan da suka kamata wajen ganin ta kawo karshen kisan kare dangi a Gaza, duk da dai ba ta yi umarni da a dakatar da yakin da ake yi ba.

    Dvir, wani mazaunin birnin Tel Aviv, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa yana tunanin sakamakon hukuncin "abu ne mai kyau" kuma hakan zai bai wa Isra'ila damar cigaba da kare kanta daga Hamas.

    Shi ma wani mazaunin birnin na Tel Aviv, Josh Mover ya ce " Ina tunanin akwai munafurci da ake kulla wa Isra'ila, domin idan ka kalli yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya za ka ga wurare da yawa soke-soke ne a kan Isra'ila kuma kasashen ma da suka yi kaurin suna wajen tauye hakkokin dan adam ba a caccakar su kamar yadda ake yi wa Isra'ilar".

    Da Take mayar da martani ga hukuncin, marubuciyar nan Deborah Jacobi ya ce " Babu wanda yake son ganin ana kashe fararen hular da babu ruwansu.

    "Hakika mun yi rashin matasan Isra'ilawa wadanda ba su ji ba su gani ba da suka sadaukar da rayuwarsu a wajen kare rayukanmu. Sannan kuma Hamas za ta mika wuya kuma za su dawo mana da mutanen da suka yi garkuwa da su, kamar yadda ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP.

  12. Muna sane da yadda 'yan Kamaru ke amfani da karfi a wasanninsu - Moses Simon

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Dawan wasan gaba na Najeriya Moses Simon ya ce suna sane da yadda Kamaru ke saka karfi wajen buga wasa, yana mai cewa sun tattauna hakan a tsakaninsu 'yan wasa.

    A gobe Asabar ne tawagar Super Eagles ta Najeriya za ta gwabza da ta Indomitable Lions ta Kamaru a wasan zagaye na sili daya kwale na gasar Kofin Afirka ta 2023 da ke gudana a Ivory Coast.

    "Mun san cewa suna saka karfi sosai, amma mu ma muna da karfi," in ji dan wasan yayin taron manema labarai a yau Juma'a.

    "Amma ni ina ganin karfin jiki ba shi ke kawo nasara ba, mu burinmu shi ne kawai mu cinye su duk da ta hanyar da ta dace."

    Wasa tsakanin kasashen cike yake da tarihi, kuma karo na karshe da suka kara shi ne a 2019, inda Najeriya ta yi nasara da ci 3-2 a irin wannan zagayen na gasar.

  13. Dalilin da ya sa tawagarmu ba ta je jamhuriyar Nijar ranar Alhamis ba - ECOWAS

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Afirka ta Yamma, ECOWAS ko kuma CEDEAO ta bata wa jamhuriyar Nijar rai sakamakon dage zuwan tawagarta wadda za ta tattauna da kasar saboda dalilin da ta kira " 'yan matsalolin karfen nasara" da suka faru da jirgin da ya kamata ya dauki mafi yawan mambobin tawagar da birnin Abuja zuwa Niamey.

    Firaiministan jamhuriyar Nijar, Lamine Zain ya soki kungiyar ta ECOWAS kan rashin halartar zaman sulhun.

    To sai dai wata sanarwa da kungiyar ta ECOWAS ta fitar ta ce rashin zuwan tawagar ba ya nufin wulakanta gwamnatin sojin jamhuriyar Nijar illa dai kawai "matsalar jirgin da aka samu wanda hukumar ta ECOWAS ta dauka haya domin ya kai tawagar birnin Niamey daga Abuja".

    Ecowas ta ce za ta sake fitar da lokacin domin tawagar tata ta kai wannan ziyara zuwa jamhuriyar ta Nijar.

    Kungiyar ECOWAS dai ta kakaba wa jamhuriyar Nijar jerin takunkumai tun bayan juyin mulin da shugabannin sojin kasar suka yi a watan Yulin 2023, inda suka hambare shugaba Mohamed Bazoum.

    Kungiyar ta nemi da sojojin su saki hambararren shugaban tun bayan da suka yi masa daurin talala.

    ECOWAS ta kuma yi barazanar daukar matakin soji baya ga yanke duk wata alakar kasuwanci da kasar.

    Gwamnatin mulkin sojin ta Nijar dai na yi wa tawagar ta ECOWAS kallon wani abu da zai warware zaman tankiyar da ake ciki.

    ...

    Asalin hoton, Reuters

  14. Kungiyar Hamas ta yi maraba da hukuncin kotun duniya kan Isra'ila

    Kungiyar Hamas ta ce tana maraba da hukuncin da kotun duniya ta yanke na umurtar Isra'ila ta dauki dukkan matakan dakatar da duk wani abu da ya shafi kisan ƙare dangi a Gaza.

    Sami Abu Zuhri wanda babban jami'i ne a kungiyar ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa "hukuncin kotun ta duniya abu ne mai muhimmancin gaske da zai taimaka wajen mayar da Isra'ila saniyar ware da kuma bayyana irin laifukan da take aikatawa a Gaza.

    "Muna kira da a tursasa Isra'ila da ta aiwatar da hukuncin kotun."

    A ranar Juma'ar nan ne dai kotun ta duniya ta kada kuri'ar amincewa da umurtar Isra'ila ta dauki dukkan matakan dakatar da duk wani abu da ya shafi kisan ƙare dangi a Gaza

  15. 'Yan Isra'ila masu zanga-zanga na tsare motocin agaji masu zuwa Gaza

    ..

    Daruruwan 'yan Isra'ila masu zanga-zanga sun tsare wasu manyan motocin da ke dauke da agaji zuwa Gaza, kwana uku a jere.

    Masu zanga-zangar dai da suka hada da iyalan mutanen da aka yi garkuwa da su suna ta faman daga tutocin Isra'ila suna rera kirarin ka da a "taimaki abokan gaba".

    Daruruwan masu zanga-zangar dai na neman cewa ka da a kai wa Gaza tallafin kayan agaji har sai sun sako musu 'yan uwansu da suka yi garkuwa da su.

    Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da Amurka ta nemi da a kai kayan agaji zuwa Gazar "ba tare da wata matsala ba."

    Kwana uku kenan a jere da masu zanga-zangar ke mamaye tituna a Kerem Shalom da ke kan iyaka tsakanin Isra'ila da Gaza, inda suke kokarin kange motocin da ke dauke da kayan agajin.

    Hakan ne dai ya janyo cunkuson manyan motocin dauke da kayan agaji a mashigar ta Kerem Shalom.

    Ofishin jinkai na Majalisar Dinkin Duniya ya ce yanzu haka manyan motoci dauke da kayan agaji 153 ne kawai suka samu damar shiga Gaza ranar Larabar da ta gabata, wani abu da ofishin ya bayyana da ya karanta.

    Gwamantin Isra'ila dai na fuskantar matsin lamba domin ta kyale kayan agaji su shiga Gaza, inda kuma a wurin 'yan kasar ke kara samun matsin lambar neman a ceto musu 'yan uwansu da ke hannun Hamas.

  16. Kotu a Kenya ta hana gwamnati aikewa da 'yan sandan kasar zuwa Haiti

    ..

    Asalin hoton, AFP

    Babbar kotun kasar Kenya ta ki amincewa da bukatar gwamnatin kasar na aikewa da jami'an 'yan sandan kasar zuwa Haiti domin yakar kungiyoyin daba.

    Alkalin kotun ya ce kai 'yan sandan Haiti ya saba ka'ida kasancewar majalisar tsaron kasar ba ta da hurumin doka na aikewa da jami'an tsaro zuwa wata kasa wajen Kenya.

    Ya kara da cewa majalisar za ta iya aikewa da sojoji ne kawai ba 'yan sanda ba, a irin wannan yanayi na kwantar da tarzoma.

    A bara, kasar Kenya dai ta aike da irin wannan rundunar ta jami'an tsaro zuwa Haiti domin samar da zaman lafiya.

    Alkalin ya kuma yi bayanin cewa dokokin kasar Kenya sun amince da gwamnati ta aike da 'yan sanda ne kawai idan akwai yarjejeniyar taimakekeniya tsakanin kasashen biyu.

    To sai dai gwamnatin kasar ta Kenya ta ce za ta daukaka kara.

  17. An gano shimfiɗar ban girma na shugaban kasa da aka sace a Malawi

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    'Yan sanda a Malawi sun gano shimfiɗar ban girma na shugaban kasa da aka sace a garin Mwanza da ke kudancin kasar, kusa da kan iyaka da Mozambique.

    An sace shimfiɗar ne tare da tanti a daren Laraba yayin da ake jigilar kayayyakin zuwa garin, inda ake sa ran shugaba Lazarus Chakwera zai gudanar da wani taron jama'a a ranar Juma'a.

    Kakakin rundunar ‘yan sandan, Peter Kalaya ya bayyana cewa, an kama wasu mutane biyu da suke da hannu a lamarin.

    Ana sa ran shugaba Chakwera a Mwanza domin bikin kaddamar da ginin filin wasa, da kuma duba sabbin gidajen ‘yan sanda da aka gina.

    Lamarin dai na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan da wasu da ba a san ko su waye ba suka kutsa kai ofishin mataimakin shugaban kasar Saulos Chilima da ke Lilongwe babban birnin kasar inda suka yi awon gaba da wasu kayayyaki.

  18. Kotun ƙoli ta tabbatar da hukuncin ɗaurin shekara biyar kan Farouk Lawan

    ...

    Kotun koli ta tabbatar da hukuncin shekara biyar da aka yanke wa tsohon ɗan majalisar wakilai Farouk Lawan bisa samun sa da laifin karɓar cin hancin na kuɗi dala 500,000 daga hannun dan kasuwa Femi Otedola, shugaban kamfanin Zenon Petroleum and Gas Limited

    Ƙarar da aka ɗaukaka ta buƙaci a soke hukuncin da kotun ɗaukaka ƙara da ke Abuja ta yanke a ranar 24 ga Fabrairu, 2022, inda ta yanke masa hukuncin ɗaurin shekaru biyar a gidan yari tare da wanke shi a kan tuhume-tuhume biyu daga cikin ukun da aka gurfanar da shi a kai, waɗanda suka shafi cin hanci da rashawa.

    A hukuncin da mai shari’a John Okoro ya shirya amma mai shari’a Tijjani Abubakar ya karanta, kotun kolin ta ce ƙarar da Lawan ya shigar ba ta da cancantar da za a saurare ta sannan ya yi watsi da ita.

    Tawagar masu yanke hukuncin da ta ƙunshi alƙalai biyar gaba ɗaya sun tabbatar da hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke a shekarar 2022 wanda ya tabbatar da hukuncin da aka yanke wa Lawan na shekaru biyar dangane da tuhume-tuhume uku da ake yi masa.

    • Farouk Lawan: Dan majalisar da ya haskaka a baya amma ya tafi kurkuku
    • Gamayyar ‘yan majalisar wakilai na adawa a Najeriya azarɓaɓi ne- Masana
  19. Dole ne Isra'ila ta dakatar da kisan ƙare dangi - Kotun Duniya

    ...

    Asalin hoton, ICJ

    Kotun Majalisar Ɗinkin Duniya ta kada kuri'ar amincewa da umurtar Isra'ila ta dauki dukkan matakan dakatar da duk wani abu da ya shafi kisan ƙare dangi a Gaza.

    Alƙalan kotun sun kaɗa ƙuria'a 16 kan cewa akwai bukatar Isra'ila ta dauki dukkan matakan da suka dace na hanawa tare da hukunta wadanda ke da hannu wajen haddasa kisan kiyashi kan Falasdinawa a Zirin Gaza.

    Har ila yau, ta hanyar kuri'a 16, kotun ta ce dole ne Isra'ila ta dauki matakan gaggawa don tabbatar da samar da agajin jin kai da na yau da kullun da ake bukata cikin gaggawa.

  20. 'Matakan da Isra'ila ta ɗauka na rage cutar da fararen hula bai wadatar ba'

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    A zaman kotun Majalisar Ɗinkin Duniya kan kiran Isra'ila da tsagaita buɗe wuta Gaza, alƙaliya Joan Donoghue ta karanto wasu wasiku da kalamai da manyan jami'an Majalisar Dinkin Duniya suka yi game da rikicin jin kai a Zirin Gaza.

    Wasu daga cikin waɗannan wasiƙun sun lura da rugujewar al'ummar Gazan kuma rikicin jin kai yana ƙara ta'azzara.

    Donoghue ta ce kotun ta yi la'akari da cewa fararen hula a Gaza na cikin mawuyacin hali.

    Ta lura cewa ana ci gaba da kai farmakin sojin Isra'ila kuma Firaministan ya ce yaƙin zai ɗauki watanni masu yawa.

    Isra'ila ta ce ta dauki matakin rage cutar da fararen hula amma yayin da irin wadannan matakan "ya kamata a karfafa su", alƙaliyar ta ce ba su wadatar ba.

    Donoghue ta ce dole ne Isra’ila ta tabbatar da gaggawar cewa dakarunta na soji ba su aikata wani abu daga cikin wadannan ayyuka ba – kashe Falasdinawa ko kuma haifar da mummunar illa a jiki ko ta kwakwalwar mutane.

    Ta kara da cewa, "Dole ne Isra'ila ta Ɗauki matakan da za ta iya Ɗauka don hanawa da kuma hukunta masu tunzura jama'a na yin kisan kare dangi kan 'yan kungiyar Falasdinawa."

    Dole ne Isra'ila ta dauki matakai masu inganci cikin gaggawa don ayyukan yau da kullun da kuma matakan jin kai, in ji ta.

    Donoghue ya ce dole ne Isra'ila kuma ta mika rahoto ga kotu a cikin wata guda da wannan umarni.