Rufewa
Da haka muke bankwana da ku a wannan rana sai kuma gobe Litinin. Umaymah Sani Abdulmumin ke cewa a kwana lafiya.
Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najieriya da sauran sassan duniya.
Abdullahi Bello Diginza
Da haka muke bankwana da ku a wannan rana sai kuma gobe Litinin. Umaymah Sani Abdulmumin ke cewa a kwana lafiya.
Wata ƙungiyar bayar da agaji ta addinin kirista ta ce mayaƙa masu alaƙa da kungiyar Al-Qaeda sun sako wani BaJamushe ɗan mishan da suka kama shekara ɗaya da ya wuce a kasar Mali.
Kungiyar mai suna Missionaries for Africa ta ce an yi awo gaba da Fr. Hans Joachim Lohre ne a babban birnin kasar Bamako.
Babu wasu bayanai game da yadda aka yi aka sako shi kuma gwamnatocin ƙasashen Jamus da Mali ba su komai ba kan batun.
Fr. Lohre ya kwashe shekaru 30 a Mali yana koyar da darussan hulda tsakanin addinai a wata makaranta mai koyar da darussan addinin musulunci da kiristanci a haɗe.
Satar mutane ne ba bakon lamari ba ne a Mali amma ba kasafai akan yi hakan a babban birnin kasar ba.
Dubun-dubatar mutane ne suka yi wani maci a tsakkiyar birni Landan wasunsu dauke da tutocin Isra'ila domin nuna rashin amince da karuwar nuna kin jini Yahudawa.
Hakan na zuwa ne kwana daya bayan da wasu dubban mutanen suka yi zanga-zanga nuna goyon bayan Falasdinawa a birni tare da kiran a tsagaita wuta a Gaza.
Burtaniya da wasu kasashen sun shaidi karuwar laifukan da ke da alaka da nuna kiyayya ga Yahudawa tun bayan fara yakin tsakanin Isra'ila da Gaza.
Wadanda sun ka shirya gangamin sun kira shi da gangami mafi girma kan nuna adawa da kin jinin Yahudawa a London tun shekarun 1930.

Asalin hoton, Getty Images
Faraministan Isra'ila Benjamin Natanyahu ya kai wa sojojin Isra'ila ziyara a Gaza karon farko tun bayan somawar yaƙinsu da Hamas.
Da yake jawabi zagaye da sojoji a arewacin Gaza, Mista Natanyahu ya ce Isra'ila za ta ci gaba da yaƙin har sai ta samu nasara.
Ya nanata musu cewa manufofin yaƙin guda uku ne wato kawar da kungiyar Hamas, da dawo da dukkanin wadanda aka yi garkuwa da su da kuma tabbatar da cewa Gaza ba ta sake zama barazana ga Isra'ila ba.
Mai ba shugaban kasar Amurka shawara kan tsaro ya ce Shugaba Biden zai sake tattaunawa da Mista Natanyahu nan gaba a yau Lahadi.
Shugaba Biden na Amurka ya ce musayar fursunoni tsakanin Isra'ila da Hamas wani kokari ne nasu na diflomasiya.
Biden ya ce suna cigaba da matsin lamba domin ganin an sako Amurkawa da sauran mutanen da ake rike da su.
Sannan ya ce zasu cigaba da matsa kaimi wajen ganin yarjejeniyar tsagaita wutar ta tsawaita.
Shugaban na Amurka ya ce abin farin ciki ne ganin yadda ake sada iyalai da 'yan uwansu da sauran dangi da abokan arziki.
Ma'aikatar harkokin noma ta Najeriya ta ce za ta ci gaba da bayar da tallafin irin noman rani mai inganci kyauta har zuwa lokacin da za a kammala shukar noman rani na bana.
Hukumomin kasar sun ce sabon irin alkama a noman ranin na bana an kawo shi ne daga kasar Mexico wanda zai iya jure rashin ruwa na wani lokaci.
Ministan albarkatun noma na Najeriya Sanata Abubakar Kyari ya ce babbar manufar shirin tallafawa manoma shi ne bunkasa samar da abinci a sassan kasar.
Matsalar sauyin yanayi da ake gani na barazana ga harkokin noma, sai dai ministan ya ce ana daukan matakan shawo kan matsalolin manoma domin samar da wadataccen abinci a Najeriya
Ƙungiyar hulda da jama'a ta NIPR a Najeriya ta buƙaci a ɗauki matakin gaggawa kan yadda mutuncin ƙasar ke zuɓewa a idon duniya saboda yadda ake gabatar da ita a matsayin matalauciya.
Ƙungiyar ta sha alwashin bin hanyoyin da suka dace domin kawo karshen lamarin, domin a cewarta Najeriya ta fi karfin matsayin da duniya ta ajiye ta a yanzu.
NIPR ta ce bayanan da ake yaɗawa kan talauci da aikata rashawa da ma sauran dabi'u marasa kyau a Najeriya, babu hakikanin gaskiya a ciki.
Dakta Sule Ya'u Sule, ɗan kwamitin koli ne na kasa a ƙungiyar, kuma babban malami a jami'ar Bayero ta Kano, dake cewa wasu tsiraru ne ke yaɗa wannan manufa.
Dakta Sule ya kuma yi bayanin ɓangarorin da wannan lamari ya shafa, lamarin da ya ce ya yi nisa wajen zubar da mutumcin Najeriyar a idon duniya.
NIPR ta ce ta tanadin wasu kwararru da za su yi aikin gangamin wayar da kai da kuma neman mafita dagane da wannan matsala, duk da cewa ta ce ta riga ta gano cewa duk wani aiki da za ta yi, ba zai kai ga nasara ba har sai gwamnati ta yi abin da ya kamata.
Najeriya dai ta daɗe tana tsintar kanta a jerin ƙasashe masu fama da talauci da abubuwan koma baya daban-daban.
Ko a shekara ta 2022 kididdigar kungiyar da Transparency International ta fitar ta ce kasar tana a matsayi na 150 daga cikin ƙasashe 180 masu fama da rashawa a duniya.
Ofishin Firaministan Isra'ila ya wallafa sunayen mutanen da ya ce Hamas ta saka kawo yanzu a karkashin yarjejeniyar musayar fursunonin bayan tsagaita wuta na kwanaki hudu. Mutanen sun hada da:
Iyalan Brodutch:
Iyalan Almog-Goldstein:
Iyalan Elyakim:
Ƙungiyar ƙasashen Yammacin Afirka, Ecowas ta yi alla-wadai da kokarin hargitsa zaman lafiya a Saliyo.
Ecowas a wata sanarwa da ta fitar ta ce abin takaici ne ganin yadda wasu tsiraru mutane suka yi kokari tada hankula da hargitsa zaman lafiya da dokokin kudin tsarin mulkin kasa a Saliyo.
Ƙungiyar ta bukaci a kama tare da gurfanar da wadanda suka aiwatar da wannan yunkuri haramtacce.
Gwamnatin Saliyo dai ta sanya dokar hana fita Ta sa'o'i 24 a faɗin ƙasar a kokarin tabbatar da zaman lafiya da kwantar da hankulan mutane
Da safiyar yau Lahadi ne mazauna birnin Saliyo suka ce sun ji ƙarar harbe-harben ne daga aƙalla barikokin soji biyu da ke birnin.
Wani jami'in da ya buƙaci a sakaya sunansa ya ce shaidun gani da ido sun tabbatar masa cewa wasu mahara ɗauke da makamai sun fasa gidan yarin 'Pademba Road' da ke tsakiyar birnin Freetown tare da sakin fursunoni.
Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ce Hamas ta ayyana sakin wani mutum ɗan ƙasar Rasha daga cikin mutanen da take garkuwa da su.
Ƙungiyar ta ce ta saki mutumin ne bisa yunƙurin Shugaba Putin.
Cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na intanet, ta ce : "Bisa ƙoƙari da shugaban Rasha Vladimir Putin, da matayin da Rasha ta ɗauka na goyon bayan Falasɗinawa, kungiyar Hamas ta saki ɗan ƙasar Rasha da take garkuwa da shi".

Asalin hoton, MOHAMMED SABER/EPA-EFE/REX/Shutterstock
A jiya an samu fargaba ta 'yan sa'o'i bayan da aka jinkirta musanyar fursunoni tsakanin Isra'ila da Hamas.
Hamas ta zargi Isra'ila da saɓa sharuɗun yarjejeniyar, tana mai cewa ana samun matsala wajen shigar da kayan agaji zuwa arewacin Gaza da ƙa'idar da Isra'ila ke bi wajen sakin fursunonin Falasɗinawa.
Yanayin da daga baya masu shiga tsakani , Qatar da Masar suka daidaita.
Wakilin BBC a Gaza Rushdi Abu Alouf, wanda ke aiko da rahotonni daga birnin Santambul ya ce hankula sun sake tashi yayin da har yanzu akwai kusan mutum 400,000 da ke zaune a arewacin Gaza, da ke fuskantar ƙarancin tallafi.
"Tun da fari mun sani cewa wannan yarjejeniya na da matuƙar wahala, sannan tana cike da kasada. yarjejeniya ce da ka iya ɓallewa a kowane lokaci''.
"Al'amura za su iya rincaɓewa a kowane lokaci. Isra'ila na amfani da jirage marasa matuƙa a arewaci da kudancin Gaza. Hamas kuma ta ce ɗaya daga cikin sharuɗan yarjejeniyar shi ne Isra'ila ba za ta yi amfani da jirage marasa matuƙa ba.''
"'Haka kuma, a halin da ake ciki, a jiya mun ji ƙarar harbin bindiga a arewaci inda aka kashe mutum biyu. Har yanzu akwai sojojin Isra'ila kuma mutane na ci gaba da zuwa yankin domin ganin abin da ya faru da gidajensu. Abin tamkar tafiya ce a cikin laka, a kowane lokaci za ka iya zamewa. Mutane na ƙoƙarin yin abubuwansu cikin gaggawa amma a kowane lokaci komai zai iya faruwa'.

Asalin hoton, EVN
Majalisar Dinkin Duniya ta tabbatar da cewa an tsallaka da litar man fetur 129,000 zuwa Gaza a ranar Lahadi.
Kimanin manyan motoci 61, ɗauke da kayan agaji ne kuma suka isa arewacin Gaza a yau, adadi mafi yawa da ya isa yankin tun ranar 7 ga watan Oktoba.
Kayayyakin agajin sun haɗar da abinci da ruwan sha da magunguna.
Mutane sun yi ta hawa dogayen layukan karɓar tallafi a rana ta uku daga cikin kwanaki huɗu na yarjejeniyar tsahirta wuta da Qatar ta jagoranta tsakanin Isra'ila da Hamas.

Asalin hoton, EVN
Mutane da dama kan ci namijin goro da nfin ya taimaka musu ajen ƙarin ƙuzarin domin gamsar da iyalansu a mu'amalar aure, to sai dai masana sun ce ba haka lamarin yake ba.
Dakta Auwal Musa Umar ƙwararren likitan abinci a Najeriya ya ce bisa dukkan bincike da aka yi babu wata hujja da ke nuna cewa namijin goron na taimaka wa ƙarfin namiji, ko ƙarfin sha'awarsa.
Likitan ya kuma ce bincike ta tabbatar da cewa daɗewa ana ta'ammali da namijin goro ba ta hanyar da ta dace ba, kan haifar da matsalar rage ƙarfin ƙwayoyin halitta na haihuwa ga maza, lamarin da ka iya jamyo wa namiji matsalar rashin haihuwa.