An lalata wasu makarantun da Falasɗinawa ke samun mafaka - MDD

Wannan shafi ne da ke kawo mu ku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza, Mukhtar Adamu Bawa, Haruna Kakangi and Ahmad Tijjani Bawage

  1. Rufewa

    Mun zo ƙarshen rahotanni a wannan shafi na labarai kai-tsaye.

    Sai kuma gobe da safe idan Allah ya kai mu.

    Ahmad Tijjani Bawage ke cewa mu kwana lafiya.

  2. Isra'ila ta ce sojojinta sun yi wa birnin Gaza ƙawanya

    Israeli army spokesman Daniel Hagari

    Asalin hoton, Getty Images

    Mai magana da yawun sojojin Isra'ila Daniel Hagari ya sanar da yammacin nan cewa sojojinsu sun yi wa birnin Gaza ƙawanya ta kowane ɓangare.

    Hagari ya ce dakarun Isra'ila "sun kammala zagaye birnin Gaza, a tsakiyar da Hamas ke harkokinta."

    Sai dai kuma, reshen soji na ƙungiyar Hamas, Al-Qassam Brigades, ya ce Gaza za ta zame wa Isra'ila gagara-badau.

  3. Joe Biden ya yi kira da a tsagaita wuta a Gaza

    Joe Biden

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Amurka Joe Biden ya yi kira da a tsagaita a rikici tsakanin Isra'ila da Hamas a Gaza.

    Shugaban na jawabi ne a lokacin yaƙin neman zaɓe a Minneapolis, inda wani ya yi kutsen magana tare buƙatarsa ya kira a tsagaita wuta.

    "Ina ganin ya kamata a tsagaita wuta," ya mayar da martani, inda ya ce hakan zai bai wa waɗanda ake riƙe da su samun damar ficewa.

    Wasu ƴan Amurka da ba a san adadinsu ba sun bar Gaza a ranar Laraba, a matsayin ƙungiya ta farko da ta fice tun bayan soma yaƙin. Wasu 400 na cikin jerin waɗanda za su fice a rana Alhamis ɗin nan.

    Babu ƴan Canada cikin jerin mutanen da suka fice ranar Laraba ko kuma waɗanda za su bar Gaza a ranar Alhamis.

    Firaministar Canada Melanie Joly ta ce akwai ƴan Canada 400 da suka maƙale a Gaza.

    Isra'ila na ci gaba da lugudan wuta kan Gaza tun bayan harin ranar 7 ga watan Oktoba da ƙungiyar Hamas ta kai mata, wanda ya yi sanadin mutuwar mutum 1,400 da kuma garkuwa da 239.

    Ma'aikatar lafiya a Gaza wadda ke karkashin ikon Hamas ta ce sama da mutane 9,000 ne aka kashe tun bayan da Isra'ila ta mayar da martani ta hanyar kai harin ramuwar gayya.

  4. Kwale-kwale ya kife a jihar Adamawa

    Hatsarin kwale-kwale

    Asalin hoton, Getty Images

    Rahotannin da muke samu daga jihar Adamawa da ke arewa maso gabashin Najeriya na cewa wani jirgin ruwa ya kife ɗauke da fasinjoji da dama.

    Lamarin ya faru ne a karamar hukumar Fufore da ke jihar.

    Zuwa yanzu an ciro gawawwaki shida, yayin da aka ceto mutane 14 da ransu.

  5. CBN ya ce babu ƙarancin takardun kuɗi a Najeriya

    Kuɗi

    Asalin hoton, CBN

    Babban Bankin Najeriya CBN ya karyata raɗe-raɗin da ake yi na ƙarancin takardun kuɗi naira a ƙasar, yayin da rahotanni ke cewa babu isassun kuɗaɗe a wasu bankunan kasuwanci a faɗin ƙasar.

    A cikin wata sanarwa da CBN ya fitar ta hannun mai magana da yawunsa Isa AbdulMumin, ya zargi wasu kwastomomin da haddasa firgici cikin mutane.

    AbdulMumin ya bayar da tabbacin cewa babban bankin na ƙoƙarin ganin an samu ci gaba a harkokin kuɗi a faɗin ƙasar.

    "Yayin da muke lura da damuwar ‘yan Najeriya game da samar da kuɗi don yin hada-hada, muna so mu tabbatar wa jama’a cewa akwai isassun kuɗaɗen a rumbun mu don gudanar da ayyukan tattalin arziki a ƙasar,” in ji sanarwar.

    CBN ya ce rassansa da ke faɗin ƙasar na aiki don tabbatar da cewa an samu zagayawar kuɗaɗe a faɗin jihohi.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  6. Mutane da dama sun mutu a hatsarin mota a Abuja, Daga Zubairu Ahmad Kasarawa

    Wani mummunan hatsarin mota da ya auku a unguwar Mpape da ke birnin tarayya Abuja, ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama tare da jikkatar wasu.

    Haɗarin ya auku ne lokacin da wata motar tifa ta kwace inda ta afka wa motoci da wasu mutanen da ke tafiya a gefen hanya.

    Ku danna ƙasa don sauraron rahoton Zubairu Ahmad Kasarawa.

    Bayanan sautiLatsa hoton da ke sama don sauraron rahoton
  7. An lalata makarantu huɗu da Falasɗinawa ke samun mafaka cikin kwana ɗaya - MDD

    Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce an lalata wasu makarantu huɗu da ake amfani da su a matsayin wuraren mafaka a Gaza cikin kasa da kwana ɗaya.

    Tun da farko, hotunan bidiyo sun nuna yadda harin bam ɗin ya auku a makarantun.

    MDD ta ce an lalata makaranta ɗaya a sansanin ƴan gudun hijira na Jabalia, da ya kasance mafi girma a Zirin Gaza, inda aka ruwaito mutuwar akalla mutum 20 tare da jikkata biyar.

    MDD ta kuma ce an lalata wata makaranta a sansanin ƴan gudun hijira na Al-Shati da ke kusa da tekun Bahar Rum, inda yaro ɗaya ya mutu. Dukkanin sansanonin na a arewacin Zirin Gaza.

    A wata sanarwa, MDD ta ce lamarin ya faru ne kwana biyu bayan samun ruwan bama-bamai a yankin.

    Ta ƙara da cewa: "A can kudanci, hare-hare sun shafi wasu makarantu biyu da suka koma wurin mafaka na sansanin Al Bureij. An ruwaito kisan mutum biyu da jikkata 31."

  8. Hotuna: Jana'iza da zanga-zanga a Isra'ila

    A can Isra'ila, ana ci gaba da jana'izar mutanen da aka kashe a yaƙi da ƙasar ke yi da Gaza.

    A ɗaya ɓangare kuma, ana gudanar da zanga-zanga, yayin da mutanen da aka yi garkuwa da ƴan uwansu ke ci gaba da roko don ganin Hamas ta sako su.

    Isra'ila

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Mutane sun taru a wajen jana'izar Sgt. Roi Daoui a yau Alhamis. Yana ɗaya daga cikin sojoji da aka kashe a wani samame ta ƙasa da Isra'ila ta kai Gaza
    Isra'ila

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Ana gudanar da jana'iza a faɗin Isra'ila yayin da mutanen da suka jikkata ke ƙaruwa
    Isra'ila

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Mutane daga Kfar Aza sun yi zanga-zanga kan ci gaba da riƙe mutanensu da Hamas ke yi
    Isra'ila

    Asalin hoton, EPA

    Bayanan hoto, Dakarun tsaron Isra'ila sun bayyana a safiyar yau cewa sun yi magana da iyalai 242 da ake garkuwa da ƴan uwansu a wuraren ɓuya da ke Gaza
    Isra'ila

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, An kaddamar da wani kamfe a birnin Jerusalem a yau Alhamis inda aka cika wani ɗakin taro da balan-balan da fostocin waɗanda Hamas tayi garkuwa da su
  9. Harin roka da Hamas ta kai Isra'ila ya jikkata mutum biyu

    Isra'ila

    Asalin hoton, Reuters

    Mutane biyu sun jikkata a garin Kiryat Shmona na Isra'ila kusa da iyaka da Lebanon bayan harin roka.

    Ƙungiyar Al-Qassam Brigade, wani ɓangare na Hamas, da ke aiki a Lebanon ta ce ta harba gomman rokoki a garin.

    Ɗaya daga cikin waɗanda aka jikkata ya kasance mai shekara 25 wanda yake samun kula, kamar yadda hukumar lafiya a Isra'ila ta faɗa wa kamfanin dillancin labarai na AFP.

    A ɗaya gefen, ƙungiyar Hezbollah ta ce ta yi amfani da jirage marasa matuki ɗauke da abubuwan fashewa wajen kai hari kan wani shingen sojojin Isra'ila a yankin Shebaa da ake tababa a kai da ke iyakar Lebanon da Isra'ila.

  10. Isra'ila ba ta yanke shawarar kai man fetur zuwa Gaza ba - Netanyahu

    Firaministan Isra'ila Benajamin Netanyahu ya ce har ygwamnatinsa ba ta yanke shawarar kai man fetur zuwa Gaza ba.

    Sai dai a wani taron manema labarai, Netanyahu ya ce gwamnatinsa na taimakawa da kayan agaji irinsu abinci da ruwa.

    "Ba mu yanke shawarar kai man fetur ba. Ban bayar da wani umarni ba," in ji shi.

  11. Majalisar wakilai ta yi watsi da buƙatar Tinubu ta sayen jirgin ruwan alfarma

    Bola Tinubu

    Asalin hoton, Bola Tinubu/Facebook

    Majalisar wakilan Najeriya ta cire kuɗi naira biliyan biyar da aka ware a cikin ƙaramin kasafin kuɗin ƙasar domin sayen jirgin ruwan shaƙatawa na shugaban ƙasa.

    Shugaban kwamitin majalisar kan kasafin kuɗ, Abubakar Bichi ne ya sanar da hakan yau Alhamis bayan sun amince da ƙaramin kasafin kuɗin na naira tiriliyan 2.17.

    Bichi ya shaida wa manema labaru cewa kwamitin ya mayar da kuɗn zuwa ɓangaren bashin karatu na gwamnatin tarayya, inda a yanzu kuɗin da aka ware wa bashin ya kai naira biliyan 10.

    Dama dai batun sayen jirgin ruwan shaƙatawan na shugaban ƙasa ya haifar da muhawara a tsakanin al'umma, inda mutane da dama suka soki lamarin.

  12. Mun kai wa bataliyar sojin Isra'ila Hari - Hezbollah

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Dakarun ƙungiyar Hezbollah sun bayyana cewa mayaƙansu sun samu nasarar kai hari da jiragensu biyu marasa matuƙa guda biyu waɗanda suka maƙare da bam a kan barikin Zabdin da ke yankin Shebaa.

    Wata sanarwa da Hezboollah ɗin ta fitar ta ce jiragen marasa matuƙa sun kai harin ne a daidai inda aka tsara.

    Wannan ne karo na farko da Hezbollah ta yi amfani da irin waɗannan bama-bamai wajen kai hari kan cibiyoyin sojin Isra'ila.

    Su kuma dakarun Isra'ila, a wani mataki na mayar da martani, suna harba makaman atilare zuwa kusa da wani gari da ke kan iyakar Lebanon.

  13. 'Yan bindiga sun tare hanyar Gusau tare da kashe matafiya

    .

    Asalin hoton, Getty Images

    Wani hari da ‘yan bindiga suka kai wa matafiya ranar Laraba da maraice a kan babbar hanyar da ke tsakanin Kucheri zuwa zuwa Gusau a jihar Zamfara, ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama.

    Baya ga salwantar rayukan fasinjoji, ‘yan bindigar sun kuma sace wasu ƙarin mutane.

    Daga cikin waɗanda harin ya rutsa da su har da tsohon ɗan majalisar wakilai ta tarayya daga jihar ta Zamfara, Alhaji Kabiru Classic.

    A hirarsa da Zubairu Ahmad Kasarawa, ya shaida masa yadda lamarin ya rutsa da su.

    Bayanan sautiLatsa hoton da ke sama domin sauraron rahoton
  14. Rodrygo ya tsawaita kwantiraginsa zuwa 2028 a Madrid

  15. CBN ya fara biyan bashin kuɗaɗen waje

    .

    Asalin hoton, CBN/FACEBOOK

    Babban Bankin Najeriya (CBN) ya fara biyan basukan kuɗaɗen ƙasashen waje da ake bin bankin.

    Inda wasu majiyoyi a bankin ke cewa tuni CBN din ya biya dala biliyan ɗaya a matakin farko.

    Mai magana da yawun CBN ɗin, Isah Abdulmumin, ya shaida wa kamfani dillancin labarai na Reuters cewa "bankin ya fara biyan wasu bankuna bashin da suke binsa, inda tuni ya biya bankuna 14", ba tare da ya bayyana adadin kuɗin ko sunayen bankunan da aka biya ba.

    Wasu majiyoyin bankin huɗu, sun ce an biya bankuna adadin kuɗaɗen da suka kai dala biliyan ɗaya, kuma za a ci gaba da biyan bashin cikin makonni masu zuwa.

    A yayin da aka biya wasu bankunan duka kudaɗen da suke bin bankin bashi, wasu bankunan an biya su kashi 80 na adadin bashin da suke bin CBN ɗin, kamar yadda wata majiya ta bayyana.

    Najeriya na da kusan bashin dala biliyan bakwai na kuɗaden ƙasar waje da ya kamata ta biya, da wasu hukumomi suka karɓa daga bankunan cikin gida.

    Biyan bashin na CBN na zuwa ne bayan sanarwar da ministan kuɗin ƙasar, Wale Edun, ya yi ranar 23 ga watan Oktoba cewa Najeriya na sa ran samun dala biliyan 10 don haɓaka kasuwar musayar kuɗaɗen wajen ƙasar.

    Hakan zai iya rage wa masu bayar da bashin na cikin gida, waɗanda ke faman ganin sun sama wa abokan hulɗarsu basuka, sakamakon matsalar ƙarancin dala da ake fuskanta a ƙasar.

    Sabon gwamnan Babban Bankin, Yemi Cardoso ya ce biyan basukan da ake bin bankin shi ne abin da zai fi bayar da fifiko, sai dai bai bayyana lokacin da za a yi hakan ba.

  16. Hotunan ɓarnar ambaliya ruwa a Birtaniya

    Mahaukaciyar guguwar Ciarán da ta auka Birtaniya ta ci gaba da shafar wasu yankunan ƙasar.

    Bishiyoyi da dama na ci gaba da tugewa a birnin Jersey sakamakon ambaliyar ruwar da ta auku, sanadiyyar guguwar.

    .

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Bishiyoyi sun yi ta tugewa a St Helier da ke Jersey
    v

    Asalin hoton, Jim

    Bayanan hoto, Guguwar ta haddasa mummunar ambaliya ruwa
    .

    Asalin hoton, PA Media

    Bayanan hoto, Ruwa ya cika wani fili da ke kusa da Exeter bayan da wani kogi a Clyst Saint Mary ya cika ya batse
    .

    Asalin hoton, Marc Cain

    Bayanan hoto, wata bishiya da ta faɗa kan wata mota tare da lalatata a Penzance da ke Cornwall
  17. Sojojin Bama sun ce sun rasa iko da wani gari a arewacin ƙasar

    Sojojin ƙasar Bama sun ce sun rasa iko a wani gari da ke arewacin ƙasar da ke kan iyaka da China bayan gwabza yaƙi tsakaninsu da ƙungiyoyin ƙabilu uku masu dauke da makamai wanda ke neman kafa ƙasa.

    Shugabannin mulkin soji na Myanmar sun bayyana cewa babu jami'an tsaro da sauran jami'an gwamnati a Chinshwehaw, mai matuƙar muhimanci ta fuskar kasuwanci a lardin Yunan na China.

    China ta yi kira da a tsagaita wuta. MDD ta ce ta damu matuƙa kan yawan mutanen da rikicin zai dai-daita.

  18. Mutane da dama sun tsallaka Masar daga Gaza

    Kusan 'yan ƙasashen waje 100 ne suka samu damar barin Gaza zuwa Masar ta mashigar Rafah, kamar yadda wani jami'in Falasɗinawa ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP.

    Kimanin baƙi 400 ne da ke riƙe da fasfo da Falasdinawa 60 da suka samu munanan raunuka ake sa ran za su fice daga Gaza a yau, Kamar yadda Wael Abu Mohsen ya bayyana wa AFP.

    Kamfanin dillancin labaran ya ce wannan adadi kaɗan ne daga cikin fiye da mutum miliyan biyu da ke zaune a Gaza.

  19. Motar MDD ta taka abin fashewa a Mali

    .

    Majalisar Dinkin Duniya ta ce ɗaya daga cikin motocinta na yaƙi a Mali ta taka wani abin fashewa ranar Laraba, tare da raunata jami'an kiyaye zaman lafiyarta takwas.

    Lamarin ya faru ne ranar a yayin da dakarun MDD ke janyewa daga arewacin Mali, bayan da a cikin watan Yuni shugabannin mulkin sojin ƙasar suka buƙace su da yin haka.

    Mali na ɗaya daga cikin ƙasashen da ke fama da rikice-rikicen masu iƙirarin jihadi a yankin Sahel.

    A ranar Talata ma jami'an MDD biyu ne suka samu ƙananan raunuka a wasu hare-hare.

    Hukumomin Mali na na ƙorafin cewar ba su samu damar mallakar sansanonin dakarun na MDD da ke ficewa ba, inda tuni 'yan tawaye suka mamaye wasu daga ciki.

    Ficewar dakarun na MDD ta janyo rikici a arewacin ƙasar, yayin da 'yan tawaye da dakarun gwamnati da kuma masu iƙirarin jihadi ke faɗa don ƙwatar ikon yankin arewacin ƙasar.

    Yankin Sahel ya kasance sansanin kashe-kashen da ke da alaka ta ta'addanci.

    Inda ƙungiyoyin masu tayar da ƙayar baya da ke da alaƙa da Al-Qaeda da IS suka kwashe fiye da shekara 10 suna kai hari kan fararen hula da sojojin gwamnati.

  20. Labarai da dumi-dumi, Mutanen da suka mutu a Gaza sun zarta 9,000

    Ma'aikatar lafiyar Hamas da ke iko da Gaza ta ce mutum 9,061 ne aka kashe a Zirin Gaza, tun bayan fara wannan yaƙin ranar 7 ga watan Oktoba.

    Wannan ya haɗar da ƙananan yara 3,760, kamar yadda ma'aikatar lafiuar ta ce.

    Ta kuma ƙara da cewa fiye da mutum 32,000 ne suka jikkata sakamakon rikicin.