Boko Haram ta kashe aƙalla mutum 40 a Yobe - Ƴan sanda

Wannan shafi ne da ke kawo mu ku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

A'isha Babangida and Umar Mikail

  1. Sai da safe

    Mun kawo ƙarshen rahotonni a wannan shafi.

    Kada ku manta muna nan tafe da wasu sababbi gobe da safe idan Allah ya kai mu.

    Kuna iya duba ƙasa domin karanta labaran da muka wallafa a yau Laraba. Umar Mikail ke cewa mu zama lafiya.

  2. Harin Isra'ila kan sansanin Jabalia zai iya zama laifin yaƙi - MDD

    Jabalia

    Asalin hoton, EPA

    Bayanan hoto, Harin na Isra'ila a sansanin Jabalia ya kashe kusan mutum 100

    Ofishin kare haƙƙi na MDD ya wallafa saƙo a dandalin X, wanda aka sani da Twitter a baya, game da harin Isra'ila kan sansanin 'yan gudun hijira na Jabalia ranar Talata.

    "Ganin yawan fararen hular da aka kashe da kuma girman ɓarnar da aka yi a sansanin Jabalia, muna da damuwa babba cewa wannan hari ne kan mai tsautsayi da zai iya zama laifin yaƙi," a cewar hukumar kare haƙƙi ta MDD.

    A jiya ne jiragen yaƙin Isra'ila suka kai munanan hare-hare kan sansanin da yamma.

    Hotunan da aka ɗauka sun nuna mummunar ɓarnar da aka yi, inda bama-bamai suka haƙa ramuka kuma ɓaraguzai da ƙarafa suka zagaye wurin baki ɗaya.

    Kusan mutum 100 aka kashe a harin, ciki har da ƙananan yara.

    Isra'ila na cewa ta kashe wani babban kwamandan Hamas a sansanin tare da lalata hanyar ƙarƙashin ƙasa da ƙungiyar ke amfani da ita.

    Ta kuma ce tana bincike kan rahotonnin "ɓarna da kuma kisan fararen hula da aka yi".

  3. Sojojin Isra'ila da aka kashe a Gaza sun kai 16, in ji ta

    An sake kashe wani sojan Isra'ila a yau Laraba, a cewar rundunar sojin ƙasar ta Israel Defense Forces (IDF).

    A cewar bayanan da ta wallafa a shafinta na intanet, an kashe 15 a ranar Talata.

  4. Yadda aka yi jana'izar wasu sojojin Isra'ila da aka kashe a Gaza

    Rundunar sojin Isra'ila ta ce sojojinta 15 ne aka kashe a yayin hare-haren da suka kai Zirin Gaza.

    Tuni iyalai da 'yan uwa suka jana'izar wasu daga cikinsu a birane daban-daban na Isra'ilar.

    Isra'ila

    Asalin hoton, Getty Images

    Isra'ila

    Asalin hoton, Getty Images

    Isra'ila

    Asalin hoton, Getty Images

    Isra'ila

    Asalin hoton, Getty Images

  5. Jordan ta janye jakadanta daga Isra'ila don yin tir da hare-hare a Gaza,

    Ayman Safadi

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Ministan Harkokin Wajen Jordan Ayman Safadi ne ya ba da umarnin dawo da jakadanta gida da kuma korar na Isra'ila

    Ƙasar Jordan ta ɗauki matakin da ta kira martaninta kan yaƙin da Isra'ila take yi a Zirin Gaza ta hanyar janye jakadanta daga Isra'ila.

    Wata sanarwa ta ce Mataimakin Firaminista kuma Ministan Harkokin Wajen Jordan Ayman Safadi ne ya ba da umarnin janye jakadan "don nuna ɓacin ran Jordan kan tashin hankalin da ke faruwa a Gaza".

    Ranar Lahadin da ta wuce, Safadi ya faɗa wa BBC yayin wata hira cewa Jordan "za ta yi duk abin da za ta iya a lokacin da ya dace, duk abin da muke ganin zai taimaka a yaƙin nan, za mu yi shi".

    Jordan ce ƙasar Larabawa ta farko da ta ɗauki irin wannan mataki.

    Kamar Masar, wadda ita ma ƙulla yarjejeniyar zaman lafiya da Isra'ila, har ma da wasu Larabawan da suka gyara alaƙa da ita, Jordan na da ofishin jakadanci a birnin Tel Aviv na Isra'ila.

    Haka nan ƙasar ta faɗ wa jakadan Isra'ila, wanda ya bar birnin Amman mako biyu da suka wuce saboda zanga-zanga, cewa kada ya koma.

    Sanarwar ta Jordan ta fayyace cewa komawar jakadan Isra'ila ƙasar "ya dogara ne idan yadda Isra'ilar ta dakatar da hare-hare a Gaza".

    Ta kuma bayyana damuwarta kan "matsananciyar rayuwa da ake ciki" a Gaza.

  6. Boko Haram ta kashe aƙalla mutum 40 a Yobe - Ƴan sanda

    Boko Haram

    Asalin hoton, Getty Images

    Rundunar 'yan sandan Najeriya reshen jihar Yobe ta ce wasu da ake zargin mayaƙan Boko Haram ne sun halaka aƙalla mutum 40 a jihar da ke arewa maso gabashin ƙasar tsakanin ranakun Litinin da Talata.

    Sun ce mayaƙan sun riƙa harbin mutane da bindiga da kuma jefa masu bam.

    Ana ganin cewa wannan shi ne wani hari mafi muni da aka kai a jihar cikin wata 18.

    Ƴan sintiri da ke aikin samar da tsaro a yankin sun ce mayaƙan na Boko Haram sun kai musu harin ne bayan da mazauna ƙauyukan suka ƙi biyan kuɗaɗen harajin da ƴan bindigar suka ƙaƙaba musu.

    Mai magana da yawun 'yan sandan Yobe ya faɗa wa BBC Hausa cewa maharan sun fara kai hari ne ranar Talata tare da kashe gomman mutane a yankin ƙaramar hukumar Geidem.

    'Yan bindigar sun sake far wa masu zaman makoki a ranar Laraba, inda nan ma suka kashe mutane da yawa.

    Ya ce har yanzu ba su kai ga tattara alƙaluman waɗanda aka kashe ba, amma mazauna yankin na cewa adadinsu ya kai kusan 40.

    Sau da dama gungun ƴan bindiga a wasu ƙauyukan Najeriya kan nemi mazauna yankunan su biya haraji a wani yunƙuri na tabbatar da ikonsu.

  7. Asamoah Gyan zai biya tsohuwar matarsa diyya

  8. Majalisar Dattijawan Najeriya ta amince Tinubu ya ciwo bashin dala biliyan 7.8

    ...

    Asalin hoton, X/President of the Senate

    Majalisar Dattawan Najeriya ta amince da dala biliyan 7.8 da kuma yuro miliyan 100 a matsayin kuɗin da Shugaba Bola Tinubu zai ciyo bashi.

    Shugaban ya rubuta wa Majalisar wasiƙa yana neman amincewarta game da ciyo bashin a tsarin rance na 2022 zuwa 2024 don kammala wasu ayyuka.

    Kazalika, Shugaban Majalisa Godswill Akpabio ya sanar da buƙatar Tinubu ta neman amincewa da mutanen da yake son naɗawa a matsayin kwamishinonin hukumar zaɓe ta ƙasa.

    Majalisar ta amince da naɗin kwamishinoni bakwai a zaman nata na yau Laraba.

  9. Adadin mutanen da suka tsallaka Masar daga Gaza ya kai 400

    Mun samu ƙarin bayani game da adadin mutanen da suka fice daga Zirin Gaza ta mashigar Rafah zuwa Masar a yau.

    Hukumomin Falasɗinu sun ce mutum 76 da ke ɗauke da raunuka ne suka tsallaka iyakar, da kuma 335 da ke riƙe da fasfo ɗin ƙasashen waje.

    Wannan ya kawo jimillar adadin zuwa 400.

  10. Yawan sojojin Isra'ila da aka kashe alama ce ta abin da zai faru nan gaba,

    Gaza

    Asalin hoton, EPA

    Bayan harin da Isra'ila ta kai kan sansanin Jabalia a jiya Talata, batun shi ne ko ya yi daidai da abin da take so ta cimma - ma'ana kisan gomman Falasɗinawa.

    Da tsakar daren jiya, na yi magana da wani likitan fiɗa a asibitin da ke kusa da sansanin, wanda ya ce sun karɓi mutum kusan 400. Kusan 120 daga cikinsu ko dai sun mutu lokacin da suka isa ko kuma 'yan mintuna kaɗan suka rage kafin su mutu.

    Isra'ila ta ce ta kai hari 11,000 kan Gaza tun bayan fara yaƙin. Yanzu ina kudancin Isra'ila a kusa da iyakar Gaza, kuma tsawon kwanaki, babu abin da nake ji sai ƙarar makaman atilare kusan a kodayaushe.

    Rundunar sojin Isra'ila (IDF) ta ce an kashe sojojinta 15. Ina ganin wannan alama ce ta abin da zai faru nan gaba, saboda har yanzu ba su shiga lungunan Birnin Gaza ba tukunna - wanda abu ne mai cike da ƙalubale.

    IDF na matsawa kusa da birnin amma dai har yanzu suna ƙauyukan da ke kusa da shi.

    'Yan kwanakin da suka wuce, mayaƙan Hamas sun yi wa dakarun IDF kwanton-ɓauna bayan sun shiga wata mota mai silke da aka ce ta zamani ce wadda ake ganin ba za a iya lalata ba, amma sai ga shi an yi kaca-kaca da ita da makamin harbe tanka ƙirar Rasha.

  11. Zuwa yanzu fiye da mutum 320 ne suka tsallaka Masar daga Gaza

    Masar

    Asalin hoton, EPA

    Bayanan hoto, Wata motar ɗaukar marasa lafiya ke nan take shiga asibitin Masar a yau Laraba bayan ta tsallaka daga Gaza ɗauke da mutanen da suka rauni

    Mutane na ci gaba da tsallaka iyakar Zirin Gaza zuwa cikin Masar.

    Zuwa yanzu aƙalla 'yan ƙasar waje 320 ne suka tsallaka iyakar, a cewar hukumomin Masar da kuma jami'an tsaro, kamar yadda kamfanin labarai na Reuters ya ruwaito.

    Wasu mutum 76 kuma da aka jikkata a yaƙin sun samu tsallakawa su ma, in ji wani jami'in gwamnatin Masar cikin rahoton AFP.

  12. Mun tsare shugaban NLC Joe Ajero ne don kare rayuwarsa - Ƴan sanda

    ..

    Asalin hoton, X/Nigeria Police Force

    Rundunar ƴan sandan Najeriya a jihar Imo ta musanta rahotannin da ke zargin jami'anta da kama shugaban ƙungiyar ƙwadago ta Najeriya, Kwamared Joe Ajero a garin Owerri.

    A cikin wata sanarwa da ta fitar ta hannun jami'in hulɗa da jama'a na rundunar a jihar Imo, ASP Okoye Henry, ta ce ta tafi da shi ne "domin tsare rayuwarsa".

    Sai dai ƙungiyar ƙwadagon ta ce jami'an tsaro sun kama shugaban nata ne bayan ya isa jihar ta Imo da ke kudu maso gabashin ƙasar.

    "Daga cikin abubuwan da Mista Ajaero ya je yi Imo akwai shirya babbar zanga-zanga da tsayar da aiki cak a filin jirgin sama, kuma a wajen yunƙurin yin hakan ne wasu ma'aikata suka nuna rashin amincewa kuma wani dandazon jama'a ya kai masa hari," in ji ASP Henry.

    "Bayan mun samu labari, sai rundunar 'yan sandan Imo ta tura dakarunta kuma jagoran tawagar ya ɗauki shugaban na NLC zuwa hedikwatarta don tabbatar da kare rayuwarsa daga maharan."

    Sanarwar ta ƙara da cewa "daga nan sai kwamishinan 'yan sanda ya bayar da umarnin kai shi asibitin 'yan sanda don duba lafiyarsa...kuma aka ba shi cikakken tsaro don ci gaba da harkokinsa".

    Sai dai kuma, rundunar ta jaddada cewa ya kamata a yi la'akari da hukuncin kotun ɗa'ar ma'aikata da ta hana NLC gudanar da zanga-zangar a ranar 27 ga watan Oktoba.

  13. Labarai da dumi-dumi, Isra'ila ta ce an kashe dakarunta 15 a Zirin Gaza

    Rundunar sojin Isra'ila ta sanar cewa an kashe dakarunta 15 tun daga ranar Talata yayin hare-haren da take kaiwa ta ƙasa a Zirin Gaza.

    Wannan adadi ƙari ne a kan 11 da rundunar ta ce an kashe mata tun da farko.

    Dakarun 11 da aka kashe dukkansu 'yan shekara 18 ne zuwa 20.

  14. Kotun Iran ta yanke wa matar aure hukuncin kisa bisa laifin 'bin maza'

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Kafofin yaɗa labarai a Iran sun ruwaito cewa kotu a birnin Tehran ta yanke wa wata mata hukuncin kisa bayan kama ta da laifin "cin amanar mijinta."

    Bayanai sun ce mutumin mai suna Parham ya gano cewa matar tasa tana hulɗa da wasu maza ne bayan ya sanya kyamarar tsaro ta CCTV a gidansa.

    Ma'auratan biyu sun kwashe shekara 10 a tare.

    Mutumin ya ce bayan sanya kyamarori a gidansa sai ya rinƙa ganin wasu maza suna shige da fice a gidan a lokacin da ba shi nan.

    A lokacin da aka tuhume ta, matar ta ce ta shiga halin neman maza ne saboda "kaɗaici", kuma bayanai sun nuna cewa takan gabatar da kanta ga mutane a matsayin mai horas da wasannin motsa jiki.

    Ɗaya daga cikin mazan da ta nema ya bayyana cewa "bai ga wata alama da ta nuna cewa matar tana da aure ba." Kotun ta yanke wa mutumin hukuncin bulala.

  15. Osimhen na cikin 'yan takarar gwarzon ɗan ƙwallon Afirka na 2023

  16. Kasar Bolivia ta yanke hulda da Isra'ila a kan yakin Gaza

    Gaza

    Asalin hoton, Reuters

    Bolivia ta zama kasar Latin Amurka ta farko da ta yanke huldar diflomasiyya da Isra'ila a kan abin da ta bayyana da "takalar fada da amfani da matakin soja na fin karfi" a Gaza.

    Kasar ta yi kiran a tsagaita wuta kuma ta ce za ta aika kayan agaji zuwa Zirin Gaza da aka yi wa kofar rago.

    Wani jami'in Isra'ila ya ce matakin tamkar "ba da kai ne ga ta'addanci".

    Lior Haiat ya soki lamirin gwamnatin Bolivia da "alakanta kanta da kungiyar Hamas ta 'yan ta'adda".

    Mataimakin ministan harkokin wajen Bolivia Freddy Mamani ya ce gwamnati ta yanke shawarar katse alakar ne "don nuna kin amincewa da kuma yin alla-wadai da matakin amfani da karfin soja na fin karfi da takalar fada a Zirin Gaza".

    Ya kara da cewa kasarsu na son kawo karshen kofar ragon da Isra'ila ta yi wa Gaza da hana "shigar da abinci da ruwa da kuma sauran muhimman kayan bukatun rayuwa".

    Sojojin Isra'ila sun yi wa Gaza tsinke tsawon makonni, inda muhimman kayan agaji ke shiga Zirin jefi-jefi ta hanyar iyakar Rafah daga kasar Masar kawai.

    "Isra'ila ta yi alla-wadai da goyon bayan ta'addancin da Bolivia ta yi da kuma karbar gwamnatin kasar Iran, abin da ke nuni da akidojin gwamnatin Bolivia," a martanin Mista Haiat.

    Ana zargin Iran da bai wa Hamas goyon baya wajen kai hare-haren ranar 7 ga watan Oktoba.

    Sai dai yayin da shugabannin Iran suka nuna murna tare da yabawa 'yan bindigan da suka haddasa tarzomar, amma dai sun musanta hannu a lamarin.

    Ba Bolivia ce kasar Latin Amurka da ta fara daukar matakan diflomasiyya a kan Isra'ila ba.

    • Yadda gawawwaki suka mamaye asibitocin Gaza
    • Ko sauran ƙasashe za su iya shiga yaƙin Gaza da Isra'ila?

    Shugaban Chile, Gabriel Boric a ranar Talata ya yi wa jakadan kasarsa da ke birnin Tel Aviv kiranye don gudanar da tuntuba "bisa la'akari da keta dokokin jin kai na duniya, wanda ba za a yarda da shi ba, da Isra'ila ke aikatawa a Zirin Gaza."

    "Chile cikin kakkausar murya ta yi alla-wadai kuma ta nunar da gagarumar damuwa cewa wadannan matakan amfani da karfin soja - wanda a wannan mataki ya kunshi ladabtar da daukacin al'ummar Falasdinawa fararen hula a Gaza," kamar yadda ya rubuta a shafin X, wanda a baya ake kira Twitter.

    Shugaban Colombia ma Gustavo Petro ya ba da irin wannan sanarwa a shafin sada zumunta.

  17. An kama shugaban ƙungiyar ƙwadago ta Najeriya a Imo

    ...

    Asalin hoton, Joe Ajaero/Facebook

    An kama shugaban kungiyar kwadago ta Najeriya (NLC), Joe Ajaero a Owerri, babban birnin jihar Imo.

    Rahotanni sun ce ƴan sanda ne dauke da makamai suka kama Ajaero a Sakatariyar ƙungiyar NLC a Owerri lokacin da yake shirin jagorantar wata zanga-zanga da aka shiya gudanarwa a yau.

    Wani babban jami'in ƙwadago a Najeriya, kwamared Nuhu Toro ya tabbatar da rahoton kama Joe Ajaero ga BBC.

    Ya ƙara da cewa mutanen da suka kama jagoran ƴan ƙwadagon na Najeriya sun je ne da kakin ƴan sanda inda suka yi awon gaba da shi.

    Kungiyar NLC na jagorantar zanga-zanga da yajin aiki a jihar Imo saboda abin da ta bayyana, a matsayin rashin mutunta haƙƙin ma’aikata da rashin biyan albashi da fansho da dai sauransu.

    • Ƙarin ƙungiyoyin ƙwadago a Najeriya sun ci alwashi shiga yajin aiki
    • Abu bakwai da gwamnatin Najeriya ta cimma da 'yan ƙwadago
  18. 'Matsalar ƙarancin abinci mai gina jiki ga yara ta ƙaru da kashi 160 a Najeriya'

    ...

    Asalin hoton, AFP

    Bayanan hoto, ...

    Wata kungiya mai zaman kanta, FHI 360, ta yi gargadi game da karuwar matsalar karancin abinci a tsakanin yara ‘yan ƙasa da shekara biyar a arewa maso gabashin Najeriya.

    Ta ba da rahoton cewa an samu tashin hankali sosai, inda yara 15,781 ke fama da rashin abinci mai gina jiki tsakanin watan Fabrairu da Satumba, wanda ya nuna kusan karuwar kashi 160 idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata.

    An bayyana lamarin a matsayin mai tsanani, kuma ana bukatar karin tallafi cikin gaggawa don magance matsalolin lafiya da abinci mai gina jiki, musamman ga mata da yara a yankin.

    Asusun kula da yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya ce Najeriya ce ƙasa ta biyu a duniya wajen fuskantar matsalar rashin abinci mai gina jiki musamman a yankin arewacin ƙasar.

    Yayin da kimanin yara miliyan biyu a Najeriya ke fama da matsalar rashin abinci mai gina jiki, kashi 20 cikin 100 ne kawai ke karɓar magani.

    Bayanai daga UNICEF sun kuma nuna cewa rashin abinci mai gina jiki na da matukar tasiri ga kashi 45 cikin 100 na mace-macen yara a Najeriya a tsakanin ‘yan kasa da shekaru biyar.

    • Miliyoyin mutane na kwana ba su ci abinci ba a Nijar - Hukumar Abinci
    • Yunwa na ƙara ta'azzara a arewa maso gabashin Najeriya - ICRC
  19. Labarai da dumi-dumi, 'Yan ƙasashen waje 110 sun shiga Masar bayan buɗe iyakar Gaza

    Aƙalla ƴan ƙasashen waje110 sun tsallaka zuwa Masar daga Gaza bayan buɗe iyakar Rafah.

    BBC ta ruwaito cewa aƙalla Falasɗinawan da suka jikkata 20 sun riga sun tsallaka zuwa Masar.

    Ana sa ran kusan majinyata Falasdinawa 80, da kuma wasu 'yan kasashen waje guda 500, za su bar Gaza zuwa Masar a yau.

    • Abin da Isra'ila take lissafawa kafin ta auka wa Gaza
    • Rikicin Gaza na rura wutar tunzuri a manyan makarantun Amurka
  20. Batun sayen motocin alfarma na Remi Tinubu na tayar da ƙura a Najeriya