Hamas ta saki ƙarin 'yan Isra'ila biyu da ta yi garkuwa da su

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya,

Rahoto kai-tsaye

Ibrahim Yusuf Mohammed, Haruna Kakangi and Umar Mikail

  1. Sai da safe

    Mun zo ƙarshen rahotonnin a wannan shafi na labarai kai-tsaye a yau Litinin.

    Kuna iya ci gaba da dubawa ƙasa don karanta rahotonnin da muka kawo daga sassan duniya, musamman na halin da ake ciki a Zirin Gaza da Isra'ila.

    Umar Mikail ne da Mukhtar Bawa ke fatan mu kwana lafiya.

  2. Hare-hare sun raba mutum 19,000 da gidajensu a Lebanon

    Lebanon

    Asalin hoton, EPA-EFE/REX/Shutterstock

    Majalisar Dinkin Duniya (MDD) ta ce fiye da mutum 19,000 ne aka raba da muhallansu a kudancin Lebanon a ci gaba da fafatawa tsakanin dakarun Hezbollah da na Isra'ila a kan iayaka.

    Ƙungiyar mayaƙan Hezbollah mai samun goyon bayan Iran ta harba makamai masu linzami da rokoki zuwa Isra'ila amma makaman suka yi kome zuwa sansanonin mayakanta.

    Isra'ila ta kwashe jama'a da dama daga garuruwan da ke kan iyakar kasashen biyu.

    Firaministan Israila Benyamin Netanyahu ya gargaɗi mayaƙan Hezbollah cewa Isra'ila "za ta mayar da martani fiye da zaton kungiyar" idan har ta ci gaba da taya Hamas a yakin da take yi.

  3. Firaminista za ta yi yajin aiki saboda bambancin albashi tsakanin maza da mata a Iceland

    Iceland prime minister

    Asalin hoton, Reuters

    Dubun dubatar mata ne a Iceland, ciki har da Firaministan kasar Katrín Jakobsdóttir, za su kauracewa aiki a ranar Talatar nan.

    Yajin aikin mai taken "kvennafri", ko kuma ranar yajin aikin mata, an tsara gudanar da shi ne, don nuna adawa da bambancin da ake nuna wa mata wajen biyan albashi a wuraren aiki idan an kwatanta da takwarorinsu maza da kuma cin zarafin jinsi.

    Bangarorin da mata ke da rinjayen ma'aikata, kamar kula da lafiya da ilmi ne yajin aikin zai fi shafa.

    Kauracewa aikin da aka tsara zai kasance yajin aiki na tsawon wuni guda da mata suka yi tun cikin 1975.

    An bukaci mata da mutanen da ke kiran jinsinsu ba maza ba-ba kuma mata ba, su kauracewa duk wani aiki a ranar Talata ciki har da ayyukan gida.

    "Ba zan je aiki ba ranar, kamar yadda nake sa ran duk matan [da ke cikin majalisar ministoci] za su yi su ma," Firaministar Iceland Misis Jakobsdóttir ta fada wa jaridar intanet ta mbl.is.

    Ta ce gwamnatinta na duba yiwuwar yadda za a rika darjanta bangarorin ayyukan kwarewa da mata suka yi kaka-gida, kamar yadda ake yi wa takwarorinsu maza.

    A cewar kungiyar malamai ta Iceland, mata ne mafi yawa a tsakanin malaman makaranta a dukkan matakan ilmi na kasar ciki har da malaman makarantun renon yara inda suke da kashi 94 cikin 100.

  4. An kama matasa 76 da suka halarci taron 'auren jinsi' a jihar Gombe

    Jami’an tsaron farar hula da ba da agaji na Civil Defense a Najeriya sun ce sun daƙile shirin da wasu matasa suka yi na gudanar da abin da ta ce auren 'yan luwadi ne a jihar Gombe.

    Rundunar ta bayyana cewa jami'anta sun kama matasa kimanin 76 waɗanda suka taru a harabar wata kasuwar zamani da ake kira Duwa Plaza domin gudanar da bikin.

    Kwamandan hukumar a Gombe, Mohammed Muazu, ya faɗa wa BBC Hausa cewa sun haɗa taron murnar zagayowar ranar haihuwa ne tukunna, inda za su yi bikin auren daga baya.

    Ya ƙara da cewa babu wanda ya kai shekara 25 a cikin matasan. Sai dai bai yi bayani ba ko dukkansu maza ne.

    Latsa hoton ƙasa ku saurari rahoton Zubairu Ahmad Kasarawa:

    Bayanan sautiLatsa hoton sama ku saurari rahoton Zubairu Ahmad Kasarawa:
  5. Matan da Hamas ta saki na da shekara 79 da 85

    'Yan Isra'ila

    Asalin hoton, Reuters

    Kafofin yaɗa labarai a Isra'ila sun bayar da ƙarin bayani kan mata dattijai biyu da Hamas ta saki bayan ta yi garkuwa da su a Isra'ila ranar 7 ga watan Oktoba.

    Hamas ta saki Nurit Cooper mai shekara 79, da Yocheved Lifshitz mai shekara 85 a yammacin yau bayan Masar da Ƙatar sun shiga tsakani.

    Ta ce ta sake su ne "bisa dalilai na jin-ƙai" da kuma "kula da lafiyarsu".

    Sai dai ɓangaren soji na ƙungiyar da ake kira Bataliyar Qassam ya ce tun ranar Juma'a ya nemi ya sake su amma Isra'ila ta ƙi yarda ta karɓe su.

    Kafofin yaɗa labarai a Masar sun ce matan sun kai mashigar Rafah da ta haɗa ƙasar da Zirin Gaza, inda aka shigar da kayan agaji a baya-bayan nan.

  6. Labarai da dumi-dumi, Red Cross ta tabbatar da sakin 'yan Isra'ila da Hamas ta yi

    Ƙungiyar agaji ta Red Cross ta tabbatar da sakin ƙarin 'yan Isra'ila biyu da Hamas ta ce ta yi a yammacin yau Litinin, tana mai cewa ita ce ta taimaka wajen sakin nasu.

    Cikin wata sanarwa a dandalin X, wanda aka fi sani da Twitter a baya, ƙungiyar agajin ta ce "rawar da muka taka a matsayin masu shiga tsakani da ba su goyon bayan kowane ɓangare ne ya ba da damar yin hakan kuma za mu ci gaba da taimakawa wajen sakin wasu".

    "Muna fatan za su haɗu da iyalansu nan gaba kaɗan."

  7. Labarai da dumi-dumi, Hamas ta ce ta saki ƙarin 'yan Isra'ila biyu

    Ɓangaren soji na ƙungiyar Hamas, Bataliyar Qassam, ya sanar da sakin ƙarin mutum biyu da suka yi garkuwa da su daga Isra'ila, Nurit Yitzhak da Yocheved Lifshitz, bayan shiga tsakani da ƙasashen Masar da Qatar suka yi.

    Zuwa yanzu dai ba a tabbatar da labarin ba, amma cikin saƙon da ta wallafa a dandalin Telegram, Hamas ta zargi "abokan gaba" - wato Isra'il - da ƙin amincewa su karɓe su tun ranar Juma'a.

    "Mun yanke shawarar sakin su saboda dalilai na jin-ƙai da kuma kula da lafiyarsu," a cewarta.

    A ranar Juma'a, Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya kira tayin da Hamas ta yi cewa "farfagandar Hamas ce".

    Idan aka tabbatar da wannan labari, adadin waɗanda aka saki zuwa yanzu sun zama huɗu cikin adadin da aka sani na 222. Amurkawa 'yan Isra'ila, uwa da 'yarta, an sake su ranar Juma'a.

  8. Allah ya yi wa Bobi, karen da ya fi tsufa a duniya rasuwa

    Bodi

    Asalin hoton, Guinness World Records

    Kare mafi tsufa da ya taba rayuwa a duniya ya mutu yana da shekara 31 da kwana 165.

    Karen mai suna Bobi wanda ya shiga kundin tarihi na Guinness World Record, irin Rafeiro do Alentejo, ya mutu ne a gidansa da ke Portugal ranar Asabar.

    Wani likitan dabbobi ne da ya sha haduwa da Bobi ne yaba da sanarwar mutuwar tasa a shafin sada zumunta.

    "Duk da yake karen ya zarce sauran karnukan da aka sani a tarihi tsawon rai, kwana 11,478 da ya yi a doron duniya, ba su isa ba, ga wadanda ke kaunar Bobi," Dr Karen Becker ya rubuta.

    Bobi ya zama kare mafi tsufa da ke raye a duniya da kuma karen da ya fi dadewa a rayuwa a watan Fabrairu - inda ya shafe tarihin tsawon kusan shekara 100 na wani kare mafi dadewa.

    Karen da ya fi dadewa a baya shi ne wani mai suna Bluey na kasar Australia, wanda ya mutu a 1939 yana da shekara 29 da wata biyar a duniya.

    Cibiyar tattara bayanai a kan dabbobin shakuwa ta gwamnatin Portugal wadda kungiyar likitocin dabbobi ke tafiyarwa ce ta tantance shekarun Bobi.

    Har yanzu dai ba a bayyana sunan da ya gaji Bobi a matsayin kare mafi tsufa a duniya ba.

    Bobi and a cat

    Asalin hoton, GUINNESS WORLD RECORDS

    Bayanan hoto, Wani bangare na sirrin tsawon ran Bobi, an ce yana da alaka da muhalli mai cike da kwanciyar hankali da ya rayu a ciki

    Bobi ya rayu ne tsawon zamansa a duniya a hannun wani iyalin Costa a kauyen Conqueiros, kusa da gabar tekun yammacin Portugal.

    Leonel Costa, wanda yake da shekara takwas a lokacin da aka haifi karen, ya ce iyayensa sun mallaki dabbobi masu yawa amma suka yi ta rabu da su, ko da yake shi Bobi ya tsallake rijiya da baya.

    Leonel da dan'uwansa sun bar maganar rayuwar Bobi cikin sirri daga iyayensu har zuwa lokacin da aka sake gano shi tare da mayar da shi cikin iyali, wadanda suka rika ciyar da shi irin abincin da suke ci.

  9. Kalli yadda ake ƙarancin likkafani a Zirin Gaza

    Bayanan bidiyo, Latsa hoton sama ku kalli bidiyo:

    Wakilin BBC a Gaza ya ga yadda ake tururuwar kai waɗanda suka mutu da waɗanda suka ji raunuka zuwa asibitocin Gaza sakamakon hare-haren Isra'ila.

    Lamarin ya kai ga asibitocin ba su da wurin ajiye gawawwakin, yayin da kuma ake ƙarancin likkafanin yi musu sutura.

    Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce kashi 60 cikin 100 na waɗanda aka kashe a yaƙin mata ne da ƙananan yara.

    Ma'aikatar lafiyar Zirin Gaza da Hamas ke iko da ita ta ce mutanen da Isra'ila ta kashe zuwa yanzu sun zarta 5,000, yayin da Isra'ila ta ce harin Hamas ɗin ya kashe 1,400 a ƙasarta.

  10. Rahotanni na cewa Amurka ta nemi Isra'ila ta jinkirta mamaye ta ƙasa, Barbara Plett Usher Wakiliyar BBC a Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka

    Kafofin yada labaran Amurka na ba da rahoton cewa gwamnatin Joe Biden ta nemi Isra'ila ta jinkirta kaddamar da mamaye ta kasa a Gaza, don bayar da lokaci ga tattaunawar neman sako mutanen da ake garkuwa da su.

    Sakin mata Amurkawa biyu da Hamas ke garkuwa da su a karshen makon jiya, ya ingiza kokarin neman a gaggauta tattunawa a kan fiye da mutum 200 da ake garkuwa da su.

    Akwai adadin sauran Amurkawa da ke cikin wadanda ake yin garkuwar da su, kuma Sakataren Wajen Amurka Antony Blinken ya ce a karshen mako ne Amurka ta “tsananta kokari” wajen ganin an dawo da su gida, “ta hanyar amfani da kowanne irin dama, abokan kawance da alakar da muke da ita.”

    Yayin da muke kawo muku rahotanni, wata majiya mai alaka da ci gaban da ake samu a tattaunawar neman a sako wadanda ake garkuwar da su ya fada wa BBC cewa tattaunawar neman a sako karin 'yan kasashen waje kimanin 50 da kuma fararen hula masu shaidar zama 'yan kasa biyu ta shiga wani muhimmin mataki.

    Akwai gagarumar damuwa da ke karuwa a kan cewa mamayen kasa na sojojin Isra'ila a Gaza zai haifar bazuwar yaki.

    'Yan Isra'ila dai na musanta rahotannin cewa an nemi su jinkirta mamaye, sai dai a bayyane take karara cewa Amurkawa na shawartar su, a kan su yi hakan.

  11. 'Tattaunawar neman sakin mutanen da Hamas ke garkuwa da su ta yi nisa'

    'Yan Isra'ila

    Wata majiya da ke cikin tawagar da ke neman kuɓutar da mutane da ƙungiyar Hamas ke garkuwa da su ta ce tattaunawar ta shiga "mataki mai muhimmanci".

    Wakilin BBC a Gaza Rushdi Abualouf ya ce majiyar ta faɗa masa cewa tattaunawar da ƙasar Qatar ke shiryawa wadda kuma Amurka ke ciki na ƙoƙarin ɗorawa kan nasarar da aka samu ranar Juma'a ta sakin Amurka biyu.

    An ce Hamas na nuna "yiwuwar sakin" ƙarin fararen hula 50 da kuma wasu 'yan ƙasar waje a madadin tsagaita wuta da kuma shigar da ƙarin kayan agaji cikin Gaza.

    Sai dai majiyar ta ce kafewar da Isra'ila ta yi kan cewa babu maganar tsagaita wuta na jawo ci baya a tattaunawar.

  12. An tuhumi direban jirgi da yunƙurin rikito da shi a Amurka

    Jirgin Alaska Airlines

    Asalin hoton, Getty Images

    An tuhumi wani matuƙin jirgin sama da ba ya kan aiki da laifi 83 na yunƙurin kisan kai, bayan ya yi ƙoƙarin rikito da wani jirgin fasinja ana tsaka da tafiya ranar Lahadi da dare a Amurka.

    Wanda ake zargin yana zaune ne a kusa da direban da ke tuƙa jirgin Alaska Airlines, a cewar wata sanarwa daga kamfanin jirgin.

    'Yan sanda sun bayyana wanda ake zargin da suna Joseph David Emerson mai shekara 44.

    Jirgin ya tashi daga Everett a birnin Washington zuwa San Francisco, California ɗauke da fasinja 80.

    An karkatar da jirgin zuwa Portland, Oregon bayan an naɗe mutumin ba tare da hatsaniya ba, in ji hukumomi.

  13. Najeriya ta yi nasara a shari'ar da ke neman ta biya diyyar dala biliyan 11

    Court symbol

    Asalin hoton, Getty Images

    Najeriya ta yi nasara a ƙarar da ta ɗaukaka kan wani hukunci da ya nemi ta biya diyyar dala biliyan 11 ga wani kamfanin ƙasashen waje, bayan rushewar wata kwangilar shimfiɗa bututun iskar gas.

    Kamfanin P&ID mai hedkwata a Virgin Islands na Birtaniya ne ya kai Najeriya ƙara, a kotun sasanta rikicin kasuwanci, inda ya nemi diyyar kudin da suka kai kashi ɗaya cikin uku na asusun ajiyar ƙasashen wajen Najeriya.

    Mai shari'a Robin Knowles ya ce ya karɓi bahasin ƙalubalantar hukuncin kotun baya da Najeriya ta yi, a wani hukunci da ya yanke ranar Litinin.

    "Ban amince da dukkan zarge-zargen da Najeriya ta yi ba," alƙalin ya faɗa a hukuncin nasa. Sai dai ya ƙara da cewa hukuncin kotun sasanta rikicin kasuwanci "an same shi ne ta hanyar damfara, kuma hanyar da aka bi, ta saɓa da manufar aikin gwamnati".

    A shekara ta 2010 ne, Najeriya ta bai wa kamfanin Process & Industrial Developments (P&ID) kwangilar aikin ginawa da gudanar da wata tashar sarrafa iskar gas tsawon shekara 20 a kudancin kasar, a wani ɓangare na wani babban shirin haƙo ɗumbin arziƙin iskar gas da Allah ya hore mata.

    Sai dai bayan rushewar yarjejeniyar, kamfanin P&ID ya garzaya gaban kotun sasanta rikice-rikicen kasuwanci da ke London a 2017, wadda ta yanke hukuncin cewa Najeriya ba ta da gaskiya a batun, kuma ta biya kamfanin dala biliyan 6.6 na asarar da ya yi.

    Kuɗin dai ya yi ta ƙaruwa har zuwa sama da dala biliyan 11, saboda kuɗin ruwa.

    Kiyasi na cewa kuɗin ya ninka har sau 10 a kan kasafin kudin Najeriya na fannin lafiya na 2019.

    Lauyoyin Najeriya sun ce ƙasar ta tsinci kanta ne a cikin "wata maƙarƙashiyar cin hanci da damfara" daga kamfanin P&ID, wanda suka ce ya bayar da toshiyar baki ga manyan jami'an gwamnati don samun kwangilar.

    Daga nan kuma sai ya riƙa bayar da rashawa ga lauyoyin ƙasar don samun takardun sirri na hukuma a lokacin shari'ar.

    P&ID ya musanta cewa ya samu kwangilar ta hanyar ba da toshiyar baki, ko ya yi ta bayar da cin hanci ga lauyoyin Najeriya a lokacin sauraron shari'ar, inda ya ɗora alhakin rushewar yarjejeniyar iskar gas ɗin a kan rashin ƙwarewar hukumomi da ke da alhakin tafiyar da shari'ar.

    • 'Ba mu ci nanin ba, saboda haka nanin ba za ta ci mu ba'
    • Sabuwar gardama ta kaure tsakanin PDP da APC kan hukuncin kotun zaɓe
  14. Bidiyo: Motar Majalisar Dinkin Duniya ta kai kayan agaji Khan Younis

    Bayanan bidiyo, Kwalayen kayan agaji daga Japan, da ake rabawa al'ummar Gaza wadanda rikici ya raba da gidajensu a wata makaranta

    Ma'aikatan Majalisar Dinkin Duniya sun isa Khan Younis don raba wa Falasdinawan da ke zaune a wata makaranta ta Majalisar.

    A ranar Asabar ne, motoci dauke da kayan agaji guda 20 suka tsallaka daga Masar ta mashigar Rafa a karon farko cikin mako biyu.

  15. Tarayyar Turai ta fara bin matakai don sanya wa Nijar takunkumi

    Niger protesters

    Asalin hoton, AFP

    Tarayyar Turai ta fara ɗaukar matakin ƙaƙaba takunkumi kan shugabannin mulkin sojan Nijar, wata uku bayan juyin mulki.

    Majalisar Tarayyar Turai ta sanar a ranar Litinin cewa, ta amince da tsarin da zai ba ta damar ƙaƙaba takunkumi kan "mutane da hukumomin masu alhakin ayyukan da ke barazana ga zaman lafiya da kwanciyar hankali da kuma tsaro a Nijar.

    Majalisar ta kuma ce takunkumin zai shafi mutanen da ke zagon ƙasa ga tsarin mulkin Nijar da dimokraɗiyya ko bin doka, da kuma mutanen da ke keta haƙƙin bil'adama ko cin zarafi.

    Takunkuman za su haɗa da hana tafiye-tafiye da rufe kadarori da kuma hana ba da kuɗaɗe ga mutanen da aka sanyawa takunkuman.

    " Da wannan shawara da ta yanke a yau, tarayyar EU ta ƙarfafa goyon bayanta ga ƙoƙarin ƙungiyar Ecowas, kuma ta aike da saƙo ƙarara cewa akwai hukuncin da ke zuwa bayan juyin mulkin soja," in ji babban jami'in harkokin wajen EU Josep Borrell.

    Matakin na Tarayyar Turai ya zo ne bayan ƙaƙabawa Nijar takunkumi da ƙungiyar Ecowas ta yi da kuma matakin dakatar da tallafin da gwamnatin Amurka ke bai wa ƙasar.

    • Kawuna sun rabu kan korar da sojojin Nijar ke wa ƙasashen duniya
  16. Ɗalibi ɗan shekara biyu ya mutu bayan faɗowa daga benen makaranta

    ...

    Asalin hoton, JOHN UDO/EMERALD INTERNATIONAL/FACEBOOK

    Iyaye sun shiga halin jimami yayin da ɗansu mai shekara biyu da wata shida ya faɗo daga ginin makaranta ya rasu a garin Aba da ke jihar Abia cikin kwanakin nan.

    Rahotanni sun ce yaron mai suna David Udo, ɗalibin makarantar ‘Emerald International School’ da ke kan titin ‘Crystal Park’, Aba, ya faɗo daga saman bene mai hawa uku na makarantarsu.

    An garzaya da yaron asibiti inda likitoci suka tabbatar da mutuwarsa.

    A cewar iyayen yaron, wasu mutane ne da ba su sani ba suka kira su a wayar tarho suka shaida musu abin da ya samu yaron nasu a makaranta.

    Mahaifin yaron mai suna John Udo wanda lauya ne ya yi zargin cewa har zuwa ranar Asabar shugaban makarantar bai kira su ya faɗa musu abin da ya faru da yaron nasu ba.

    Da BBC ta tuntubi shugaban makarantar , Peter Nwoke, ya ce rahotonnin da aka bayar ba daidai ba ne, amma ya ki yin wani karin bayani kan abin da ya sani a kan lamarin. "Ba abin da ya faru ba ke nan," in ji shi. "Idan kun zo ido da ido zan bayyana muku abin da na ji ya faru saboda ba na nan abin ya faru."

    Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar, Maureen Chioma Chinaka, ta shaida wa BBC cewa an samu korafi daga iyayen yaron kan abin da ya faru, kuma rundunar ta fara gudanar da bincike kan lamarin.

    • Yadda 'siniya ya yanka makogoron' wani dalibi a makarantar kwana a Borno
  17. 'An kashe ɗan Birtanyia a harin da Hamas ta kai wa Isra'ila'

    ...

    An tabbatar da cewa an kashe wani ɗan Birtaniya a hare-haren da Hamas ta kai wa Isra’ila.

    Yosef Guedalia, mai shekaru 22, soja ne a sashen yaƙi da ta'addanci kuma an kashe shi a lokacin da ya tunkari ƴan bindigar Hamas a garin Kibbutz Kfar Aza lokacin da suka kai hari a ranar 7 ga Oktoba.

    Ɗan'uwansa Asher ya ce ya taimaka wajen kwashe fararen hula da suka jikkata kafin ya koma ya ci gaba da artabu da ƴan bindigan Hamas.

    Akwai bidiyon Yosef yana ɗauke da wani mutum wanda ya ji rauni, wanda yanzu haka ke samun sauƙi a asibiti, in ji Asher.

    ''Ya ceci mutane mintuna kaɗan kafin a harbe shi. Ya nuna jaruntaka da jajircewa, ya kuma ci gaba da fafutuka ba tare da ya yi tunanin kansa ko nuna shakka ba... ya kai ɗaukin ceto ga ƴan ƙasa da dama kafin a kashe su a gidajensu, ya kuma kashe ƴan ta’adda da yawa.''

    Yanzu haka an san cewa Hamas ta kashe ƴan Birtaniya 11.

    An yi garkuwa da daya, kuma aƙalla guda huɗu ba a san inda suke ba.

    • Wace ce Hamas, mene ne ke faruwa a Isra'ila, da sauran tambayoyi
    • Iyayen 'yan Isra'ila da ke hannun Hamas sun yi roko ga al'ummar duniya
  18. Labarai da dumi-dumi, Ma'aikatar lafiya ta ce an kashe Falasɗinawa 436 a rana guda

    ...

    Asalin hoton, Rex Features

    Ma'ikatar lafiya a Gaza ta ce an kashe mutum 436 cikin sa'o'i 24, lamarin da ya sanya Falasdinawan da aka kashe tun bayan sake ɓarkewar rikici tsakanin Hamas da Isra'ila ya kai 5,000.

    Mun samu bayanin da ke cewa a yanzu mutanen da aka kashe daga ranar 7 ga watan Oktoba ya kai 5,087, inda aka samu ɗoriyar 436 daga alƙaluman da aka samu jiya.

    Wannan ya haɗa da yara 2,055 da mata 1,119 da tsofaffi 217.

    Ma'aikatar lafiyar ta ce sama da mutum 15,273 ne aka raunata.

    Kamar sauran hukumomin gwamnati, ita ma ma'aikatar lafiyar tana ƙarƙashin ikon ƙungiyar Hamas ne.

    Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyo
    • Rikicin Isra'ila da Gaza: Mene ne asalin sa?
    • Isra'la ta ce Falasdinawa miliyan ɗaya su fice daga Arewacin Gaza
  19. Za mu kama gurbatattu - Tubabbun 'yan daban da suka koma 'yan sandan sa-kai

    Bayanan bidiyo, Kano Constabulary Recruits

    'Yan sandan sa-kai ko kuma 'yan sandan sarauniya kamar yadda wasu ke kiransu sun bayyana kudurin yin aiki tare da rundunar 'yan sanda ta jihar Kano wajen yaki da aikata laifuka.

  20. Kotun ƙoli ta jinkirta yanke hukunci kan ƙarar da Atiku da Obi suka ɗaukaka

    ...

    Asalin hoton, Facebbok/Obi/Tinubu/Atiku

    Kotun ƙolin Najeriya ta jinkirta yanke hukunci kan ƙarar da Atiku Abubakar da jam’iyyar PDP suka ɗaukaka kan hukuncin da kotun sauraren kararrakin zaben shugaban kasa ta yanke wanda ya tabbatar da nasarar shugaba Bola Tinubu a zaben shugaban ƙasa na 2023.

    Har ila yau, ta dakatar da yanke hukunci kan ƙarar da Jam’iyyar Labour ta daukaka, yayin da ta kori korar jam'iyyar Allied Peoples Movement (APM).

    Kotun ta kuma saurari buƙatu daga lauyoyi kan bukatar da Atiku ya miƙa na gabatar da sabbin shaidu kan shaidar karatun Tinubu.

    Lauyan Atiku Abubakar, Mista Chris Uche, ya buƙaci kotun da ta amince da buƙatar da suka miƙa ta kuma saurari ƙarar da aka daukaka tare da soke takarar Tinubu.

    • Waiwaye: Ranar yanke hukunci kan ƙarar Atiku, ƙungiyar ƙwadago ta bai wa gwamnoni wa'adi kan albashi
    • Abubuwan da kotun zaɓen Najeriya ta cimma a farkon zaman shari'o'i kan Tinubu