'Amurkawa 20 sun ɓata a Isra'ila'

Asalin hoton, Getty Images
Fadar White House ta yi bayanin cewa akwai Amurkawa 20 da suka bata bayan harin da Hamas ta kai wa Isra'ila, in ji mai ba Amurka shawara kan harkokin tsaro Jake Sullivan.
Sai dai ya ce ba zai iya tabbatar da adadin mutanen da aka yi garkuwa da su ba.
Gwamnatin Amurka ta dauki samun bayanai game da Amurkawa da suka bace da matuƙar muhimmanci, kuma tana tuntubar duk iyalan da abin ya shafa, in ji Sullivan.
Tun da farko shugaban Amurka Joe Biden ya ce an san Amurkawa 14 ne aka kashe a hare-haren. Sullivan ya kuma nanata kudurin Amurka kan Isra'ila: "Wannan abu ne mai muhimmanci ga jama'ar Amurka saboda alakarsu da Isra'ila."
- Amurka ta fara matsar da jiragen yaki kusa da Isra'ila bayan harin Hamas
- Firaministan Isra'ila ya yi watsi da kiran shugaban Amurka



























