Ganduje ya karbi 'ya'yan jam'iyyar NNPP ta Kwankwaso
Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da wasu sassan duniya.
Rahoto kai-tsaye
Haruna Kakangi and Mukhtar Adamu Bawa
Sai da safenmu!
To kuma a nan ne wannan shafi mai kawo muku rahotanni da labarai kai tsaye, zai dasa aya. Amma gobe Alhamis, za mu dawo don ci gaba da gabatar muku rahotanni daga sassan Najeriya da Afirka ta Yamma da ma sassan duniya.
Kafin nan kuna iya gangarawa kasa don ci gaba da karanta labaran da muka rigaya muka wallafa muku.
Mukhtari Adamu Bawa ke muku fatan alheri!
Ministan Abuja ya sallami wasu manyan jami'ai a ma'aikatarsa daga aiki
Ministan Abuja, babban birnin Najeriya ya amince da sallamar shugabannin hukumomi da kamfanonin gwamnati da ke karkashin ma'aikatarsa nan take.
Tashar talbijin ta Channels TV ta ambato wata sanarwa daga ofishin Minista Nyesom Wike yana ba da umarnin ga jami'an da ke rike da wadannan mukamai su damka harkokin tafiyar da ofisoshinsu ga jami'ai mafi girman mukami.
A ranar Litinin 21 ga watan Agusta, sabon ministan babban birnin na Najeriya ya kama aiki, bayan nada shi da kuma rantsar da shi da Shugaba Bola Tinubu ya yi.
Daga cikin hukumomi da kamfanonin da wannan mataki ya shafa har da kamfanin kula da harkokin zuba jari na Abuja da hukumar kula da kasuwannin Abuja da kamfanin manyan motocin sufuri na Abuja.
Akwai kuma hukumar samar da ruwan sha ta Abuja da hukumar kula da unguwannin bunkasa unguwannin wajen Abuja da Kamfanin bunkasa kadarorin Abuja da sauransu.
Abin da ya kamata ku ci idan kuna son yin ƙiba
Ana neman waɗanda suka shirya bikin da mutane kimanin 100 har da amarya suka mutu
Asalin hoton, Getty Images
Kafar yaɗa labaran gwamnati a Iraqi ta ce hukumomi sun ba da sammacin kama mutum 13, waɗanda suka haɗar da masu wurin da aka yi bikin da ya yi sanadin rasuwar kimanin mutum 100.
A cikin mutanen da ake nema, kamar yadda rahotanni suka ambato, akwai ma'aikatan kula da ɗakin taron.
Rahotanni sun ce an yi amfani da abubuwa masu saurin kama da wuta wajen yin ciko a bangon zauren taron, wanda ke lardin Nineveh a arewacin Iraqi.
Amfani da irin waɗannan abubuwa ya saɓa wa ƙa'idojin gini a cewar hukumomi.
Jami'ai sun ce binciken farko-farko da suka gudanar, ya gano cewa an yi amfani da tartsatsin wuta a lokacin bikin.
Yanzu haka an ayyana zaman alhini na tsawon kwana uku a ƙasar.
Amarya da ango na cikin mutanen da aka tabbatar sun rasu a lamarin.
Dubban mutane na fakewa a makarantu yayin da rikici ya rincabe a Sudan
Dubban mutanen da yaki ya tilasta wa ficewa daga gidajensu a Sudan, sun koma zama a makarantu, wadanda ba su dace da wannan manufar ba, wani gwamnan lardi ya fada wa BBC.
Rikici na tsawon watanni tsakanin sojojin Sudan da mayakan dakaru masu kayan sarki ya tilasta wa iyalai kimanin 40,000 tserewa daga Darfur ta Arewa, in ji Nimr Abdel, jami'in da ke shugabantar jihar.
Tun bayan fara rikicin a watan Afrilu, Darfur ta shaida kafsawar fada mafi muni a kasar ta Sudan.
Nimr Abdel ya fada wa wani shirin Rayuwa a Sudan na BBC cewa: "Da yawan mutanen da suka bar gidajensu a yanzu sun koma zama a makarantu, wadanda ba su dace yadda ya kamata da irin wannan rayuwar ba. Wadannan makarantu ba su cancanci zama makwanci ba.
"Bandakunan makarantun, wadanda aka samar don dalibai, ba su da yawan da za su iya biyan bukatun dumbin mutanen da suke samun mafaka a ciki."
Matukar fadan ya ci gaba, hukumomi za su duba yiwuwar samar da sansanoni don wannan manufa.
An ga hotunan jirgin saman sojojin Mali da ya yi hatsari
Asalin hoton, @JacdecNew
Shugabannin mulkin sojan Mali sun mika sakon ta'aziyya kan mutuwar wani hafsan sojan kasar mai mukamin Laftanal Kanal wanda danginsa suka ce ya rasu ne a cikin wani jirgin saman Rasha da ya yi hatsari a karshen makon jiya.
Akwai rahotannin da ke cewa jirgin yana tafiya ne da mayakan kamfanin Wagner na Rasha kuma an samu asarar rayuka da yawa.
Jami'ai a Mali da Rasha sun kama bakinsu sun yi shiru game da hatsarin, amma dai sannu a hankali gaskiya tana ta fitowa.
Bidiyo a shafukan sada zumunta na nuna wani babban jirgin da aka kera a Rasha - kirar Ilyushin - ya yi sabi-zarce a kan titin filin jirgin sama na Gao, inda ya karye sannan ya kama da wuta.
Majiyoyin tsaro a ranar Lahadi sun ce jirgin saman mallakar rundunar sojojin Mali ne kuma yana dauke da mayaka masu yawa daga kungiyar Wagner ta Rasha.
Rikici a arewacin Mali yana dada kazancewa cikin sauri. Dubban dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya suna ficewa daga kasar kamar yadda sojoji masu mulki suka nema.
Dakarun Mali da abokan kawancensu daga kungiyar Wagner na kokarin dakatar da mayaka 'yan ta-da-kayar-baya masu ikirarin jihadi da Azbinawa 'yan tawaye daga kwace yankuna ciki har da sansanonin sojoji.
Ganduje ya karbi 'ya'yan jam'iyyar NNPP ta Kwankwaso da suka canza sheka
Asalin hoton, SALIHU TANKO YAKASAI/FACEBOOK
Shugaban jam'iyyar APC na kasa a Najeriya, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya karbi dan takarar gwamna na jam'iyyar adawa ta NNPP a jihar Bauchi a zaben 2023, wanda ya sauya sheka zuwa jam'iyya mai mulki.
Shugaban APC ya yaba wa shawarar Haliru Dauda Jika ta koma wa jam'iyya mai mulki, a matsayin wani mataki da ya dace, inda ya nunar cewa tabbas a yanzu tsohon dan takarar na NNPP ya gane cewa jam'iyyar NNPP "mai samun goyon bayan Kwankwasiyya, yaudara ce da ci da gumi".
Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa da yake karbar Haliru Jika da illahirin shugabannin jam'iyyar NNPP a Bauchi, Ganduje ya ce "Lokacin da na samu labarin cewa za ka zo ganina don tattaunawa a kan hanya mai bullewa, na san na hadu da wani jigon dan siyasa, wanda kowa ya san shi a Bauchi".
“Ya dawo zuwa jam'iyyar masu ra'ayin ci gaba da kuma alkibla, musamman ganin inda ya baro. Ya taho daga wata jam'iyya wadda a baya ta kasance mai daraja da matukar kima, amma daga baya sai Kwankwasiyya ta karkatar da ita, ta gurbata ta.
“Muna farin cewa NNPP ta ainhi ta dawo kuma ta hau kan cikakken matsayinta, inda ta yasar da kungiyar Kwankwasiyya, duk ta yi watsi da ita gaba daya.
Shugaban APC ya kuma yi wa 'yan siyasar da suka koma jam'iyyar tasa alkawarin shigar da kowa a dama da shi cikin tafiyar jam'iyyar a jihar Bauchi, a wani bangare na kokarin sake fasalin APC kafin zaben 2027, inda ya nanata cewa jam'iyyar ta yi nadama kan rawar da ta taka a Bauchi, yayin zabukan da suka wuce.
Tsohon dan takarar na jam'iyyar NNPP ya bayyana wa manema labarai cewa ya yanke shawarar komawa APC ne saboda muradan dumbin magoya bayansa a jihar Bauchi.
Ya ce, "jingine tafiyar NNPP da na yi zuwa APC, ba shi wata alaka da dan shugaban kasa na jam'iyyar. Ba ni da wani sabani da Kwankwaso".
Kotu ta ayyana Gawuna a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan Kano
An ci tarar makarantar da ta sa hotunan dalibanta a intanet
Hukumar kare bayanan mutane a kasar Kenya ta ci tarar wata makaranta dala 31,000 saboda wallafa hotunan dalibanta a intanet ba tare da izinin iyayensu ba.
Wannan ne mataki irinsa na farko da sabon ofishin kare bayanan mutane ya dauka.
Haka zalika, hukumar ta ci tarar wani gidan rawa dala 12,000 da kuma wani kamfanin ba da bashi dala 20,000.
A cewar hukumar, gidan rawar ya buga hoton abokin huldarsa a shafinsa na sada zumunta, ba tare da izini ba.
Shi kuma kamfanin ba da bashin ya rika yi wa abokan huldarsa barazana ta hanyar kiraye-kirayen waya da aika sakonni daga bayanan da ya samu ta wasu hanyoyi daban.
Tarar ta janyo muhawara game da 'yancin tsare sirrin mutane musamman a gidajen rawa da na shan barasa.
Wasu cikin irin wadannan cibiyoyi a yanzu sun fara wallafa sanarwar cewa duk mutumin da ya sa kafa ya shiga harabobinsu, tamkar ya yarda ne a dauki hoto ko bidiyonsa ba tare da neman diyya ba, kuma duk wanda bai yarda da dokokinsu ba, to kada ya shiga.
Wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafin X, ta ce tana fata tarar da ta ci cibiyoyin za ta aika wani sako ga ire-irensu a kan su rika bin dokokin kare bayanan mutane na kasar ciki har da wadanda suka bukaci a nemi amincewar mutum kafin a buga hotunansu a intanet.
An kama tsuntsayen aku da ake yunkurin fasa-kwaurinsu daga Najeriya
Asalin hoton, Nigeria Customs
Hukumar hana fasa-kwauri ta Najeriya ta ce ta kama wasu tsuntsaye nau'in aku da shaho wadanda ke cikin kasadar bacewa daga doron duniya a lokacin da ake yunkurin fitar da su zuwa kasashen waje.
Kwanturolan hukumar na shiyyar iyakar Seme, Timi Bomodi ya sanar a ranar Litinin cewa jami'ansa sun kama tsuntsayen ne da sanyin safiyar ranar, bayan sun samu bayanan sirri, inda suka tarbe masu fasa-kwaurin a shingen bincike na Gbaji suna yunkurin shiga Jamhuriyar Benin.
Ya ce sun samu bayanan sirri cewa an kwaso tsuntsayen ne a babbar motar safa daga Kaduna zuwa Lagos, da niyyar kai su kasashen waje don sayarwa.
"Kamar yadda mai yiwuwa kuka sani, wannan haramtaccen kasuwanci na tsuntsayen da ke kokarin bacewa daga doron kasa."
Kwanturolan hukumar ya ce sun kama mutum biyu masu alaka da fasa-kwaurin tsuntsayen.
Bayanan bidiyo, Za a iya kashe mu a kowane lokaci - Armeniyawa
Dubban Armeniyawa ne ke tserewa daga yankin Nagorno-Karabakh bayan Azerbaijan ta
ƙwace yankin a makon da ya gabata.
Dubban Armeniyawan sun tsallaka zuwa cikin
Armeniya, wadda ita ce yankin ƴan ƙabilar su 120,000 ke rayuwa.
Jakadan Faransa a Nijar ya isa gida
Asalin hoton, facebook/Sylvain Itté
Jakadan Faransa a jamhuriyar Nijar, Sylvain Itté ya isa brinin Paris na ƙasar Faransa a yau Laraba.
Ma'aikatar harkokin waje ta Faransa ce ta tabbatar da hakan, bayan a safiyar Larabar an samu rahoton ficewar ambasadan daga Yamai, babban birnin jamhuriyar Nijar.
Sanarwar ta ce: "Jakadanmu a Nijar ya isa Paris a yau, kamar yadda shugaban ƙasa ya bayar da umarni a ranar Lahadi."
"Ministan harkokin Turai da ƙasashen ƙetare ne ya tarbe shi domin isar masa da godiya kan yadda shi da tawagarsa suka gudanar da ayyukansu duk da hali na matsi."
A yau Litinin ne jakadan na Faransa a jamhuriyar Nijar ya bar Yamai, inda ya tashi a jirgin sama daga birnin Ndjamena na ƙasar Chadi zuwa gida.
An kwashe tsawon lokaci ana taƙaddama bayan da shugabannin mulkin soji na Jamhuriyar Nijar suka umarci jakadan na Faransa da ya fice daga ƙasar bayan ya ƙi amsa gayyatar da suka masa.
Wani mutum ya shirya sace kansa don kada ya kwana a gidan 'matarsa'
Asalin hoton, Getty Images
An umarci wani mutumin kasar Ostireliya ya biya 'yan sanda diyya bayan ya shirya sace kansa da kansa.
Paul Iera, daga yankin Wollongong a New South Wales, ya shirya makarkashiyar ne don ya samu damar gujewa kwana a gidan abokiyar zamansa don zuwa gidan wata matar da yake son kwana a wurinta a ranar Jajiberen Sabuwar Shekara.
Wata kotu ta ba da umarni ga mutumin mai shekara 35 ya biya 'yan sandan New South Wales diyyar dalar Ostireliya 16,218 kwatankwacin naira miliyan takwas saboda aikin binciken da suka gudanar.
Kotun majistaren Wollongong ta ce Paul Iera ya "biye wa ragon tunanin son zuciya da ya zo masa".
A ranar 31 ga watan Disamba ne 2022, Paul Iera ya aika wani takaitaccen sako ga abokiyar zamansa inda ya yi ikirarin cewa daga mutanen da suka sace shi ne. Sakon ya ce mutanen da suka sace shi din za su tsare shi "har zuwa safiya".
Daga nan sai abokiyar zaman nasa ta tuntubi 'yan sanda a lardin Lake Illawarra, wadanda suka gano Paul Lera a cikin motarsa da ke unguwar Dapto washe gari.
Kafofin yada labarai sun ba da rahoton cewa 'yan sanda sun shafe fiye da tsawon sa'a 200 suna aikin bincike a kan ikirarin Paul, tare da kashe dala 16,218 wajen biyan albashi da bin diddigin layin waya.
Jaridar Illawarra Star ta ce da farko mutumin ya yi ikirarin cewa gungun wasu mutane ne 'yan Gabas ta Tsakiya suka kama shi kafin su sake shi daga bisani.
An kama shi daga baya a cikin watan Janairu inda aka tuhume shi da yin ikirarin karya da nufin tilasta wa wani mutum gudanar da bincike, shari'ar da za a iya yanke wa hukuncin daurin shekara bakwai a gidan yari.
Paul Iera ya kauce wa zaman gidan yari amma dai an yanke masa hukuncin yin hidimar al'umma tsawon shekara uku, kuma ya biya 'yan sanda diyya.
CAF ta sanar da ƙasashen da za su karɓi baƙuncin gasar 2025 da 2027
Koriya ta Arewa ta miƙa wa Amurka jami'in sojanta da ya tsere
Wani jami'in sojan Amurka da ya tsallaka iyaka zuwa Koriya ta Arewa yanzu haka an miƙa shi ga jami'an Amurka.
Kafafen yaɗa labaru na Amurka sun ce yanzu haka sojan na hannun jami'an Amurka a China.
Sojan na Amurka ya tsallaka zuwa Koriya ta Arewa ne ba bisa ƙa'ida ba a cikin watan Yuli.
Har yanzu babu cikakken bayani kan yadda aka tsare shi a Koriya ta Arewar da kuma lafiyarsa.
Tun farko, da safiyar ranar Laraba ne kafar yaɗa labarun Koriya ta Arewa ta bayyana cewa ƙasar ta yanke shawarar mayar wa Amurka sojan nata.
An kwashe sojojin Mali bayan wani hari da aka kai wa sansaninsu, Daga Will Ross editan BBC na Afirka
Asalin hoton, Getty Images
An kwashe sojoji daga wani sansaninsu da ke arewacin Mali, bayan wani da 'yan bindiga suka kai, a cewar rundunar sojin kasar.
Wata sanarwa da rundunar ta fitar ta ce dakarun na Mali sun wargaza shirin maharan a Acharane, wani yanki da ke birnin Timbuktu mai tsohon tarihi.
Babu bayani a fayyace a kan ko maharan, 'yan ta-da-kayar-baya masu ikirarin jihadi ne ko kuma Azbinawa 'yan tawaye.
Duka bangarorin biyu sun kara yawan hare-haren da suke kai wa a cikin 'yan makonnin nan - a daidai lokacin da dakarun kwantar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya ke janyewa daga kasar bayan shugabannin mulkin sojin Mali sun nemi su fice.
Majalisar dokokin Ondo za ta ci gaba da yunƙurin tsige mataimakin gwamnan jihar
Majalisar dokokin jihar Ondo ta ce za ta ci gaba da yunƙurinta na tsige mataimakin gwamnan jihar, Lucky Aiyedatiwa duk da ƙarar da ya shigar a kotu na neman a dakatar da batun.
Aiyedatiwa ya garzaya babbar kotu ne da ke Akure, inda ya buƙaci da a dakatar da ƴan majalisar daga yunƙurin tsige shi.
Sai dai a wata sanarwa da ta samu sa hannun shugaban majalisar dokokin jihar, Oladiji Olamide Adesanmi, majalisar ta tabbatar wa al'ummar jihar cewa za ta ci gaban da bin matakin har ƙarshe, sai dai duk da haka za ta bi matakan da kundin tsarin mulkin ya gindaya.
Sanarwar ta ce "majalisar ba za ta yi watsi da nauyin da kundin tsarin mulki ya ɗora mata na binciken masu riƙe da muƙaman gwamnati ba, musamman a inda ake batu na manyan zarge-zarge aikata rashawa da tozarta matsayi, kamar yadda ake yi wa mataimakin gwamnan."
Wani baturen Birtaniya ya amsa laifin yin lalata da karnuka
Asalin hoton, SUPPLIED
Wani sanannen mai nazari kan rayuwar kadoji ɗan asalin Birtaniya ya amsa tuhumar da ake yi masa ta yin lalata da dabbobi da kuma mallakar abubuwan da suka jiɓanci cin zarafin yara.
Wata kotu a ƙasar Australiya ce ta saurari ƙarar, kan cewa Adam Britton ya ɗauki bidiyon kansa yana azabtar da gwamman karnuka har kusan dukkanin su suka mutu.
Haka nan mutumin ya riƙa wallafa irin waɗannan bidiyoyi a shafukan intanet.
Yanzu haka dai ana jiran kotu ta ajiye ranar da za ta yanke hukunci a kan mutumin, wanda ya taɓa yin aiki da BBC da kuma tashar talabijin mai shirye-shirye kan rayuwar dabbobi ta National Geographic.
A lokacin sauraron ƙarar a ranar Litinin, alƙalin kotun ya ce yawancin bidiyon da aka kawo a matsayin shaida sun yi muni da yawa, inda aka gargaɗi mahalarta kotun kan cewa za su iya fita domin gudun kada hankulansu su tashi.
Alƙalin kotun, mai shari'a Michael Grant ya ce ya damu kan cewa bayanan abubuwan da Britton ya aikata za su iya haifar da mummunar damuwa ga mahalarta kotun, inda ya buƙaci jami'an tsaro da ƙananan ma'aikatan kotun da su fita daga zauren.
Masu gabatar da ƙara sun ce Britton ya kasance mai 'matsananciyar muguwar aniya da son yin lalata da dabbobi' tun aƙalla shekarar 2014.
Sun ce baya ga cin zarafin nasa dabbobin, ya kuma shawo kan wasu mutane daban domin su ba shi ajiyar dabbobinsu, waɗanda su ma ya ci zarafin su.
An tabbatar da cewa ya riƙa cin zarafin dabbobin ne a wani ɗakin kwantena da ya mallaka, wanda ya maƙala wa kyamarori, kuma ya laƙaba wa wurin sunan "ɗakin azabtarwa."
An bayyana cewa daga cikin karnuka 42 da ya ci zarafi a tsawon wata 18, guda 39 sun mutu.
Yanzu haka dai ana tsare da Briiton tun bayan da aka kama shi, inda ake sa ran yanke masa hukunci a watan Disamba.
An haife shi ne a yankin West Yorkshire na Birtaniya, inda ya koma Australia shekaru 20 da suka gabata domin yin aikin da ya shafi kadoji.
Koriya ta Arewa za ta mayar wa Amurka sojanta da ya tsere
Asalin hoton, Reuters
Koriya ta Arewa ta ce ta yanke shawarar korar wani jami'in sojan Amurka wanda ya tsallaka cikin ƙasar ba bisa ƙai'da ba daga Koriya ta Kudu a watan Yuli.
Babu dai ƙarin bayani kan lokaci da kuma hanyar da Koriya ta Arewar za ta yi amfani da ita wajen mayar wa Amurkar da sojan nata.
Kafar yaɗa labaru ta Koriya ta Arewa ta ce sojan, mai muƙamin karabiti, ya tsere zuwa cikin ƙasarta ne sanadiyyar cuzguna masa da ake yi da kuma nuna masa wariyar launin fata a sansanin sojin Amurka.
Tun farko dai, sojan na kan hanyarsa ce ta komawa Amurka domin fuskantar hukunci kan wasu laifuka da ake zargin sa da aikatawa, inda ya samu damar sumɓulewa, ya bi sahun masu ziyarar kan iyakar Koriya ta Arewa da ta Kudu.
Bayan lokaci kaɗan kuma ya samu nasarar tsallakawa zuwa cikin Koriya ta Arewa.
Abubuwan da ake sa ran Kim Jong-un zai aiwatar a 2023
Duka da zubar da ciki: Rayuwa a gidan yarin Koriya Ta Arewa
Karen shugaban Amurka Joe Biden ya ciji mai kare lafiyar shugaban ƙasar
Asalin hoton, Getty Images
Karen shugaban Amurka, Joe Biden, wanda ake yi wa laƙabi da 'Kwamanda', ya sake cizon wani jami'in tsaro na sirri wanda ke cikin masu kare lafiyar shugaban ƙasar.
Lamarin ya faru ne a ranar Litinin da daddare, inda aka bai wa jami'in kulawa a wajen da lamarin ya faru, kamar yadda wata sanarwa ta ƙunsa.
Wannan ne karo na 11 da karen ke cizon jami'an tsaro a fadar ta White House.
A baya, sakataren yaɗa labarun fadar White House ya ɗora alhalkin faruwar lamarin kan gajiya sanadiyyar ayyukan da ke gudana a fadar.
Karen shi ne ƙarami a cikin jerin karnukan iyalin shugaban ƙasar.
Wasu lokutan da aka samu rahoton cizon karen sun faru ne a gidan shugaban ƙasar da ke Delaware.
A watan Yulin da ya gabata, jamai'an fadar White House sun ce suna shirin bai wa karen horo bayan yunƙurin da ya yi na cizon ma'aikata.
Asalin hoton, Getty Images
Joe Biden: Kalubale biyar da ke gaban Shugaban Amurka
Joe Biden ya soki Rasha kan harin da ya hallaka fararen hula
An ci tarar wata makaranta saboda wallafa hotunan ɗalibai a shafin sada zumunta
Asalin hoton, Getty Images
Hukumar kula da sadarwar zamani ta Kenya ta ci tarar wata makaranta kuɗi dalar Amurka 25,000 saboda wallafa hotunan ɗalibanta a shafin intanet ba tare da samun izinin iyaye ba.
Wannan ne mataki irin haka na farko da ofishin kare bayanai ta intanet na ƙasar ya ɗauka.
Haka nan an kuma ci tarar wani gidan rawa da kuma wani kamfanin bayar da rance.
Hukumar ta ce an ci tarar gidan rawar ne bayan ya wallafa hoton wani abokin hulɗarsa a shafinsa na sada zumunta ba tare da izinin mutumin ba.
Shi kuma kamfanin bayar da rancen ya yi wa abokan hulɗarsa barazana ta hanyar kiran waya da kuma tura wa na kusa da su sakonni.
Wannan tara dai ta haifar da muhawara a ƙasar game da sirrin bayanan al'umma da kuma yadda kamfanoni ke amfani da su.
A wani saƙo da hukumar ta wallafa a shafinta na X, ta ce tana sa ran wannan tara za ta zama izina da kamfanoni domin su riƙa martaba dokokin kare bayanan al'umma, ciki har da batun neman izinin mutane kafin wallafa hotunansu a shafukan intanet.
Shugaban Kenya ya nemi afuwar al'ummar ƙasar kan mace-macen masu azumi
Wanne irin wa'azi limamin coci mai sa azumin mutuwa ke yi wa mabiyansa?