Ban kwana
Sai da safe daga nan BBC
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya
Abdullahi Bello Diginza
Sai da safe daga nan BBC

Shugabannin kasashen Mali da Burkina Faso da Nijar sun ce sun kulla wani kawancen tsaro na kasashensu.
Shugaban sojan Mali Assimi Goita ya ce kasashen uku sun sanya hannu kan wata yarjejeniyar kafa abin da ya kira kungiyar hadin kan kasashen Sahel (AES).
Ya bayyana yarjejeniyar a matsayin wani ginshiki ga tsaro da taimakon juna domin amfanin al'ummar kasashen uku.
Kasashen uku sojoji ne ke mulki bayan juyin mulki, ta baya-bayan nan ita ce Nijar.
Sai dai kasashen na fama da matsalar tsaro ta mayaka masu da'awar jihadi - matsalar da ta samo asali daga arewacin Mali - daga baya kuma ta bazu zuwa Nijar da Burkina Faso.

Asalin hoton, Reuters
Jami'an tsaro a Tunisia sun ce sun kama daruruwan yan ci-rani a wani samame da suka kaddamar kan masu fataucinsu.
Ma'aikatar cikin gida ta kasar ta ce shugaban Tunisia ne ya bayar da umarnin gudanar da samamen a gabar ruwan Sfax, domin dakile kwararar yan ci rani a kasar.
Jami'an tsaron sun abka gidaje tare da kwace jiragen ruwa.
Wannan na zuwa yayin da hukumomin Italiya ke fama da kwararar yan ci rani ta ruwan Lampedusa

Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El - Rufai ya ce wa'adi na biyu na tsohon Shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo cike ya ke da yalwatuwar arziki, samar da ayyukanyi da kuma rage hauhawar farashin kaya a Najeriya.
El Rufa'i ya bayyana haka ne a ranar Juma'a yayin wani taron Afrika da ya gudana a Afrika ta Kudu, wanda aka tattauna kan samar da tsari mai kyau da zai bunƙasa tattalin arziƙin ƙasashen nahiyar.
Tshon ministan ya ce "Muna da hukumar tsare-tsare sai dai ba ta aiki yadda ya kamata.".
"Idan ka dubi tsari tattalin arzikin Najeriya lokacin da ya fi samun tagomashi shi ne shekaru huɗu zuwa biyar na wa'adi na biyu na tsohon shugaban Najeriya Obasanjo daga 2003 zuwa 2007, lokacin da a karon farko ƙasar ta koma tsarin da yake mai inganci da ya dace kuma muka yi sa'a," in ji El Rufa'i.
Obasanjo ya jagoranci Najeriya daga shekarar 1999 zuwa 2007, kuma shi ne shugaban farar hula na farko bayan komawar ƙasar kan tsarrin dimokraɗiyya.
Shi kuwa El Rufa'i ya yi ministan babban birnin ƙasar Abuja.

Asalin hoton, Getty Images
Manchester City ta je ta doke West Ham 3-1 a wasan mako na biyar a gasar Premier League ranar Asabar.
James Ward-Prowse ne ya fara ci wa West Ham kwallo a minti na 36, sai Jeremy Doku ya farke wa City kwallon.
Daga baya ne Bernardo Silva ya kara na biyu, sannan Erling Haaland ya ci na uku a wasan kwallo na bakwai da ya zura a raga kawo yanzu.
Haaland ya fara da cin kwallo a karawa da Burnley da City ta ci 3-0 a wasan farko na kakar nan ranar 11 ga watan Agusta.

Firaiministan Burtaniya ya sanar da cewa za a haramta amfani da kare ƙirar Amurka XL bayan gano gawar wani mutumi da ake zargin irin karen da kashe shi.
Rishi Sunak ya ce wannan karen "haɗari ne ga al'ummarmu" kuma za a haramta amfani da shi nan da ƙarshen shekara.
Wasu karnuka biyu ne suka jikkata mutumin mai suna Ian Price a ranar Alhamis daga baya kuma ya rasu a asibiti.
Nau'in wannan kare da ake kira American bully XL yana da haɗari, yana iya tsalle ya ɗane mutum tare da kai masa rahi.

Asalin hoton, GT
Nan ne inda ruwan da ke Derna ke taruwa.
Kuma yana nan yaƙi raguwa duk da an kai mako guda da fuskantar ambaliya, har yanzu ruwan na koro gawarwaki.
Za ka iya ganin shara - sassan motoci, karyayyun tagogi da kayan amfanin gida da dai sauran abubuwa da ruwan ya yi awon gaba da su.
Akan ji mummunan warin kwatami da na gawarwaki.
Wasu tawagar masu ceto ta Turkiyya da ta kwashe kimanin kwanaki biyar tana aiki, ta za gaya da manema labarai domin gane wa idanunsu.
Sun riƙa zagayawa suna neman gawarwakin da ruwa ya koro gefen gaɓa ko jikin shara.
Sun ce sun samu gawa uku a safiyar yau.

Asalin hoton, gt

Asalin hoton, Getty Images
Liverpool ta yi wasa biyar a Premier League ba tare da rashin nasara ba a kakar bana ta 2023/24.
Kungiyar ta Anfield ta je ta doke Wolverhampton 3-1 a Molineux a fafatawar ta babbar gasar tamaula ta Ingila.
Wolves ce ta fara cin kwallo minti na bakwai da take leda a karawar da Andy Robertson na Liverpool ya buga wasa na 200 a Premier League.
Minti 10 da suka koma zagaye na biyu bayan hutu ne Liverpool ta farke ta hannun Cody Gakpo, sannan Robertson ya ci na biyu da kuma ta uku da Hugo Bueno da ya ci gida.
Salah wanda ya bayar da kwallo biyu aka zura a raga, ya zama ɗan wasa na hudu da ya bayar da kwallo aka zura a raga a waje a karawa biyar a jere.

Yayin da ake gudanar da bikin tunawa da mutuwar Mahsa Amini a karon farko, an girke jami'an tsaro masu yawa a kusa da gidansu da ke Iran.
Mahsa Amini ta mutu ne a hannun 'yan sanda lokacin da suka tsare ta, abin da ya ja zanga-zangar ƙin jinin gwamnati a Iran ta watanni.
Ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan adam sun ce an tsare mahaifinta a gida lokacin da ya nemi ya fita daga gidan tun da fari.
A cewar ƙungiyoyin jami'an tsaro sun yi wa mahaifin Mahsa gargaɗin cewa kada ya sake ya je kabarinta domin bikin tunawa da ita.
Domin kaucewa sake faɗawa zanga-zanga a titinan Iran, gwamnati ta tsaurara tsaro ta ko ina.
A jiya da daddare an ta jin waƙen nuna adawa da gwamnati a titinan ƙasar.

Asalin hoton, Getty Images
Erik ten Hag ya ce bai sani ba ko Jadon Sancho zai ƙara buga wa Manchester United wasa nan gaba.
Mai shekara 23 yana atisaye shi kaɗai ne ba tare da sauran 'yan wasa ba, bayan da ya yi iƙirarin ɗora masa laifin rashin sanya shi cikin 'yan wasan da suka buga karawa da Arsenal.
Ten Hag ya sanar cewar dalilin da bai yi amfani da Sancho ba a karawar, saboda ƙwazonsa a atisaye ya ragu.
An tambayi Ten Hag ko zai sake saka ɗan ƙwallon a wasa sai ya ce ''Ban sani ba.''

Firaiministar Italiya Giorgia Meloni ta roƙi Tarayyar Turai ta taimaka wajen rage yawan 'yan ciranin da ke tururuwar tsallakawa tsuburin Lampedusa na ƙasar.
Meloni ta ɗora alhakin hakan ga Afrika, musamman mutanen da ke fitowa daga yankin ƙasashen Sahel, ta ce idan da yiwuwa kamata ya yi a kafa wata tawagar sojin ruwa ta haɗin gwiwa domin a kare jiragen ruwa shigowa yankin daga Arewacin Afrika.
Ta ce Gwamnatin Italiya na shirin ɗaukar wasu matakai masu tsauri na musamman domin magance tururuwar 'yan ciranin.
Kimanin 'yan cirani dubu bakwai ne suka shiga Italiya a jiragen ruwa 200 a wannan makon.
Sai dai tuni hukumomin Italiyan suka mayar da wasu tsuburin Sicily da wasu sauran yankuna.

Girgizar ƙasar da ta faru a Morocco ta haifar da labarai masu ta da hankali.
Cikin waɗanda suka mutu har da wasu 'yan makaranta da babu wanda ya rayu cikinsu.
Wata malama da ake kira Nesreen Abu EIFadel ta yi rashin duka ɗalibanta.
Nesreen Abu EIFadel na Marrakesh - amma Adassel, ƙauyen da dutsen yake nan ne garin ɗalibanta da ita kanta, wanda kuma yana tsaka da inda aka yi wannan girgizar ƙasa.
Wannan malama da ke koyar da Larabci da Faransanci ta koma ƙauyen Adassel inda ta fara lura da yara.
Bayan girgizar ƙasar an sanar da ita cewa duka ɗalibanta 32 da take lura da su da shekarunsu ke tsakanin 6 zuwa 12 sun mutu.
Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce ta aike da tallafin magunguna ga mutum 250,000 a Benghazi ta ƙasar Libya.
Cikin sanarwar da ta fitar, WHO ta ce ta aike ta metric tan 29 na tallafin magunguna zuwa Benghazi.
Tashar ruwa ta Benghazi na da nisan kilomita 300 daga Derna, wanda ke da wahalar isa saboda rashin hanya mai kyau.

Shugaban Guinea- Bissau Umaro Sissoco Embalo ya ce har yanzu Ecowas na kan matsayinta na amfani da ƙarfin soji a Nijar.
Cikin wata hira da ya yi da kafar yaɗa labaran France24, Embalo ya koka kan yawaitar juyin mulki a yankin yammacin Afirka cikin shekarun baya-bayan nan, sannan ya yi magana kan rawan da Ecowas ke taka wa wajen hana aukuwar hakan.
Mista Embalo ya bayyana juyin mulkin da ake a yankin yammacin Afirka da cewa yi wa dimokraɗiyyar yankin tarnaƙi ne.
Yana mai cewa rashin ɗaukar matakai kan juyin mulkin da ake yawan yi a yankin, ka iya rage kimar Ecowas.
"Ecowas ta ɗauki matakin girke sojojinta, kuma mun gudanar da taruka har guda biyu game da haka a Najeriya", in ji shi.
Tun da farko ƙungiyar Ecowas ta yi barazanar amfani da ƙarfi soji don mayar da hamɓararren shugabna Nijar Mohamed Bazoum, idan duka hanyoyin tattaunawar diplomasiiya suka ci-tura.

Asalin hoton, Getty Images
Shugaban mulkin sojin Sudan, Janar Abdel Fattah Al-Burhan na wata ziyara zuwa Uganda.
Ziyarar shugaban na zuwa ne adaidai lokacin da 'yan siyasa a ƙasar ke gargadi game da rarrabuwar kawunan ƙasar, sakamakon yaƙin basasar da aka kwashe watanni ana gwabzawa a ƙasar.
Shugaban dakarun RSF, Mohamed Hamdan Dagalo ya yi barazanar kafa gwamnati a yankunan da ke ƙarƙashin ikon mayaƙansa.
RSF na iko da yankuna masu yawa na babbar birnin ƙasar Khartoum, baya ga kudu maso yammaci da kuma tsakiyar ƙasar.
Kungiyar 'yan tawayen Sudan ta SPLM ƙarƙashin jagorancin Abdelaziz al-Hilu, na iko da wasu sassan na jihar Kordofan da ke kudancin ƙasar.
Yayin da gwamnatin al-Burhan ke iko da sauran sassan ƙasar, ciki har da birnin Port Sudan da ke gabashin jihar Red Sea.

An gudanar da jana'izar bai-ɗaya ta dubban mutane a wata maƙabarta a wajen birnin Derna.
Masu aikin ceto sun ce an binne kusan gawarwaki 30,000 a maƙabarta tun bayan mummunar ambaliyar da ta afka wa yankin.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce fiye da mutum 1,000 aka yi wa jana'izar bai-ɗaya a Libya tun bayar da ambaliyar ta amka wa ƙasar.
Kungiyoyin agaji tare da hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) na kira ga hukumomin Libya su daina binne gawarwakin a kaburan bai-ɗaya da ke kusa da ruwa.
Suna masu cewa hakan ka iya haifar da hatsari ga lafiyar mutanen ƙasar, tare da sanya damuwa a zukatan 'yan uwan mamatan.

Asalin hoton, EPA
Rasha ta umarci wasu jami'an diplomasiyyar Amurka biyu da ke ofishin jakadancin Amurka a ƙasar da su fice daga ƙasar.
Cikin wata sanarwar da ma'aikatar harkokin wajen ƙasar, ta bai wa Jeffrey Sillin da David Bernstein wa'adin mako ɗaya su fice daga Rasha
Sanarwar ta zargi jami'an biyu da yin wasu abubuwa da suka 'saɓa ƙai'ida'.
Haka kuma Rasha ta zargi mutanen biyu da yin alaƙa da tsohon ma'aikacin ofishin jakadancin Amurka a Vladivostok, Robert Shonov, wanda Rasha ta zarga da tattara bayanai kan ayyukan sojinta a Ukraine.
Robert Shonov ya yi aiki da ofishin jakadancin Amurka a Vladivostok na fiye da shekara 25, kafin Rasha ta bayar da umarnin korarsa a shekarar 2021.
Shirin Lafiya Zinariya na wannan makon ya duba batun kurajen fuska.
Habiba Adamu ce ta gabatar da shirin.

Asalin hoton, Getty Images
Gwamnatin Birtaniya ta bayyana karin kudin bizar dalibai da ta masu yawon bude ido.
Cikin wata sanarwa da ma'aikatar cikin gida ta kasar ta fitar ta ce kudin bizar ziyarar - kasa da wata shida- ya karu zuwa fan 115, ya yin da na karatu zai karu zuwa fan 490.
Sanarwar ta ce karin kudin bizar zai taiamka wa gwamnati wajen samun kudin shiga.
''Karin kudin zai taimaka wa ma'aikatar cikin gida wajen samun damar aiwatar da tsare-tsaren da suka shafi batun shige da fice'', in ji sanarwar.
Matakin na zuwa ne kasa da wata shida bayan da Birtaniyar ta sanar da karin kudin bizar jinya ga marasa lafiya.