Juyin mulkin Gabon: Annoba ta kama Afirka - Tinubu
Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
Rahoto kai-tsaye
Umaymah Sani Abdulmumin, Haruna Kakangi and Umar Mikail
Ƙarshen rahotanni
Nan muka zo ƙarshe a rahotannin da muke kawowa a wannan shafi.
Kuna iya duba ƙasa don karanta halin da ake ciki a rikicin siyasar Gabon bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a yau Laraba.
Umar Mikail ne ke cewa mu haɗu da ku gobe da safe domin ɗorawa daga inda muka tsaya.
Najeriya da Kanada za su haɗa kai don ƙarfafa dimokuraɗiyya a Afirka
Asalin hoton, State House
Shugaban Najeriya ya tattauna ta waya da Firaministan Kanada Justine Trudeau, inda suka duba halin da dimokuraɗiyya ke ciki a Afirka.
A cewar fadar shugaban Najeriya, Bola Tinubu da Mista Trudeau sun amince cewa za su mayar da hankali wajen ƙarfafa mulkin dimokuraɗiyya a Afirka.
"Shugaba Tinubu ya bayyana wa takwaran nasa ra'ayinsa game da halin da ake ciki a Nijar da Gabon," in ji sanarwar da fadar ta fitar ranar Laraba.
Yayin da dakarun tsaron fadar shugaban ƙasa suka hamɓarar da gwamnatin Mohamed Bazoum na Nijar a watan Yuli, irinsu ne dai suka hamɓarar da gwamnatin Ali Bongo a Gabon a ranar Laraba.
Murna da juyin mulki ko kuma zama da shugaban da 'ba a zaɓa' ba?
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Wasu mazauna birnin Libreville ne ke gaisawa da wani soja yayin da suke murnar ƙwace mulki daga hannun Ali Bongo ranar Laraba
Mazauna Gabon na fuskantar ƙalubale wajen amincewa da juyin mulki ko kuma "shugaban da ba a zaɓa ba", a cewar 'yar gwagwarmaya Scheena Donia game da kifar da gwamnatin Ali Bongo.
Sojojin sun bayar da sanarwar juyin mulkin ne a gidan talabijin ɗin ƙasar a ranar Laraba. Sun ce sun soke sakamakon zaɓen da aka yi ranar Asabar, wanda aka bayyana Shugaba Ali Bongo a matsayin wanda ya yi nasara.
Donia wadda ke zaune a Faransa, ta faɗa wa BBC cewa wasu a Gabon za su fi son juyin mulkin a kan iyalan Bongo su ci gaba da mulki.
Iyalan Bongo sun shafe shekara 53 a kan mulki, yayin da shi kansa Ali ya hau mulki a 2009.
"Abin haushi babu wata hanya da za a iya kawar da mutanen nan daga mulki a Gabon," in ji Donia.
"Duk da haka juyin mulkin soja "abin tsoro" ne, a cewarta.
Yadda Nema ke auna yiwuwar ambaliyar ruwa a Adamawa
Asalin hoton, Nema
Bayanan hoto, Bayan sanarwar barazanar da aka bayar ta ambaliyar ruwa a Najeriya sakamakon ruwan Kogin Lagdo daga Kamaru, tawagar jami'an hukumar Nema sun je duba yanayi a Jihar Adamawa.
Asalin hoton, Nema
Bayanan hoto, Tawagar ta hukumar ba da agajin gaggawa ƙarƙashin jagorancin Ladan Ayuba, ta je yankin Bakin Kogi ne da da ke Jimeta.
Asalin hoton, Nema
Bayanan hoto, Hukumar ta ce bincikensu ya gano cewa cikowan ruwan ta kai maki 8.0 ya zuwa ƙarfe 10:00 na safiyar Laraba, 30 ga watan Agusta.
Asalin hoton, Nema
Bayanan hoto, "Hikimar ziyarar ita ce duba yawan ruwan kogin a shirin ko-ta-kwana da ake yi na yiwuwar ambaliyar ruwa a Adamawa," a cewar wata sanarwa daga Nema.
Sai dai hukumomin kogin na Lagdo a Kamaru sun ce sun dakatar da buɗe kogin don rage yawan ruwan da ke cikinsa.
Me ya sa ake yawan yin juyin mulki a ƙasashe rainon Faransa?
Asalin hoton, Reuters
Bayanan hoto, "Sauka lafiya Faransa," kamar yadda yake a rubuce a jikin wannan kwalin da mai goyon bayan juyin mulki a Nijar ke riƙe da shi
Gabon ce ƙasa ta baya-bayan nan da sojoji suka ƙwace mulki a Afirka ta ƙasashe rainon Faransa bayan Nijar, da Burkina Faso, da Guinea, da Mali, sai kuma Chadi.
Tun daga 1990, kashi 78 cikin 100 na juyin mulki 27 da aka yi a ƙasashen baƙar fatar Afirka sun faru ne a ƙasashen da Faransa ta yi wa mulkin mallaka.
Hakan ya sa masu sharhi ke ɗiga ayar tambaya: Shin Faransa - ko kuma tsare-tsaren mulkin mallaka - za a zarga da haddasa hakan?
Tsarin mulkin mallaka na Faransa ya ba da damar kwasar albarkatun ƙasa daga ƙasashe ta hanyar amfani da matakai na rashin imani.
Bakwai daga cikin ƙasashen Afirka ta Yamma da Faransa ta yi wa mulkin mallaka har yanzu suna amfani da kuɗin CFA, wanda aka tsago darajarsa daga kuɗin yuro, wanda yana ɗaya daga cikin tsare-tsaren Faransa kan ƙasashen.
Haka nan, Faransa ta ƙulla yarjejeniyar tsaro da ta ba ta damar kutsa kai da dakaru a ƙasashen don tabbatar da mulkin shugabannin da ke yi mata biyayya.
Kuna iya karanta cikakkiyar maƙalar a nan:
Rashin kwanciyar hankali a Afirka ta Yamma laifin Faransa ne?
Ma'abota shafukan zumunta na goyon bayan juyin mulkin Gabon
Asalin hoton, Reuters
Bayanan hoto, Wasu 'yan Gabon ke nan suke murna da hamɓarar da gwamnatin Ali Bongo tare da sojoji a kan titin birnin Libreville
Ƙasar Gabon na cikin abubuwan da aka fi tattaunawa a kansu a dandalin sada zumunta, inda mutane ke nuna goyon bayansu ga juyin mulkin da sojoji suka yi.
Wannan lamari ya sha bamban da sauran juyin mulkin da aka yi a Afirka, waɗanda suka gamu da tirjiya ko kuma suka raba kan al'umma.
Mutane da dama sun goyi bayan juyin mulkin a Twitter, wanda ake kira X a yanzu. Haka ma TikTok, inda wasu ke fatan zai "ceto" ƙasar mai arzikin fetur daga mulkin kusan shekara 60 na iyalan Bongo.
"Hankali ba zai ɗauka ba a ce dangi ɗaya sun mulki wata ƙasa tsawon shekara 54 kuma suna kiran ta ƙasar 'dimokuraɗiyya'," a cewar saƙon wani ma'abocin Twitter.
Duk da goyon bayan da ake nunawa a shafukan zumunta, wasu na gargaɗin cewa yanzu ne Gabon ta fara shiga yanayi na gaskiya, kuma za a gane hakan ne yayin da sojojin suka miƙa wa sabuwar gwamnatin farar hula mulki.
Labarai da dumi-dumi, Sojoji sun sanar da Janar Nguema a matsayin shugaban ƙasar Gabon
Jagororin sojin da suka yi juyin mulki a Gabon sun sanar da Janar Brice Oligui Nguema a matsayin shugaban ƙasar na riƙon-ƙwarya.
Lamarin na faruwa ne 'yan awanni bayan wasu sojoji daga rundunar tsaron fadar shugaban ƙasa sun zagaya da shi a titunan birnin Libreville don yin murna.
Ɗazu Shugaba Ali Bongo ya saki wani saƙon bidiyo daga gidan da ake tsare da shi, yana neman abokansa su ƙyamaci juyin mulkin - yayin da mutane ke ci gaba da murna a titunan ƙasar.
Shi da mahaifinsa sun mulki ƙasar da ke da arzikin man fetur tsawon shekara 56, amma da yawan 'yan ƙasar na zaune cikin talauci.
Ina Shugaba Ali Bongo yake?
Har yanzu babu tabbas game da abin da ke faruwa a cikin Gabon, duk da ƙoƙarin da muke yi na tantance rahotannin da muke ji.
Akwai tambayoyin da babu amsarsu har yanzu. Tun daga yaushe aka fara shirya juyin mulkin? Wane ne jagora? Ina Shugaba Ali Bongo yake?
Da aka tambayi Brice Oligui Nguema game inda shugaban yake a hira da jaridar Le Monde, shugaban rundunar tsaron fadar shugaban ƙasar daji ya sake tura mutane.
"Za ka iya tabbatar da cewa an yi masa ɗaurin talala a gidansa?" kamar yadda aka tambaye shi.
Nuguema ya ce: "Ba zan iya faɗa muku ba. Za ku sani nan gaba."
Bayani mai sauƙi a kan juyin mulkin ƙasar Gabon
Mutumin da ya zana tutar Najeriya Taiwo Akinkunmi ya rasu
Asalin hoton, Akinkunmi Akinwumi
Gwamnatin Najeriya ta bayyana alhini a kan mutuwar mutumin da ya zana tutar Najeriya, Pa Taiwo Akinkunmi, wanda ya rasu bayan gajeriyar jinya a gidansa da ke birnin Ibadan.
Wata sanarwa da ministan yaɗa labarai da wayar da kai, Alhaji Mohammed Idris ya fitar ta bayyana marigayin a matsayin wani jigon ƙasa, wanda ba za a iya kankare gudunmawar da ya bayar ga haɗin kan Najeriya daga zukatan al'umma ba.
Tutar Najeriya, kamar yadda ministan ya bayyana, tana ɗaya daga cikin tambarin ƙasar masu daraja, kuma wata kadara ce da Pa Akinwunmi ya rubuta sunansa da ita a cikin kundin tarihin Najeriya.
Taiwo Akinkunmi, wanda ya zana tutar Najeriya, ya rasu yana da shekara 87.
Ɗaya daga cikin 'ya'yansa Akinkunmi Akinwumi ne ya sanar da rasuwar tasa a wani saƙon Facebook a yau Laraba.
"Duk mai rai tabbas mamaci ne, zan iya cewa ka yi rayuwa mai cike da tasiri. Ka huta mahaifina Pa Michael Taiwo Akinwunmi," in ji shi.
Rahotanni sun ce Akinkunmi ya rasu ranar Talata da tsakar dare.
Juyin mulkin Gabon: Za mu mayar da martani tare da sauran shugabanni - Tinubu
Asalin hoton, State House
Shugaban Najeriya ya bayyana cewa yana bin halin da ake ciki a Gabon "cikin damuwa" sakamakon juyin mulkin da sojoji suka sanar a yau Laraba.
Tinubu, wanda shi ne shugaban ƙungiyar Ecowas - ta raya tattalin arzikin ƙasashen Afirka ta Yamma - ya ce yana duba hanyoyin da zai mayar da martani tare da sauran shugabannin Afirka.
Da yake ba da misali da juyin mulkin baya-bayan nan, Tinubu ya ce "annoba" ta kama Afirka, kamar yadda mai magana da yawunsa Ajuri Ngelale ya bayyana.
A ranar Laraba sojoji a Gabon suka sanar da ƙwace mulki kuma suka yi wa Shugaba Ali Bongo mai shekara 64 ɗaurin talala.
Bayani mai sauƙi na juyin mulkin ƙasar Gabon
Wane ne Ali Bongo?
Dole ne mu hukunta Ukraine kan hare-haren da ake kai mana - Rasha
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Shugaban Rasha Vladimir Putin
Hare-haren da aka kai wa Rasha "ba za su wuce ba tare da martani ba", a cewar mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Rasha.
Maria Zakharova ta faɗa wa 'yan jarida cewa Ukraine ce ta kai harin, kuma ta ce harin da ake kaiwa cikin Rashar ba zai yiwu ba ba tare da bayanai daga ƙasashen Yamma ba.
Wasu daga cikin jirage marasa matuƙa da suka hari birnin Moscow cikin dare sun faɗa kan wani filin jirgi a Pskov mai nisan kilomita 600 daga Ukraine.
Ya zuwa yanzu, Ukraine ba ta ce komai ba - da ma ba su fiya cewa komai ba game da hare-haren da ake kaiwa cikin Rasha.
Gwamnan Katsina ya ba da umarnin raba shinkafa buhu 40,000 don rage raɗaɗi
Asalin hoton, UMAR DIKKO RADDA/X
Gwamnan jihar Katsina, Umar Dikko Raɗɗa ya ce ya ba da umarnin raba shinkafa buhu 40,000 nan take, ga al'ummar jihar da nufin rage raɗaɗin matsin rayuwa bayan cire tallafin man fetur a Najeriya.
Wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, Gwamna Raɗɗa ya ce gwamnatinsa ta sayo shinkafar ne daga kuɗin rage raɗaɗi da jihar ta karɓa daga gwamnatin tarayya.
Ya kuma ce ya amince da kafa kwamitoci don raba shinkafar a matakan ƙananan hukumomi da mazaɓu na jihar.
Sai dai, saɓanin naira biliyan biyar da Majalisar kula Tattalin Arziƙin Ƙasa ta ambata tun farko bayan wani taro da ta gudanar kwanan baya, Gwamna Umar Raɗɗa ya ce gwamnatinsa ta sayo shinkafar ne da naira biliyan biyu da gwamnatin tarayya ta saki.
Haka zalika ya bayyana kafa kwamitocin bibiya da sa ido don ganin yadda aikin rabon shinkafar zai kasance.
Umar Dikko Raɗɗa ya kuma yi gargaɗin cewa duk mutumin da aka samu da ƙoƙarin cin amana a aikin rabon shinkafar, kai tsaye ko a kaikaice, to zai fuskanci fushin hukuma.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a X
Tashin hankali ya ɓarke a gabashin DR Congo
Asalin hoton, Reuters
Tashin hankali ya ɓarke a gabashin Jamhuriyar Dimukuradiyyar Congo, tsakanin jami'an tsaro da mabiya wata kungiyar addini da ke adawa da kasancewar Majalisar Dinkin Duniya a can.
Rahotanni sun ce sojoji sun kai hari kan wata tashar rediyo da kuma wani wajen bauta a birnin Goma, inda suka kashe mutum akalla tara, a yunkurin hana zanga-zangar kin jinin majalisar.
An ce, yayin dauki-ba-dadin, wani ɗan-sanda ma ya rasa ransa, inda aka yi masa atire.
Har yanzu ana cikin yanayi na dar-dar a yankin, inda shaguna da harkokin kasuwanci da dama ke rufe.
Ofishin Majalisar Dinkin Duniya a ƙasar ta Kongo na ɗaya daga cikin mafiya girma a duniya, to amma ana sukan aikinsa saboda gaza kawo ƙarshen tashin hankali tsakanin ƙungiyoyi masu makamai a gabasin ƙasar.
Ana ƙarancin kwaroron roba a Kenya
Asalin hoton, Getty Images
Kenya na fama da karancin kwaroron roba da take rabawa kyauta ga maza saboda ragin tallafi da take fuskanta daga kungiyoyi. Ƙasar na bukatar akalla kwaroron roba miliyan 400 a kowacce shekara.
Gwamnati a yanzu na iya raba kwaroron roba miliyan 150 ne kacal, wanda bai kai rabin abin da ake bukata ba.
Gidauniyar AIDS Foundation, ta yi gargaɗin cewa idan ba a shawo kan matsalar ba, Kenya na iya fuskantar kalubalen yaɗuwar cututtuka irinsu HIV, da cutar da ke yaɗuwa ta jima'i da ɗaukar cikin da ba a so.
Wani babban jami'i a hukumar da ke yaƙi da cututtuka masu yaɗuwa ya ce akwai bukatar ɗaukan matakai a cikin gaggawa.
Ƙwararru a fannin lafiya da 'yan majalisa da ƙungiyoyin tallafi za su gudanar da wani taro nan da kwanaki uku a birnin Mombasa domin shawo kan matsalar da kuma samar da karin magungunan HIV.
Lagos za ta ƙaddamar da jirgin ƙasa mai zirga-zirga a cikin gari ranar Litinin
Asalin hoton, LAGOS STATE GOVT
Gwamnatin jihar Lagos ta sanar da cewa rukunin farko na sufurin jirgin ƙasa da zai yi zirga-zirga a cikin birnin Ikko mai taken Blue Rail Line zai fara aiki ranar Litinin 4 ga watan Satumba.
Manajar darakta a hukumar kula da sufuri a ƙwaryar birnin Lagos (LAMATA), Misis Abimbola Akinajo ce ta sanar da haka a tashar jirgin ƙasa ta Marina ranar Laraba, inda ta nunar cewa jirgin farko zai tashi ne da misalin ƙarfe 9 na safe, inda Gwamna Babajide Sanwo-Olu zai kasance a cikin jirgin tare da sauran fasinjoji daga Marina zuwa tashar Mile 2.
Sanarwar na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin jihar Lagos ta gayyaci 'yan jarida waɗanda suka zagaya a cikin jirgin ƙasa mai suna Lagosmetro.
Misis Abimbola Akinajo ta bayyana cewa a cikin mako huɗu na farko jirgin ƙasa mai amfani da kwal zai riƙa zirga-zirga tsawon sa'a 12.
Daga nan kuma sai jirage masu tafiya da lantarki su fara aiki da jigila 76, kuma an yi ƙiyasin cewa jiragen ƙasa za su riƙa ɗaukar fasinjoji tsakanin 150,000 ko 175,000 a kullu yaumin.
Jiragen ƙasa za su riƙa sufuri ne tun daga ƙarfe 5:30 na safe har zuwa ƙarfe 11 na dare.
Misis Abimbola Akinajo ta ce jirgin ƙasan zai riƙa tsayawa ne tsawon minti ɗaya da rabi kawai a kowacce tasha.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a X
An binne gawar shugaban Wagner Yevgeny Prigozhin
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Yevgeny Prigozhin
Sashen yaɗa labaru na Wagner ya bayyana cewa an binne tsohon shugaban kamfanin, Yevgeni Prigozhin a birnin St Petersburg na ƙasae Rasha.
An bayyana cewa an yi jana'izar ce a asirce a mahaifar tasa, kuma an buƙaci masu son su yi ban-kwana da shi za su iya zuwa maƙabartar Porokhovskoe.
An tabbatar da mutuwar shugaban ƙungiyar mayaƙan hayar ne bayan yin nazari a kan ƙwayar halittar waɗanda hatsarin jirgin sama ya rutsa da su a ranar 23 ga watan Agusta.
Fadar gwamnatin Rasha ta musanta cewa tana da hannu a hatsarin jirgin saman.
Sai dai masu lura da al'amura sun riƙa bayyana cewa kwanansa ya ƙare tun bayan boren da ya jagoranta na mayaƙan Wagner a watan Yuni.
Ɗaukacin mutane 10 da ke cikin jirgin da ya yi hatsarin sun mutu, ciki har da na daman Prigozhin, wato Dmitry Utkin, wanda shi na ƙusa ne a kamfanin na Wagner.
Labarai da dumi-dumi, Ali Bongo ya roƙi ƙasashen duniya su kai masa ɗauki
Shugaban Gabon, Ali Bongo, wanda ke cikin yanayi na ɗaurin talala bayan juyin-mulkin sojoji ya nemi ƙasashen duniya da abokansa su kai masa ɗauƙi.
A wani bidiyo da aka fitar a shafukan sada zumunta an jiyo Mista Bongo a inda ya ke tsare a harshen Turanci yana cewa shi da iyalinsa na tsare, sai dai kuma bai san halin da matarsa da ɗansa ke ciki ba.
Sojoji da suka kifar da gwamnatin Bongo sun rushe gwamnatinsa tare da rufe iyakokin ƙasar, suna mai jadadda cewa jagoran juyin-mulkin ne zai riƙe ƙasar.
Zuri'ar iyalan Bongo sun shafe shekaru 56 akan mulkin Gabon.
Ƙungiyar Commonwealth ta nuna matuƙar damuwarta kan juyin-mulkin sojoji a Gabon
Sakatare janar na ƙungiyar Commonwealth ta nuna matuƙar damuwarta kan halin da Gabon ke ciki bayan juyin-mulkin sojoji, tana mai cewa ƙungiyar na bibbiyar abubuwan da ke faru.
Patricia Scotland ta ce akwai damuwa mai tsanani kan yada abubuwa ke kasancewa: "Ya zama dole ƙasashen wannan ƙungiya su mutunta doka da dimokuraɗiyya a kowanne lokaci."
Gabon ta shiga wannan ƙungiyar ta reinon Ingila a Yunin 2022 domin rage karfin dogaro da Faransa - ƙasar da ta mulkesu kafin 'yanci.
Kalli yadda sojoji suka sanar da juyin mulki a Gabon
Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyo