Ra'ayi Riga: Tattaunawa da ma'abota sauraron BBC Hausa
Ku latsa lasifikar sama don sauraro:
Ra'ayi Riga na wannan makon ya tattauna ne kan cikar BBC Hausa shekara 65 da kafuwa.
Masu sauraro daga kasashe da dama sun shiga filin kamar daga Sudan da Libiya da Saudiyya da Amurka da Birtaniya da Nijar da Kamaru da Chadi da ma nan Najeriya.
Cikin wadanda suka bayyana labaran ban mamaki har da wanda cikin sunansa da yake amfani da shi a hukumance har da inkiyar BBC.
A ranar Lahadi 13 ga watan Maris ne BBC Hausa ta cika shekara 65 da kafuwa.