Bidiyon makarantar su Hanifa da aka kona
Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon:
Rundunar 'yan sandan jihar Kano da ke arewacin Najeriya ta tabbatar da cewa wasu matasa sun kona makarantar su Hanifa Abubakar, yarinyar nan 'yar shekara biyar da ake zargin mai makarantar ne ya kashe ta.
Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya shaida wa BBC cewa matasan sun kona makarantar ce da tsakar daren Litinin.
Ya ce babu wanda ya rasa ransa ko ya samu rauni.