Coronavirus: Ko allurar riga-kafin cutar korona za ta ɓata jinin al'adata?
Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:
Wasu matan da suka yi allurar riga-kafin cutar korona sun yi ta ganin sauyi a jinin al'adarsu,
Da yawansu al'adar ta sauya lokacin zuwa ne inda ta dinga ƙara kwanaki, sauran kuma yawan jinin da ke zuba ne ya ƙaru.
Amma shin hakan wani abin damuwa ne?
Mun tambayi wata ƙwararriyar likitar al'amuran da suka shafi garkuwar jiki a Kwalejin Imperial da ke Landan, Dr Viki Male.