Angon da ya auri mata biyu a rana ɗaya
Latsa hoton sama ku kalli hirar BBC da angon mata biyu a rana ɗaya
Babangida Sadiq ya fara rayuwarsa ta aure da mata biyu.
An ɗaura masa aure da matan biyu duka a yau Asabar a Abuja, babban birnin Najeriya.
An fara ɗaura auren wadda ya kira uwargida da misalin ƙarfe 12:00 na rana, yayin da kuma aka ɗaura auren ta biyu da misalin karfe 2:00.
Angon na mata biyu a rana ɗaya ya ce ya yi hakan ne domin ƙarfafa Sunnah.