Gane Mini Hanya: Tarihin Hula Zanna Bukar

Bayanan sautiLatsa sama don sauraron shirin
Gane Mini Hanya: Tarihin Hula Zanna Bukar

Da zarar an ambaci Hula Zanna Bukar, babu tababa an san daga yankin da ta fito a arewa maso gabashin Najeriya, wato jihar Borno.

Wannan hula dai na ɗauke da daɗadɗen tarihi da ake yi mata kallon cikamakin kwalliya ko ado ga maza.

A wata ziyarar aiki da tawagar BBCHausa ta kai birnin Maiduguri na jihar Borno, Badriyya Tijjani Kalarawi ta ziyarci wata fitacciyar unguwa ta maɗinka hula ta Zanna Bukar ga kuma rahoto na musamman da ta haɗa mana: