...Daga Bakin Mai Ita tare da Asiya Chairlady
...Daga Bakin Mai Ita tare da Asiya Chairlady
A wannan mako cikin shirin ...Daga Bakin Mai Ita, mun kawo muku tattaunawa da Asiya Abdullahi, wadda aka fi sani da Asiya Chairlady a masana'antar finafinan Hausa.
Ƴar asalin jihar Kebbi, Asiya ta ce ta so shiga harkar fim ne tun tana ƴar ƙarama, lamarin da ya zama ƙalubale gare ta kasancewar shekarunta sun yi kaɗan tun da farko.



