...Daga Bakin Mai Ita tare da Barista na Kwana Casa'in

Bayanan bidiyo, Latsa hoton sama ku kalli bidiyo:
...Daga Bakin Mai Ita tare da Barista na Kwana Casa'in

A wannan makon, filin Daga Bakin Mai Ita ya tattauna da Ahmad Turaki Kaka, wanda aka fi sani da Barista a fim ɗin Kwana Casa'in.

Ahmad Turaki haifaffen cikin garin Kano ne, wanda ya fara da waƙa a fina-finan Hausa na Kannywood.

Ya yi fina-finai da dama kamar Kwana Casa'in na Arewa 24, da kuma Labarina na kamfanin Saira Movies.