...Daga Bakin Mai Ita tare da Ilya na Kwana Casa'in
...Daga Bakin Mai Ita tare da Ilya na Kwana Casa'in
Filin Daga Bakin Mai Ita na wannan makon ya tattauna da Bashir Abdu, inda ya ji tarihin rayuwarsa da kuma harkokin fim.
Bashir ya shahara da sunan Ilya sakamakon rawar da ya taka a fim ɗin nan na Kwana Casa'in mai dogon zango da Arewa 24 ke shiryawa.




