Daga Bakin Mai Ita Tare da Daniel na Dadin Kowa
Daga Bakin Mai Ita Tare da Daniel na Dadin Kowa
Daga Bakin Mai Ita na wannan makon ya tattauna da Joseph Anekheh - wanda aka fi sani Daniel mijin Madam Gloria a fim ɗin Daɗin Kowa.
Tsohon ɗan wasan kwaikwayon ya fara wasan daɓe a shekarar 1987 a cikin birnin Kano da ke arewacin Najeriya.
Ya shafe lokaci mai tsawo yana fitowa a finafinai amma sai a shirin Daɗin Kowa tauraruwarsa ta haska yadda ba a taɓa tsammani ba.
Ya shaida wa BBC cewa finafinan da ya fito suna da dama, ya yi aiki da irinsu Hamisu Iyantama da dai sauransu.



