Yadda ake kunun madara da kuskus

Bayanan bidiyo, BBC Hausa
Yadda ake kunun madara da kuskus

Wannan wani shiri ne da BBC Hausa take kawo muku kullum a watan azumi, don bai wa mata damar gwangwaje basirarsu ta girki.

A wannan bidiyo, za ku kalli gwanar girkinmu ta yau, tana nuna mana yadda ake haɗa kunun madara tare da kuskus.

CookWhiteXee kamar yadda aka fi saninta da shi a shafin sada zumunta na Instagram, gwanar mai girki ce kuma ta nuna mana yadda ake wannan kunu mai burgewa.