Har yanzu zafin shan kaye ne ke damun Atiku - Tinubu

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya mayar wa babban mai hamayya da shi na Jam'iyyar PDP Alhaji Atiku Abubakar da martani bayan sukar gwamnatinsa.

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, kuma dan takarar shugaban kasa na babbar jami'iyyar hamayya ta PDP a zaben da ya gabata, ya bukaci shugaba Bola Tinubu ya sauka daga shugabancin kasar idan ba zai iya shawo kan matsalolin tsaron da kasar ke fama da su ba.

Atiku Abubakar, wanda shugaba Tinubu ya kayar a zaben da ya gabata, ya zargi shugaban da yin wasa da aikinsa yayin da kasar ke nutsewa cikin matsalar tsaro da ta tabarbarewar tattalin arziki.

Sai dai fadar shugaban Najeriyar ta yi watsi da kalaman na Atiku tana mai cewa wata suka ce irin ta 'yan hamayya.

A sanarwar martani da ta fitar, fadar shugaba Bola Tinubu ta ce har yanzu zafin shan kaye ne ke damun Atiku.

"Mun san cewa har yanzu zafin shan kaye bai saki Atiku ba don haka zai iya furta komi na sukar shugaba Tinubu," in ji sanarwar.

Mai magana da yawun shugaba Tinubu, malam Abdul'aziz Abdul'aziz a hirarsa da BBC ya ce tsohon mataimakin shugaban na son ya ci gaba da jan hankali ne.

"Wannan batu ne na ɗan adawa da yake son ya ja hankali domin a yi masa tafi domin mutum ne da ya faɗi zaɓe, saboda haka ƙoƙari yake a san da shi a riƙa jin sa a labarai domin kada a manta da shi," in ji Abdul'aziz Abdul'aziz

Ya ce duk wanda yake Najeriya ya san akwai shugaba mai cikakken iko kuma ko mutum ba ya ra'ayin gwamnatin APC ana ganin shugaban ƙasa da ganin aikinsa.

Abin da Atiku Abubakar ya ce

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar ya caccaki shugaban kasar Bola Ahmad Tinubu kan yadda yake tafiye-tafiye a daidai lokacin da Najeriya ke dabaibaye da kalubalen tsaro.

Atiku wanda ya yi takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP a zaɓen 2023 ya bayyana haka ne a shafinsa na X inda ya ce masu garkuwa da mutane na cin karensu babu babbaka a kasar.

Ya bayar da misali da yadda yan bindiga suka kashe wata uwa mai shayarwa da dattijuwa a Abuja saboda gaza biyan kudin fansa da kashe sarakunan gargajiya biyu a jihar Ekiti.

A cewarsa Najeriya na bukatar shugaban da ba ya bukatar hutu domin tunkarar kalubalen tsaro da tattalin arziki da ke durkushewa. Yana mai hannunka mai sanda ga abokin hamayyarsa Shugaba Tinubu "ya sauka tun da ya gaza"

Sai dai a martaninta, fadar shugaban na Najeriya ta ce fita zuwa ƙasashen waje ba laifi ba ne don shugaba ya dauki hutu domin kowane mutum yana buƙatar hutu,'' in ji Malam Abdul'aziz.

Ya kuma ce gwamnatin Tinubu na yin abinda ya dace a ɓangaren ƙalubalen tsaro.

Haka kuma fadar shugaban ƙasar ta bayyana kiran da stohon mataimakin ƙasar Alhaji Atiku Abubakar ya yi na shugaba Tinubu ya sauka da "kalamai wadanda ba su ma taso ba wanda kuma bai kamata dattijo kamar Alhaji Atiku yana furtasu ba."

A kullum dai gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu na bada bayyanan ƙoƙarin da take na shawo kan matsalar tsaro da tattalin arziƙi da sauran matsalolin da Najeriya ke fama da su, sai dai kuma ana ganin matsalolin na ci gaba da ƙaruwa.