Dan Aliyu ya buge Shagon 'Yar biyar, 'Yar Mage da Autan na Aisha ba kisa

Dan Aliyu na Arewa ya buge Shagon 'Yar biyar a damben gasa ranar Lahadi a gidan wasa na Idris Bambarewa da ke Marabar N'yanya jihar Nasarawa, Najeriya.

Bayan da Labaran dan Gwamba ya wake 'yan damben biyu ne, sai magoya baya suka ta yi musu ruwan kudi don kara musu karfin gwiwa.

Nan da nan Alkalin wasa Anas Dandume ya umarci a fara damben, turmin farko ya kayatar da 'yan kallo, amma ba kisa.

Bayan da suka sha ruwa suka koma turmi na biyu ne Dan Aliyu ya buge Shagon 'Yar biyar dan danben Guramada.

Daga nan aka shiga daya wasan gasar tsakanin 'Yar Mage da Autan na Aisha.

Turmi uku suka yi ba kisa tsakanin dan damben Kudu da na Guramada, wanda fiye da wata hudu bai fadi ba a gidan wasa da ke Marabar N'yanya.

Sauran wasannin da suka yi kisa:

  • Rabe Shagon Ebola ya buge Garkuwan Kurma
  • Garkuwan Kurma ya yi nasara a kan Shagon Shagon Sama'ila
  • Shagon Mustapha ya doke Shagon Ali Terminator
  • Shagon Dunan ba ta jemu ba ya yi nasara a kan Autan Makada
  • Aljanin Autan Nokiya ya buge Dogon Shagon Lawwali
  • Ushu Shagon Inda ya buge Shagon na Aisha
  • Autan Nokiya ya doke Shagon Autan Makada

Wasannin da aka yi canjaras:

  • Dogon Inda da Shagon Bahagon Ali Yaro
  • Shagon Lawwali da Jan Idon Guramada