Ra'ayi Riga: Kan hauhawar farashi da tsadar rayuwa da rashin kuɗi 20/12/24
Ra'ayi Riga: Kan hauhawar farashi da tsadar rayuwa da rashin kuɗi 20/12/24
A shirin namu na wannan mako mun tattauna kan batun tsadar rayuwa da tashin farashin kayan masarufi da rashin kudi a hannun jama'a a Najeriya.
Ɗimbin iyalai ne dai suka shiga cikin tsananin da halin matsin rayuwa sakamakon hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya.
A watan Nuwamban wannan shekara alƙaluman hukumar ƙididdiga ta ƙasar sun nuna cewa hauharawar farashi ya kai kashi 34.64 cikin ɗari a ƙasar.
Wannan batu ya jefa 'yan ƙasar musamman masu karamin ƙarfi cikin halin tagayyara.
Zaharadden Lawan ne ya jagoranci gabatar da shirin a wannan mako