Halin da na samu Zamfara ya shallake hankali - Gwamna Dare

Halin da na samu Zamfara ya shallake hankali - Gwamna Dare

Kimanin mako uku da kama ragamar mulki a Zamfara, sabon gwamnan jihar Dauda lawal Dare ya ce mawuyacin halin da ya samu jihar, ya tayar masa da hankali.

Ya yi iƙirarin cewa gwamnatin da ya wuce ta bar jihar Zamfara cikin ƙangin bashin albashin ma'aikata waɗanda suka shafe wata uku ko fiye ba tare da an biya su albashi ba.

Sabon gwamnan ya ce bayan zuwan sa kan karagar mulki, ya fara da ƙoƙarin farfaɗo da aikin samar da ruwan sha musamman wanda ya ce ya durƙushe saboda rashin kuɗi da yanke wa gidan samar da ruwan wutar lantarki da sauran matsaloli.

Gov Dare