Daga Bakin Mai Ita tare da Isan Koki
Daga Bakin Mai Ita tare da Isan Koki
Filin Daga Bakin Mai Ita na wannan makon ya karɓi baƙuncin Isa Awwal Koki, ɗaya daga cikin matasan taurari a masana'antar Kannywood.
Ya fito a matsayin Magaji a cikin fim ɗin Laure, da kuma Imam a cikin fim ɗin Duka Ɗauka.
An haife shi a unguwar Koki da ke ƙwaryar birnin Kano, kuma ya yi firamare da sakandare, kafin daga baya ya halarci jami'ar Northwest University, Kano (Yusuf Maitama Sule a yanzu.



