..Daga Bakin Mai Ita tare da Fatima ta kwana Casa'in

Bayanan bidiyo, Latsa alamar da ke sama domin kallo
..Daga Bakin Mai Ita tare da Fatima ta kwana Casa'in

A wannan makon mun kawo muku tattaunawa da tauraruwa Fatima Mohammed Mustafa wadda aka fi sani a fim mai dogon zango mai suna kwana Casa'in da gidan talabijin na Arewa24 ke nunawa.

Fatima wadda ƴar asalin jihar Kaduna ce, da ke zaune a birnin Kano, ta fara harkar fim ne bayan haɗuwarta da wani abokinta a shafin sada zumunta wanda ya nemi da ta aike masa da muryarta domin tantance ta.