...Daga Bakin Mai Ita tare da Abdul D One

Bayanan bidiyo, Ku latsa hoton da ke sama ku kalli bidiyo
...Daga Bakin Mai Ita tare da Abdul D One

A wannan makon, mun karɓi baƙuncin mawaƙi kuma makaɗi Abdulkadir Tajuddin - wanda aka fi sani da Abdul D One.

Matashin ɗan asalin jihar Katsina ne da ke arewacin Najeriya, kuma ya ce ya fara waƙa ne tun yana makarantar firamare.

Sai dai ya fara shiga sutudiyo ne bayan ya shiga sakandare.

Ya ce shahararren mawaƙi Umar M. Sheriff ne mai gidansa a harkar waƙa.

Ku latsa hoton da ke sama ku sha kallo lafiya.