Girke-girken Ramadan: Yadda ake sarrafa danderu da kazar gida
Girke-girken Ramadan: Yadda ake sarrafa danderu da kazar gida
Wannan wani shiri ne da BBC Hausa take kawo muku kullum a watan azumi, don bai wa mata damar gwangwaje basirarsu ta girki.
A wannan bidiyo, za ku kalli gwanar girkinmu ta yau, da ke nuna mana yadda ake sarrafa danderu da kazar gida, don masu azumi.
Maryam Adam Hamza wadda aka fi sani da Chef- Maryama a shafin Instagram, gwanar mai girki ce kuma ta nuna mana Yadda ake sarrafa danderu da kazar gida.
Girki ne da mai azumi, ba zai so ya wuce shi ba, idan an sha ruwa!



