Girke-girken Ramadan: Shinkafar persley da miyar shredded beef

Bayanan bidiyo, Girke-girken Ramadan
Girke-girken Ramadan: Shinkafar persley da miyar shredded beef

Wannan wani shiri ne da BBC Hausa take kawo muku kullum a watan azumi, don bai wa mata damar gwangwaje basirarsu ta girki.

A wannan bidiyo, za ku kalli gwanar girkinmu ta yau, tana nuna mana yadda ake haɗa shinkafar persley da miyar shredded beef.

Hafsat Othman wadda aka fi sani da muhafoven a shafin sada zumunta na Instagram, gwanar mai girki ce kuma ta nuna mana yadda ake wannan shinkafar ganye mai ban sha'awa.