Juyin mulkin Nijar ya kassara sana'ata - Wata mai ƙaramar sana'a

Juyin mulkin Nijar ya kassara sana'ata - Wata mai ƙaramar sana'a

Juyin mulkin da sojoji suka yi ranar 26 ga watan Yuli a Nijar, ya shafi harkokin rayuwa a ɓangarori daban-daban ciki har da masu ƙananan sana'o'i da ke hada-hada a tsakanin ƙasar da sauran ƙasashe maƙwabta kamar Najeriya.

Duk da yake, kasuwanni sun ci gaba da kasancewa a buɗe, kuma 'yan kasuwa na gudanar da harkokinsu a biranen ƙasar, sai dai shiga ko fitar da kaya daga Nijar, ya zama wani babban ƙalubale saboda rufe iyakokin ƙasar da Najeriya da kuma Jamhuriyar Benin.

Akwai ɗumbin 'yan kasuwa da kayayyakinsu suka maƙale a kan iyaka, sannan akwai ƙananan masu sana'o'i da ba sa iya shigar da haja ko su fitar da ita daga Nijar, lamarin da ya kassara rayuwarsu.

Niger coup