Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ghana ta naɗa Schafer don taimakawa masu horar da Black Stars
Hukumar ƙwallon kafa ta Ghana ta naɗa Winfried Schafer domin taimakawa masu horar da Black Stars, wadda ta kasa samun gurbin shiga gasar kofin Afirka ta 2025.
Mai shekara 75 ɗan kasar Jamus, ya ja ragamar Kamaru ta lashe babban kofin tamaula na Afirka a 2002.
Wanda ya yi fice a sana'ar horar da tamaula a Karlsruhe mai buga Bundesliga a lokacin, ya yi kocin tawagar Jamaica da kuma Thiland.
Schafer zai taimakawa Otto Addo, bayan da Ghana ta yi sauye-sauye a gurbin masu horar da ita tamaula, domin tunkarar wasannin neman shiga kofin duniya da za ta yi a cikin Maris.
Addo zai ci gaba da aiki, duk da kasa kai kasar gasar kofin nahiyar Afirka da za a yi a bana a Morocco.
Karon farko da Black Stars ba za ta halarci wasannin ba, bayan gasa 11 baya, wadda ta kasa cin wasa da ta kai yin ta karshe a rukuni na shida da ya haɗa da Angola da Sudan da kuma Niger.
Ghana za ta buga wasan neman shiga gasar cin kofin duniya da Chad da Madagascar a cikin watan Maris.
Tawaga ɗaya ce daga rukuni na tara za ta wakilci Afirka a gasar kofin duniya da za a yi a 2026 a Amurka da Canada da Mexico.