Ina jin kamar shekara 35 da na yi ina aiki sun tafi a banza - Ɗan fansho

Bayanan bidiyo, Latsa alamar da ke sama domin kallon bidiyon
Ina jin kamar shekara 35 da na yi ina aiki sun tafi a banza - Ɗan fansho

Matsin rayuwar da ake fama da shi a Najeriya ya shafi kusan duk wani ɓangare da al'amuran rayuwa ciki har da ƴan fensho.

Wani ɗan fensho da ya yi aiki a matsayin mai share-share a jihar Gombe, Aliyu Umar ya ce yana jin tamkar wahalar da ya yi a tsawon shekara 35 ta aikinsa, tamkar ta tafi a banza.

Ɗan fenshon ya ce iyalan gidansa 15, kuma hatta gonar da ya saya don ya bar wa ƴaƴansa gado, bayan ya karɓi kuɗin sallamarsa, ala dole ya sake sayar da ita domin ciyar da gida.

A watan Maris ɗin 2024 ne, gwamnatin jihar Gombe ta biya shi naira 600,000 a matsayin kuɗin sallamarsa, sai dai a cikin wata bakwai kacal kuɗin duka sun ƙare.

Ya ce a lokacin ya sayi buhun masara uku sannan ya biya bashin da ake bin sa, na abincin da ya riƙa karɓa a tsawon shekara shida da ya yi yana jiran garatutin nasa.

Hauhawar farashi sanadin ƙarin farashin man fetur a Najeriya ya daɗa tsanani ga miliyoyin iyalai a ƙasar.