Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Aƙalla ƙungiyoyi 12 ne ke zawarcin Mainoo, Nottingham Forest na shirin ƙara farashin Anderson
Dan wasan Ingila Kobbie Mainoo mai shekara 20 zai zabi wurin da yake son ya koma taka leda daga cikin kungiyoyin 12 da ke zawarcinsa, idan Manchester United ta amince ta bayar da shi aro a watan Janairu..(Mail)
Watakila Nottingham Forest ta nemi kudi fiye da fam miliyan 100 kan dan wasan Ingila Elliot Anderson, mai shekara 23 a lokacin bazara. (Football Insider)
Ana da kwarin gwiwa cewa za a samu wata kungiyar Saudiyya da za ta iya siyan dan wasan Masar Mohamed Salah, mai shekara 33, daga Liverpool a watan Janairu karkashin yarjejeniyar da suka kulla da ta shafi zaftare farashi.(The i paper )
Lyon na tattaunawa kan yuwuwar siyan dan wasan Chelsea Axel Disasi, mai shekara 27, a watan Janairu.(L'Equipe )
Crystal Palace na ci gaba da bibiyar halin da dan wasan Ingila da West Ham ke ciki watau Max Kilman, mai shekara 28.(Football Insider)
Everton da West Ham sun fara bincike a matakin farko kan dan wasan Brazil Yuri Alberto mai shekara 24 , wanda a halin yanzu ke taka leda a Corinthians. (Teamtalk)
Flamengo na son dan wasan Colombia Jhon Arias mai shekara 28 , wanda ya koma Wolves a watan Yuli . (Ekrem Konur)
Manchester United da Tottenham na cikin kungiyoyin Ingila da aka sanar da su kan cigaban dan wasan Anderlecht da Ecuador Nilson Angulo mai shekara 22. (Teamtalk)
Dan wasan Lille ,Ayyoub Bouaddi na jan hankalin kungiyoyin Turai inda Arsenal ce ake ganin za ta iya siyan dan wasan na Faransa mai shekara 18 (RMC Sport )