Daga Bakin Mai Ita tare da Radeeya Jibril
Daga Bakin Mai Ita tare da Radeeya Jibril
Filin Daga Bakin Mai Ita ya karɓi baƙuncin Radeeya Jibril, tauraruwar finafinan Hausa na Kannywood.
An haifi jarumar a jihar Legas da ke kudancin Najeriya amma ta koma Kaduna da zama, har ma ta yi makaranta a can.
Ta fito a finafinai da dama kuma shahararru daga cikinsu sun haɗa da Uku Sau Uku, da Lulu da Andalu, da Ɗanjarida, da Madafar Ƙauna, da Fatake.



