Ku San Malamanku tare da Dakta Abdulmajid Almadani
Cikin shirin Ku San Malamanku na wannan mako BBC ta tattauna da Dakta Abdulmajid Muhammad Umar Almadani.
An haifi Sheikh Abdulmajid Muhammad Umar a unguwar Tudun Wada da ke jihar Kaduna a arewacin Najeriya.
Karatunsa
Malamin ya fara karatun addini ne kafin shigarsa karatun Boko, inda ya haddace Alqur'ani, kafin shigarsa Primary ta Abu Mutalib Internation School.
Ya kuma halasci makarantar Islamiyya ta Sheikh Abubakar Mahmood Gumi inda inda ya kammala a matakin sakandire.
Daga nan ya tafi wata makaranta a ƙasar Ghana, domin fadada karatunsa, a wannan makarantar ne aka zabe shi domin shiga gasar karatun al'qur'ani na duniya da aka gudanar a ƙasar Saudiyya.
Wannan dalili ne ya bai wa malamin damar neman gurbin karatu a jami'ar musulunci da ke Madina, Inda ya karanta fannin qira'a da tafsiri.
Ya kuma yi digirinsa na biyu, sannan digiri na uku a fannin tafsiri duk dai a jami'ar ta Madina.
Malamin ya kwashe akalla shekara 24 a Madina yana neman ilimi a jami'a da majalisun malamai daban-daban a birnin Madina.
Fannin da malamain ya fi ƙwarewa
Sheikh Abdulmajid Almadani ya ce ''har yanzu ni bana jin na ƙware a wani fanni, amma idan ake shiga ayi abin da ya sauwaƙa, shi ne fannin karatar da ruwayoyin al-qur'ani da ilimin qur'ani da tafsiri, sai a wasu lokuta ɓangaren rabon gado''.
Malamin ya ce yana iya karantar da mutum, ya kuma fahimtar da shi ilimin rabon gado a cikin ƙasa da sa'o'i biyu ko wani abu makamancin haka, da ilimin harshen Larabci
Abin farin ciki
Sheikh Abdulmajid Almadani ya ce abin farin cikin da ba zai taɓa mantawa da shi a rayuwarsa ba, shi ne lokacin da ya samu gurbin karatu a jami'ar Musulunci da ke Madina
Tambayar da aka fi yi wa malamin
Malamin ya ce mafi akasari tambayoyin da mutane suka fi yi masa, sun shafi matasa, kasancewar ya shagaltar da kansa wajen jiɓantar al'amuran da suka shafi matasa a lokacin da yake dab da komawa Najeriya bayan kammala karatunsa a Saudiya.
Sheikh Abdulmajid Almadani ya ce yana damuwa matuƙa da halin da matasa ke ciki musamman matalar shaye-shaye da ke shafar ƙwaƙwalen matasan.
''Sai kuma abin da ya shafi siyasa, kasancewar na shiga siyasa har ma na yi takara, to mutane kan yawan yi min tambayoyi kan dalilan da suka sanya ni shiga siyasa''.
'Abin da ke faranta min rai'
Sheikh Abdulmajid Almadani ya ce babban abin da ke faranta masa rai shi ne ya ga matasa sun samu fahimtar addini.
Sannan kuma ya ce yana son ganin matashin da ke da alqiba mai kyau a rayuwarsa.
'Abin da ke ɓakanta min rai'
Babban abin da ke ɓata wa malamin rai shi ne ganin matasa a cikin wani mummunan hali.
''Abin na ba ni takaici idan na ga matasa sun taso cikin rayuwar da ɓarna ta yawaita", in ji Malamin.
'Abincin na da fi so'
Sheikh Abdulmajid Almadani ya ce abincin da ya fi so shi ne shinkafa, ko ta wane hali aka sarrafa ta, musamman idan ta ji wake ga mai, ga kuma yaji.
Wasan ƙuruciya
Malamin ya ce wasan da yake yawan yi a lokacin da yake ƙuruciya shi ne wasan ƙwallon ƙafa
Hadisin da ya fi faranta masa rai
Sheikh Abdulmajid Almadani ya ce hadisan da suka fi faranta masa rai su ne hadisan da suka yi magana a kan ƙudurar ubangiji.
Misali hadisin da ke cewa ''babu wani yini, face mala'iku biyu sun bayyana suna addu'ar Allah ya bai wa wanda ke bayarwa, Allah ka kara talauci kan wanda ke hanawa''.
Babban burina
''Babban burina a rayuwa shi ne kafa wani abu da zai amfanar da matasa da kuma mutane''.




